Jirgin fasinja ya yi taho mu gama da helikoftan sojoji a Amurka

Wani karamin jirgin fasinja dauke da mutum 64 ya yi taho mu gama da wani jirgin mai saukar ungulu na soji a yayin da yake daf da sauka a filin tashi da saukar jirage na Reagan da ke Washington DC.
Jirgin ya taso ne daga Wichita da ke Kansas.
Jami'an agaji da 'yan sanda da sauran jami'an tsaro sun isa filin jirgin saman Reagan inda jirgin fasinjan ke dab da sauka.
Wasu jiragen ruwa da ke kashe gobara sun kasance a wajen da lamarin ya afku inda suke neman wadanda suka tsira da ransu kasancewar jiragen sun fada cikin kogi.
Filin jirgin sama na Reagan ya kasance mai yawan hada-hada inda a koda yaushe jirage ke tashi da sauka.
Jami'ai sun ce lamarin ya afku ne da misalin karfe tara na dare agogon Amurka kuma sojoji uku ne a cikin jirgi mai saukar ungulun na soji.
Mahukunta sun ce jirgin mai saukar ungulun na wani atisaye ne a lokacin da lamarin ya afku.
Jami'an ceto na ta neman wadanda suka tsira da ransu a hadarin jiragen.
'Yan sanda sun shaida wa BBC cewa a yayin aikin neman wadanda suka tsira an gano gawawwaki 18 to amma ba a kai ga gano ko mutum guda da rai ba.
Shugaban kamfanin jirgin saman da ya yi hadari Robert Isom, ya bayyana alhininsa da jajensa ga iyalan wadanda wannan iftila'i ya shafa, inda ya ce kamfaninsu na yin duk mai yiwuwa wajen ganin an nemo fasinjojin.
Ya ce za a gudanar da bincike don gano musabbabin hadarin jirgin.
Manyan mutane da 'yan siyasa da sauran shugabanni na ta jajantawa 'yan uwan wadanda wannan lamari ya shafa inda wasunsu ke ta rubuta sakon jajen a shafukansu na sada zumunta.














