Wane ne Ryan Wesley Routh, mutumin da ake zargi da yunƙurin kisan Trump?

Asalin hoton, Reuters
Kafafen watsa labaran Amurka dai sun bayyana Ryan Wesley Routh a matsayin wanda ake zargi sakamakon yunƙurin kisan ɗantakarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican, Donald Trump, a Florida.
Mista Routh, mai shekara 58 dai ɗan North Carolina ne inda ya shafe fiye da rabin rayuwarsa a can kamar yadda bayanai masu inganci suka nuna, sai dai kuma a baya-bayan nan ya koma Hawaii da zama.
Abin da ya aikata ya sanya ana bincike kansa kuma wani abu da ya fito fili shi ne cewa yana da aƙida sosai ta ƙaunar Ukraine. Sannan ya yi shari'u da dama da jama'a.
Ana dai zargin Ryan da zuwa filin wasan ƙwallon Golf da ke Florida ranar Lahadi, yana ɗauke da bindiga ƙirar AK-47.
Jami'an FBI sun karɓi bindigar da kuma jakunkuna guda biyu na goyawa a baya daga dajin da ake zargin ɗanbindigar ya ɓoye su.
Duk da cewa Routh ya tsere a motarsa, amma wani wanda ya shaida al'amarin ya gano shi bayan ɗaukar hotonsa a cikin baƙar motarsa ƙirar Nissan.
Daga nan ne aka fitar da hoton motar ana neman ta. Ƴansandan yankin sun ce jami'ansu sun gano motar miniti 45 bayan faruwar al'amarin kuma suka bi ta.
Kuma daga ƙarshe an tsayar da shi a kan babban titin Interstate 95 inda aka tafi da shi domin tsarewa.
Mece ce alaƙar Routh da Ukraine?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mista Routh ya shaida wa jaridar New York Times A 2023 cewa yana son kai ɗauki ga Ukraine a yakin da take da Rasha, kuma yana son ɗaukar sojojin Afghanistan waɗanda suka guje wa Taliban.
A wata hira ta waya da ya yi da jaridar, Routh ya ce gomman sojoji na sha'awar yaƙi kuma yana shirin ɗaukar su daga kasashen Pakistan da Iran da Ukraine, akwai yiwuwar zai yi hakan ne ba bisa ƙa'ida ba.
“Za mu iya sayen fasfo-fasfo ta Pakista tunda ƙasa ce wadda ta ɓaci da rashawa da cin hanci,” in ji shi.
Routh ya kuma shaida wa jaridar a lokacin cewa yana birnin Washington ne domin gana wa da kwamitin Amurka kan tsaro da haɗaka a Turai domin nema wa ƙasar Ukraine ƙarin tallafi.
Bayanai sun nuna Routh yana ta fama ɗaukar sojoji a watan Yuli.
Wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a watan Yuli ya ce "Sojoji, don Allah ka da ku kira ni. Muna ta ƙoƙarin ganin Ukraine ta karɓi sojojin Afghanistan kuma muna fatan mu samu bayanan da za mu ba ku a ƴan watanni masu zuwa....ku ƙara haƙuri."
Sai dai kuma ƙungiyar sojojin sa-kai ta ƙasa da ƙasa kan Ukraine ta musanta yin alaƙa da mista Routh. Wasu jami'an ƙasar ta Ukraine ma sun ce ba su san shi ba.
Tuni Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya yi Allawadai da yunƙurin kisan na Trump.











