Alƙawarin Trump na ceto Amurka daga taɓarɓarewa na sauya ra'ayin 'yan ba-ruwanmu

- Marubuci, John Sudworth
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, North America correspondent, BBC News
- Aiko rahoto daga, Saginaw, Michigan
- Lokacin karatu: Minti 4
Duk da irin ƙalubalaen da Kamala Harris ta bai wa Donald Trump yayin muhawara, alƙawarin da yake yi na ceto Amurka daga cikin ƙangin taɓarɓarewa na shiga kunnen masu zaɓen da ba su da alƙibla a wannan jihar mai matuƙar muhimmanci.
Na tarar da Rachel Oviedo mai shekara 57 zaune a kan kujerarta tana kallon wasu kujeru da aka zubar a gefen titi kusa da wata ma'aikata, wadda a baya take samar da kayayyakin mota ƙirar Chevrolet da Buicks amma aka kulle ta a 2014.
"Nan muke zama kodayaushe," kamar yadda ta faɗa mani. "Mukan ga mutanen da ba su da muhalli suna shige da fice da zimmar yin amfani da wurin."
Na fara haɗuwa da ita kwana ɗaya kafin muhawarar ranar Talata a Philadelphia, lokacin da ta faɗa mani cewa har yanzu ba ta yanke hukunci kan wanda za ta zaɓa ba.
Ta ce Donald Trump ya yi kama da wanda zai iya kuma "mutum ne mai cika alƙawari" , yayin da Kamala kuma ke da alamar nasara amma har yanzu ba a san ta ba sosai.
"Tana birge ni," in ji ta, "amma ba mu san abin da za ta yi ba nan gaba."
Akasarin jihohin Amurka na bin aƙidar ko dai jam'iyyar Democrat ko kuma Republican, abin da ke sa a san wanda zai yi nasara tun kafin jefa ƙuri'a.
Amma Michigan na cikin jihohin da ba su da alƙibla a siyasance, kuma yankin Saginaw na cikin wuraren da ƙuri'unsu za su iya faɗawa cikin akwatin Trump ko ta Kamala.
Idan suka zo kaɗa ƙuri'unsu, mutane irinsu Rachel ne - da ba su da alƙibla tukunna - za su yanke hukuncin yadda Amurka za ta kasance a nan gaba.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Chuck Brenner, tsohon ɗansanda Saginaw, shi ma yana ɗaya daga cikinsu.
Mutumin mai shekara 49 da ke aikin wucin-gadi kuma yake da kamfanin harkokin gine-gine, ya ce ya lura da matsalar.
"Kusan duka iyayenmu na aiki ne a wannan ma'aikatar," kamar yadda ya faɗa mani.
"A baya, kowa na da kuɗi kuma akwai ayyuka. Yanzu kuwa komai ya sauya, mutane na fama saboda yara na tasowa a talauce, sai kuma shan ƙwayoyi da sauransu."
Alƙawarin da Trump ke yi na ceto Amurka daga taɓarɓarewa ya shiga zuciyar Chuck.
"Tabbas," a cewarsa. "Saboda a bayyane abin yake."
Amma duk da cewa ya zaɓi Trump a 2016, Joe Biden ya zaɓa a 2020.
"Trump ɗan dirama ne," in ji shi. "Ga kuma shari'o'in da ake yi masa. Ni na gaji da waɗannan abubuwan."
A wannan karon ya ce zai yanke hukunci ne kawai bayan ya ji abin da kowane ɗantakara zai ce a muhawarar.
Signaw, kamar sauran yankunan Michigan, cikakkun 'yan Democrat ne a baya - sun goyi bayan 'yantakara kamar: Bill Clinton, Al Gore, John Kerry, Barack Obama and Joe Biden.
Amma zaɓen 2016, lokacin da 'yan Signaw suka zaɓi Trump, ya nuna sauyi.
Jeremy Zehnder na da kamfanin fentin mota, kuma ya ce ba wai ƙoƙari a wurin muhawara ne zai sa mutane su sauya ra'ayi ba, tsadar rayuwa ce.
Kuma akasarin masu zaɓe a yankin kan faɗa wa masu neman jin ra'ayin jama'a cewa sun fi yarda da Trump a kan tattalin arziki.
"Akasarin masu wannan aiki, duk wani da muka sani, na karkatawa zuwa ɓangaren Trump ne," a cewarsa.

Yayin wani taro da ƙungiyar masu harkar motoci ta United Auto Workers Union (UAW) ta shirya inda a nan ne mambobinta suka kalli muhawarar, na haɗu da ɗaya daga cikin jagororinta Joe Losier.
UAW ta goyi bayan Kamala, inda kusan dukkan mambobin ke taɓawa tare da sowa duk lokacin da ta amsa ko ta soki Trump yayin muhawarar.
Amma kuma rarrabuwar kan Amurkawa a bayyane take a nan.
"Mahaifina da duka kawunnaina, waɗanda duka 'yan UAW ne, sun koma 'yan Republican," in ji Mista Losier.
Yayin da ma'aikata ke fargabar rage yawan ayyukan yi, mambobin ƙungiyar na ta samun rarrabuwar kai.
Akwai masu goyon bayan Trump sosai a nan musamman saboda alƙawarin da ya yi cewa zai ƙara haraji kan kayayyakin da ake shigowa da su, da kuma rashin amincewa da batun da Kamala ke yi cewa hakan zai jawo hauhawar farashi.
Bayan kammala muhawarar, na kira Chuck domin jin ko ya yanke shawara.
"Na yarda cewa Kamala na tashe. Kuma da alama ta samu goyon bayana. Ta burge ni game da abubuwan da ta faɗa da kuma yadda ta faɗe su," in ji shi.
"Shi kuma Trump, abin da na tsammata dai shi ya faru. Babu wani abin mamaki. Bai sauya ba. Haka yake."
Har yanzu Rachel Oviedo ba ta yanke hukunci ba, amma dai ta fi tunanin zaɓar Trump.
"Ina ganin zai fi yi mana aiki a nan," a cewarta.
"Ya yi abubuwan da bai kamata ya yi su ba, amma dai za ka iya yafe wa mutum."
Shi kuwa mai fentin mota Jeremy Zehnder, ya aminta cewa Kamala ta ba shi mamaki.
"Ta yi ƙoƙari sosai fiye da yadda na yi tsammani," kamar yadda ya faɗa mani. "Ina ganin ta cinye muhawarar."
Amma fa Trump yake goyon baya, yana mai ceawa magana ake yi ta tsare-tsare, kamar haraji, da tsaron iyaka, da kuma tsadar rayuwa.











