Yadda fasinjoji 379 suka fice daga jirgin sama mai ci da wuta cikin daƙiƙoƙi

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:

Fasinjojin sun ruga zuwa kofofin fita daga jirgin saman Japan da ke ci da wuta, ba tare da daukar kayayyakinsu ba, kamar yadda ma'aikatan jirgin suka umarce su.

Barin duk wani abun da suka mallaka ne "kashin bayan" kwashe fasinjojin 379 da aka yi da gaggawa daga jirgin da ya kama da wuta, a filin jiragen sama na Haneda da ke birnin Tokyo a ranar Talata, a cewar masana a fannin sufurin jiragen sama.

Jirgin na Japan mai lamba 516 ya kama da wuta ne a yayin da ya yi karo da wani karamin jirgi na masu kula da gabar teku, a lokacin da jirgin na Japan ke sauka.

Mutane biyar daga cikin mutane shida da ke cikin karamin jirgin sun mutu.

Kwashe dukkanin mutanen da ke jirgin saman na Japan ba tare da wata tangarda ba ya bai wa duniya mamaki ya kuma zama abun yabo.

Masana a fannin sufurin jiragen sama da ma'aikatan jirgin sun shaida wa BBC cewa an cimma hakan ne saboda ma'aikatan sun yi amfani da horon da suka samu a daidai lokacin da ya dace, yayin da fasinjoji kuma suka yi biyayya ga umarnin kare lafiyarsu.

"Ban ga ko daya daga cikin fasinjojin da suka fado kasa daga jirgin dauke da wani kaya ba, a bidiyon da na gani..... Idan da wani ya tsaya daukar kayansa to da ya janyo tsaiko a kokarin fitar da su," a cewar Farfesa Ed Galea, darakta a cibiyar nazarin ayyukan injiniya don kaucewa gobara da ke jami'ar Greenwich.

Inda ya kara da cewa jirgin mai samfurin Airbus A350, ya sa an fuskanci wahalhalu wajen kwashe mutanen.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Wannan jirgin yanayinsa na da wuyar sha'ani saboda kansa ya yi kasa, kuma hakan na nufin fasinjoji sun sha wuya wajen tafiya a cikinsa ," In ji shi.

Abubuwan zamiya uku da basa kamawa da wuta da za a iya amfani da su wajen kwashe fasinjojin, amma ba a iya kaisu kamar yadda ya kamata ba, saboda yadda jirgin ya sauka.

Abun zamiyar na da karfi, abin da yasa za su iya zama masu hatsari.

Haka kuma na'urar sadarwa don sanar da mutane su fice daga jirgin ya daina aiki a lokacin da ake kwashe fasinjojin, sai ma'aikatan suka dinga amfani da amsa-kuwwa suna kuma ihun bayar da umarni, a cewar kamfanin jirgin.

Daya daga cikin fasijojin ya kurkurje, yayin da wasu 13 suka nemi shawarwarin likita saboda ciwon jikin da suka fuskanta, a cewar kamfanin.

Jirgin na kasar Japan ya baro filin jiragen sama na New Chitose da ke birnin Sapporo da misalin karfe hudu agogon kasar, ya kuma sauka a filin jiragen sama na Haneda gab da karfe shida.

Shi kuma karamin jirgin masu gadin bakin tekun yana kan hanyarsa ne na kai kayan agaji ga wadanda girgizar kasar da aka samu a ranar farko na sabuwar shekara ya rutsa da su.

An fara bincike kan hatsarin da ya auku tsakanin jiragen biyu.

Bayanan bidiyo, Fasinjoji sun fice ta ƙofar fitar gaggawa bayan jirgin ya kama da wuta

Tasirin horon bayar da kariya

Tsohuwar ma'aikaciyar kamfanin jiragen sama na Japan ta gaya wa BBC cewa fasinjojin sun yi "matukar sa a."

"Na ji dadi da na ji cewa dukkanin fasinjojin da ke cikin jirgin sun tsira. Amma lokacin da na tuna da hanyoyin da ake bi domin fitar da mutane sai na fara jin tsoro, in ji ta. "Ya danganta da yadda jiragen biyu suka yi karon da kuma yadda gobarar ta bazu, lamarin da ya fi haka muni."

Yadda fasinjoji suka tsallake rijiya da baya daga gagarumar gobarar da ta tashi a jirgin.

