Yadda faɗa tsakanin mata da miji ya tursasa wa jirgin sama saukar gaggawa

Asalin hoton, Reuters
Hukumomi sun ce jirgin, mai lamba LH 772, wanda aka sauya akalarsa ya sauka a birnin Delhi na ƙasar Indiya ne da ƙarfe 10:26 na safiyar ranar Laraba (29 ga watan Nuwamba)
Kamfanin dillancin labaru na ANI ya ce an ɗauki matakin ne bayan ma'aikatan jirgin sun ce faɗan da ke gudana tsakanin ma'auratan biyu ya fara ƙamari.
Ma'aikatan sun bayyana hakan ne bayan da suka gaza sulhunta lamarin.
Sun kuma ce babu cikakkiyar masaniya kan abin da ya haifar da saɓani tsakanin ma'auratan, waɗanda dukkanin su fasinjoji ne a cikin jirgin da ke tafiya a sararin samaniya.
Kan haka ne aka sauya akalar jirgin daga inda ya nufa zuwa birnin Delhi na Indiya.
Bayan faruwar lamarin, kamfanin jirgin na Lufthansa ya fitar da wata sanarwa, inda a ciki ya ce an fitar da matar da mijinta daga jirgin bayan saukar sa a Delhi, waɗanda asali suke kan hanyarsu ta zuwa Bangkok.
Kamfanin ya ce "Ma'auratan sun nemi afuwa."
Mahukunta ba su tabbatar kan ko za a miƙa ma'auratan da suka tursasa wa jirgin sauka ga jami'an tsaron Indiya ba ne ko kuma za a mayar da ƙasar da suka fito, wato Jamus.
Tun farko jirgin ya yi aniyar sauka ne a Pakistan sanadiyyar hatsaniyar, sai dai bai samu izini ba, lamarin da ya sa jirgin ya sauka a Delhi.
Yadda faɗa ya kacame tsakanin ma'auratan

Asalin hoton, Getty Images
Mijin dai ɗan asalin ƙasar Jamus ne, yayin da ita kuma matar ƴar asalin ƙasar Thailand ce.
Jaridar Indian Express ta ruwaito cewa da farko matar ce ta fara koka wa ma'aikatan jirgin game da halayyar mijin nata.
Ta ce mijin nata yana yi mata barazana, har ma ta buƙaci a taimake ta a fitar da shi daga jirgin, lamarin da ba zai yiwu ba a lokacin kasancewar suna tsakar tafiya ne a sararin samaniya.
Kamfanin dillancin labaru na PTI ya ce faɗan ya fara ne lokacin da mijin ya yi jifa da abincin da aka bai wa matar tasa a cikin jirgin, sannan baya ga haka ya yi ƙoƙarin amfani da leta wajen cinna wa bargon da ta lulluɓa da shi wuta.
Haka nan ya ci gaba da kururuwa yana auna wa matar tasa zagi.
Kamfanin dillancin labarun ya ce mutumin "ya bijire wa duk ƙoƙarin da ma'aikatan jirgin na sulhunta lamarin."
Dalilan da sukan tursasa karkata akalar jirgi

Asalin hoton, Getty Images
Akan karkata akalar jirgi zuwa wani wurin da ba nan ya yi aniyar sauka da farko ba saboda dalilai daban-daban.
Wani lokacin akan sauya akala ko ma a soke tashin jirgi sanadiyyar rashin kyawun yanayi.
Ko kuma sanadiyyar matsalar da ta shafi lafiytar jirgi.
Sai kuma idan aka samu mara lafiya da ke neman agajin gaggawa.
Haka nan kuma akan sauya akalar jirgi idan fasinjoji suka bijiro da wata ɗabi'a da za ta iya kawo hargitsi.
A wasu lokutan kuma ana sauya akalar jirgi sanadiyyar yaƙi ko kuma wani bala'i da ya afku wanda ba a yi tsammani ba.
Sau da yawa sauya akalar jirgi kan haifar da damuwa ga fasinjoji kasancewar zai iya sauya musu shiri.













