Wane ne ya yi nasara tsakanin Harris da Trump a muhawara?

Kamala Harris da Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kamala Harris da Donald Trump kenan lokacin da suke caccakar juna a muhawarar 'yantakarar shugabancin Amurka ranar Talata da dare
Lokacin karatu: Minti 3

Donald Trump da Kamala Harris sun fafata a karon farko a muhawarar 'yan takarar shugabancin Amurka a birnin Philadelphia ranar Talata da dare.

A muhawarar da suka kwashe tsawon minti 90, Ms Harris ta soki aniyar Trump ta sanya haraji mai yawa a kan kayayyakin waje, wanda shiri ne da ta kwatanta da haraji a kan masu matsakaicin samu, inda ta tallata shirinta na rage haraji ga iyalai da masu kananan harkokin kasuwanci.

Haka kuma, Harris ta soki Trump da janyo rashin akin yi a Amurka a lokacin yana shugaban kasa daga 2017 zuwa 2021.

Ta kuma zarge shi da hannu a boren da aka samu a majalisar dokokin ƙasar, da kuma yadda ta ce wasu tsoffin jami'an gwamnatinsa sun juya masa baya har ma suka zama daga cikin masu sukar manufofin yaƙin neman zaɓensa.

'Yar takarar jam'iyyar Democrats ɗin ta tilasta wa abokin karawar tata komawa kare kansa a wasu lokutan muhawarar, inda a wasu lokutan ya riƙa ɗaga muryarsa tare da sosa kai.

A nasa ɓangare Donald Trump ya kare kan sa sannan ya ƙaryata rahotonnin da ke cewa 'yan ciranin Haiti da ke zaune a garin Springfield na jihar Ohio, na kamawa tare da cin dabbobin makwabtansu.

Mista Trump ya kuma soki Harris a kan yawan tashin farashin kaya da ayyuka da ya ce an rika samu a lokacin mulkin Biden, kodayake ya rika kara gishiri a kan yadda aka samu karuwar farashin.

Sannan kuma nan da nan ya karkata a kan babban batun da ya fi sanyawa a gaba na shige da fice, inda ya yi ikirari ba tare da wata sheda ba cewa bakin haure sun rika shiga Amurka daga iyakarta ta kudu da Mexico.

‘Yar takarar ta Democrat ta gabatar da jawabi mai tsawo na suka a kan ‘yancin zubar da cikin da ake magana kan yadda take ganin an danne wa mata ‘yancinsu na samun kulawar gaggawa a harkar lafiya, da kuma yadda matan suka rasa damar zubar da ciki saboda dokoki na jihohi da suka samu gindin zama tun bayan da kotun ƙolin kasar ta kawar da damar da jihohi ke da ita a kan hakan a 2022.

Hukuncin da ta danganta da alkalai uku na kotun da Trump ya nada.

Wane ne ya yi nasara?

Kamala Harris da Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Harris da Trump sun sha sukar juna a lokacin kamfe tun kafin muhawarar

Idan ana maganar wanda ya yi nasara da wanda ya gaza a wannan muhawara, ana nufin ɗan takarar da ya samu damar amsa tambayoyi tare da kare manufofinsa, da kuma fannonin da ya gajiya.

Ƙur'ar jin ra'ayin jama'a da CNN ta yi kan waɗanda suka kalli muhawarar ta nuna Harris ta fi Trump ta taka rawa a muhawarar, haka ma wata ƙungiyar da ke sanya idanu kan muhawarar ta nuna hakan.

Wannan sakamako zai iya kasancewa na ɗan lokaci, to amma salon da Kamala Harris ta ɗauka ya sanya Trump zama mai kare kansa musamman a kan manyan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da 'yancin zubar da ciki.

Kafin wannan lokaci dai, gangamin yaƙin neman zaɓen Harris na ta nazarin ko zai iya sake amincewa da wata muhawarar.

To amma jim kaɗan bayan kammala wannan, sun yi ta kiran sake shirya wata muhawarar kafin watan Nuwamba.

Wannan kaɗai alama ce da ke nuna yadda muhawarar ta yi wa 'yan jam'iyyar Demockrats daɗi.