Abu mai matukar wuya shi ne tabbatar da cewa fasinjoji ba su dimauce ba, a cewar tsohuwar ma'aikaciyar kamfanin jiragen wadda ta bukaci a boye sunanta.

"Sai dai sun yi namijin kokari, idan aka duba abun da suka yi.

"Yadda suka fitar da duka wanda ke cikin jirgin yana da ban mamaki saboda an samu kyakkyawan tsari a tsakanin ma'aikatan, kuma suma fasinjojin sun bayar da goyon baya wajen bin umarnin da aka basu," a cewarta.

Ta ce duka sabbin ma'aikata sai sun yi horo na tsawon mako uku mai tsauri kan yadda za a kubutar da mutane, kafin a basu damar yin aiki a jiragen sama na kasuwanci.

Haka kuma ana sabunta horon duk shekara.

"Muna rubuta jarrabawa, tattaunawa a kan yadda abubuwa za su iya kasancewa da kuma yin gwaji kan yanayi da dama da zasu iya faruwa a zahiri, kamar idan jirgi zai yi saukar gaggawa a kan teku ko kuma idan an samu gobara.

Su ma ma'aikatan tabbatar da lafiyar jirgin suna yin horon," a cewar matar da ta bar aiki da kamfanin shekaru goma da suka wuce.

Wani matukin jirgin South East Asian airline, wanda shi ma ya nemi a sakaya sunansa ya ce, horo mai tsaurin da ma'aikatan ke samu ya taimaka gaya wajen kwashe fasinjojin jirgin da ya yi hatsarin cikin gaggawa.

"Abun mamaki ne kwarai, ina tunanin cewa abun da ya faru shi ne horon da aka basu ya yi tasiri. Domin basu da wani lokacin tsayawa su yi tunani a yanayin da suke ciki, sai dai kawai aiwatar da abun da suka koya a lokacin horar da su," in ji shi.

Ya kara da cewa: "Kafin ko wani jirgin saman fasinja ya samu amincewa ta kasa da kasa, dole masu kera shi su nuna cewa duk wanda ke cikin jirgin zai iya ficewa a cikin dakikoki 90 ( minti daya da rabi), a wasu lokutan a kan yi amfani da mutane wajen gwada hakan."

Hatsarin jirgi a Japan

Asalin hoton, Reuters

Matukin jirgin ya kuma bayyana cewa an kara karfafa dokokin bayar da kariya a sufurin jiragen sama tun bayan hadduran da aka samu a baya.

Inda ya bayar da misali da karon jirgare samfurin Boeing 747 biyu da aka samu a filin jiragen sama na Los Rodeos a Spaniya a shekarar 1977, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 583, kuma ya kasance hatsarin da ya fi kowanne muni a tarihi.

Lamarin da ya sa aka sake duba yadda ake gudanar da abubuwa a gaban jirgi da kuma tsarin sadarwa ta hanyar waya.

Ya ce abun da aka gano a wannan hatsarin shi ne an samu rashin sadarwa sakanin matukan jirgin da kuma masu kula da sauka da tashin jirage.

Kamfanin jiragen Japan ya taba samun na shi mummunan hatsarin a watan Agustan 1985, a lokacin da wani jirgin mai lamba 123 da ya kamata ya je Osaka ya yi karo da tsauni jim kadan bayan tashinsa daga filin jirage na Haneda da ke birnin Tokyo.

Amma daga bisani aka alakanta hatsarin da matsala daga kamfanin kera jiragen Boeing.

Da farko mutane hudu ne kawai suka tsira daga cikin fasinjoji 524 da ke jirgin.

A shekarar 2006, kamfin jiragen Japan ya bude wani wuri kamar wajen ajiye kayan tarihi a kusa da filin jiragen Haneda, inda ya baje-kolin baraguzan jirgin da ya yi hatsarin don tunatar da ma'aikatansa kan muhimmanci kariya.

"Sakamakon alhini da iyalan wadanda suka mutu suka fuskanta da kuma rashin amincewa da al'umma ke nunawa kan rashin kariya a jiragen sama bayan aukuwar (hatsarin 1985) mun yi alkawarin ba zamu kara barin irin wannan mummunan hadarin ya janyo asarar rayuka ya sake aukuwa ba," Kamfanin ya rubuta haka a shafinsa na intanet.

"Muna tunatar da kowane ma'aikacinmu cewa mutane sun sanya rayukansu masu daraja da dukiyoyinsu a matsayin amana a gare mu."