Iyalan matashin da aka harbe yayin zanga-zanga a Kaduna na neman adalci

Asalin hoton, Ismail Abdullahi
- Marubuci, Mansur Abubakar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos
- Lokacin karatu: Minti 3
Iyalan matashi kuma tela mai shekara 24, Abubakar Adam Abdullahi, na neman a tabbatar musu da adalci bayan sun zargi ‘yansanda da kashe shi yayin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Rundunar ‘yansandan yankin jihar ta musanta cewa tana da hannu a mutuwar tasa, yayin da mai magana da yawun gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa ba su da masaniya kan asarar rayuka da aka yi sakamakon zanga-zangar.
Sai dai ƙungiyar Amnesty International ta ce an kashe mutum uku a Kaduna a yayin zanga-zangar.
Da yake magana da BBC a madadin iyalan, dan'uwan Abubakar Ismail ya yi iƙirarin cewa ‘yansandan sun harbi Abubakar a ƙirji ranar Alhamis, lamarin da ya kai ga mutuwarsa a asibitin Yusuf Dantsoho.
“Abin da muke so shi ne a tabbatar da adalci ga dan’uwanmu,” in ji Ismail.
Tun bayan da aka fara zanga-zangar kwana biyar da suka gabata, ‘yansanda sun bayar da rahoton kashe aƙalla mutum bakwai, an kama 700, sannan wasu jami’an tsaro sun tsare wani jagoran zanga-zangar.
Duk da gargadin da Shugaba Bola Tinubu ya yi, dubban ‘yan Najeriya ne suka fito kan tituna domin nuna adawa da tsadar rayuwa, sakamakon nasarorin da matasan Kenya suka samu a baya-bayan nan, wadanda zanga-zangarsu ta kai ga gwamnati sauya ra’ayinta.
Abubakar, wanda shi ne ƙarami a cikin ‘yan’uwansa 14, yana zaune tare da iyayensa a Kaduna kuma shi tela ne wanda ke da burin samun bunƙasa da kuma tara nasa iyalin, amma kuma tsadar rayuwa ta sa waɗannan burikan suka samu cikas wanda har ma ta sa shi shiga zanga-zangar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"A matsayinsa na tela, farashin kayan da ya kamata ya dinga amfani da su ya yi tashin gwauron zabi, da farashin abinci, da kuɗin hayar gida. Kowa ma dai na jin duriyar wannan matsalar tattalin arziki," in ji Ismail.
Hotunan bidiyo na ranar mutuwar Abubakar sun nuna shi tare da gungun matasa, suna yi wa ‘yansanda ihu kafin su yi yunkurin guduwa.
A cewar Ismail, wanda ya zanta da shaidu, lamarin ya faru ne a kusa da ofishin gwamnan Kaduna, Uba Sani.
Rahotanni sun ce Abubakar ya shaida wa abokansa cewa ya gaji kuma yana son komawa gida, amma bayan wani lokaci, ‘yansanda suka buɗe wuta kan masu zanga-zangar.
Wani bidiyo ya nuna lokacin da Abubakar ke faɗuwa kasa bayan an harbe shi, ana kuma jin abokansa suna ta ihu da cewa "ofisa ka dakata, sai kuma ya harbe shi".
Ismail ya ba da labarin irin kaduwar da ‘yan'uwan marigayin suka shiga a lokacin da aka kira su asibiti aka sanar da su cewa an harbe shi.
“Daga baya mun ga bidiyonsa yana zaune yana magana da abokansa a yayin zanga-zangar, wanda hakan ya kara tabbatar da cewa ba ya wani rashin-ji a lokacin zanga-zangar”.
Ismail ya kara da cewa, har yanzu yana kokarin fahimtar yadda wannan musiba ta faru da dan’uwansa.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Kaduna, Mohammed Lawal Shehu, ya bayyana cewa dalilin da ya sa ba su gaskata adadin mutanen da suka mutu a zanga-zangar na baya-bayan nan ba shi ne sun dogara ne da bayanan ‘yansanda, wadanda suka ce ba a samu asarar rai ba.
"A cewar 'yansanda, babu wani mutum da ya mutu a zanga-zangar, kuma mun dogara da su don samun bayanai," in ji Shehu.
Sai dai ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Amnesty International ta buƙaci a gudanar da bincike kan mutum 23 da suka mutu a fadin kasar, ciki har da mutum uku a Kaduna.
Ismail, a madadin iyalansa, ya sha alwashin cewa ba za su huta ba har sai sun samu amsa da adalci kan mutuwar ɗan'uwansa.
"Yana cikin farin ciki lokacin da ya fita tare da abokansa wajen zanga-zangar, ya damu da halin da kasar ke ciki," in ji Ismail, yayin da yake tuna da jajircewar dan'uwansa Abubakar na tofa albarkacin bakinsa kan kalubalen da ake fuskanta a Najeriya.











