'Har yanzu muna biyan harajin shigo da kayan da gwamnati ta ce an cire wa haraji'

Rice

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Batun cire harajin shigar da kayan masarufi irin su shinkafa da alkama da wake da sauran dangoginsu Najeriya na ɗaya daga cikin abubuwan da shugaban ƙasar ya faɗa yayin jawabinsa na matakan da gwamnatinsa ke ɗauka ga masu zanga-zangar tsadar rayuwa da ƴan ƙasar ke ci gaba da yi.

A makonnin da suka gabata ne gwamnatin kasar ta sanar da cewa za ta daina karbar kudin harajin shigo da wasu kayan abinci zuwa kasar a wani mataki na sassauta farashin kayan abinci da ke ci gaba da tashi.

A lokacin da ya bayar da sanarwar a farkon watan Yuli, ministan harkokin noma na Najeriya Abubakar Kyari, ya ce sassaucin zai shafi kayan abinci kamar shansherar shinkafa da kuma alkama.

Sai dai a cewar kungiyar masu shigowa da fitar kaya ta Najeriya har yanzu mambobinta na ci gaba da biyan haraji kan wadannan kayyaki.

Alhaji Aminu Dan-iya, wanda shi ne shugaban kungiyar a Arewacin Najeriyar ya kuma ce ko a kwanakin baya an yi ta bayanin cewa shugaban ƙasar ya cire harajin shiga da kayan abinci, amman idan suka je wajen hukumar da ke kula da shigi da fice, sai a ce musu jami’an hukumar ba su samu umarnin haka daga sama ba.

"Saboda haka babu abin da aka rage ana ci gaba da biya"

Alhaji Aminu ya ce mutane na kiran su kan cewa shugaban ƙasa ya cire haraji kan kayayyaki amman har yanzu ana ci gaba da samun hauhawar farashi a kasuwa,"bisa ga zahirin gaskiya ko gobe ana biyan kuɗin harajin, saboda haka yana da kyau su fahimci cewa idan shugaban ƙasa ya yi magana sannan kuma ya bayar da umarni, to ba za a wuce sa’a daya ba, ba tare da an janye harajin ba."

Shugaban ƙungiyar ya ce lokacin da aka ɗiba na aiwatar da wannan mataki tsawon wata shidda amman ga shi lokaci yana wucewa ba tare da an fara amfani da matakin ba.

"Wahalhalun da ƴan Najeriya ke sha ya ta'allaƙa ne kan yadda ake shigo da kayan da kuma yadda ake sufurinsu da kuma yadda ake hada-hadar canji, wadannan su ke azabatar da kasuwar abinci a Najeriya, wanda kuma ya kamata hukuma ta fahimci haka."

Alhaji Aminu ya ƙara da cewa kudin harajin ya yi nunkin ba nunki, ga kuma yadda gwamnati ta cire tallafin man fetur da haddasa tsadar sifuri, "To ya ya kaya za su je kasuwa da sauƙi? ba za su je ba."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shugaban ƙungiyar masu shigi da ficen a Arewacin Najeriya, ya ce idan har aka aiwatar da manufofin da shugaban ƙasar ya zayyana za a samu sauƙin rayuwa a ƙasar.

"Gobe idan aka aiwatar na tabbatar sati mai zuwa abinci zai sauka, kuma mutane za su samu sawaba, kuma baya ga haka a ba kowa wanda zai iya ya kawo ba a tsabbace wasu ɗaiɗaiku a ba su waibar shiga da kayan ba."

Najeriya dai na ci gaba da fuskantar hauhawar farajin kaya, lamarin da ya sanya ƴan ƙasar fara zanga-zangar nuna ƙin amincewarsu da wasu manufofin gwmanatin.

Matsalar tsaro dai na daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da rashin noma a Najeriya musamman a arewacin kasar da aka fi yin noma, sakamakon matsalar yan bindiga da ke hana manoman zuwa gonakinsu, a wasu wuraren kuma suka tursasa biyan haraji.

Tun a lokacin gwamnatin da ta gabata ne shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya rufe iyakokin kasar, inda aka haramta shigo da wasu kaya, ciki har da shinkafa wadda kasar ta yi matukar dogara da ita.

Gwamnatin ta ce ta yi hakan ne domin bunkasa noma da sarrafa shinkafa a cikin gida.

Duk da cewa matakin ya taimaka wajen samar da sabbin kamfanonin sarrafa shinkafa a cikin gida, to amma farashin shinkafar, wadda akasarin al’ummad kasar suka dogara da ita a matsayin abinci na ci gaba da tashi babu kakkautawa.