Yadda yara huɗu suka yi kwana 40 cikin ƙungurmin daji mai hatsari a Colombia

Rescuer in front of two rescued children in teh jungle

Asalin hoton, Reuters

    • Marubuci, By Matt Murphy
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Da tsakar dare a ranar Juma'ar da ta gabata aka samu saƙon da ɗaukacin al'ummar ƙasar ke jira daga sojoji masu aikin ceto: "Wani babban abin al'ajabi ya faru."

Saƙon da aka samu daga sojojin na cewa an gano wasu yara huɗu da ransu, waɗanda suka ɓace a tsakiyar wani ƙungurmin daji na tsawon kwana 40.

Yaran sun ɓace ne bayan da wani ƙaramin jirgi da suke ciki ya yi haɗari a dajin Amazon, wanda shi ne daji mafi girma a duniya.

Lamarin ya faru ne a safiyar ranar ɗaya ga watan Mayu.

Faruwar haɗarin ya yi sanadiyyar mutuwar mahaifiyar yaran, inda yaran, waɗanda babbarsu ke da shekara 13, sai na biyu mai shekara tara, na ukun na da shekara huɗu, ɗan ƙaramin kuwa na da shekara ɗaya, suka zamo su kaɗai a tsakiyar dokar daji.

Wuri ne wanda ke cike da macizai da damisoshi da kuma dandazon sauro.

Da farko masu ceto sun ɗauka cewar yaran sun mutu, to amma sai suka rinƙa ganin sawun ƙafafunsu da kuma ragowar ƴaƴan itace da suka rinƙa ci, lamarin da ya ƙarfafa wa masu ceton gwiwa.

Daga nan suka yi tunanin cewa akwai yiwuwar yaran suna da rai bayan barin inda hatsarin ya faru.

Yaran sun kwashe mako shida suna tsallake haɗarin miyagun namun daji da yunwa - al'amarin da shugaban ƙasar Colombia ya bayyana a matsayin wani abu da tarihi ba zai taɓa mantawa da shi ba.

Yaran a zaune tare da waɗanda suka ceto su

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Yaran a zaune tare da waɗanda suka ceto su

'Mahaifiyarmu ta ce mu gudu'

Mahaifiyar yaran ta rayu tsawon kwana huɗu bayan haɗarin jirgin kafin ta rasu.

Matar mai suna Magdalena Mucutury ta ce wa 'ya'yanta su tafi ko za su samu agaji, a daidai lokacin da ranta ke fita.

A lokacin da ya zanta da ƴan jarida, mahaifin yaran, Manuel Ranoque ya ce babbar ɗiyarsu ta faɗa masa cewa mahaifiyarsu ta ce "ku tafi domin tsira da ranku."

Ya ce "Abu ɗaya da ya fito fili shi ne (Lesly - mai shekara 13) ta tabbatar min cewa mamarsu ta rayu har tsawon kwana huɗu."

"Kafin ta mutu, mamar tasu ta ce "ku tafi, ku fita daga nan. Za ku ga wani mutum mai tausayi kamar mahaifinku, kuma zai kula da ku kamar yadda na kula da ku." In ji shi.

'Yaran daji'

Idan har akwai wasu yara da za a ce sun shirya wa wannan haɗari, to ba za su wuce waɗannan yara ba, domin kuwa sun fito ne daga wata ƙabila da ake kira Huitoto.

Ƙabilar Huitoto mutane ne da kan koyi farauta da kamun kifi tun suna ƙanana.

Kakan yaran, Fidencio Valencia ya shaida wa ƴan jarida cewa manya guda biyu daga cikin yaran, Lesly da Soleiny sun saba da dajin.

A lokacin da ta zanta da kafofin yaɗa labaru na Colombia, ƴar'uwar iyayen yaran, Damarys Mucutuy ta ce iyalan kan rinƙa yin wasan yadda za su tsira daga haɗari a lokacin da yara ke tasowa.

Ta bayyana cewa babba daga cikin yaran ta san irin ƴaƴan itacen da suka kamata a ci, domin kuwa akwai ƴaƴan itatuwa da dama a cikin dajin waɗanda suke da guba. Kuma ta san yadda za ta kula da yara.

Fidencio Valencia

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Fidencio Valencia ya shaida wa manema labaru cewa a lokacin da suke tasowa, yaran sun koyi yadda za su kula da kansu a cikin daji
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan da haɗarin ya faru, Lesly ta haɗa wata ƴar bukka da itace da ganye, ta ɗaure su da ɗankwalinta.

Daga nan sai ta kwaso wani gari daga jikin jirgin nasu da ya yi haɗari, garin ne suka rinƙa ci har ya ƙare, inda suka koma cin ƴaƴan itatuwa.

Wani mutumin ƙauye, wanda ke cikin waɗanda suka shiga aikin ceton ya ce yaran sun rinƙa cin wani ƴaƴan itace mai kama da 'passion', sun rinƙa tafiya har ta fiye da kilomita ɗaya wajen neman ƴaƴan itacen."

Astrid Cáceres, shugaban Hukumar Kula da Walwalar Iyali ta Colombia ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da ƴaƴan itatuwa suka nuna, wanda hakan ya ba su damar cin irin waɗannan ƴaƴan itace.

Sai dai sun fuskanci ƙalubale na rayuwa a wuri mai haɗari.

Lokacin da ya tattauna da BBC, wani masani kan al'ummar da ke zaune a kusa da dajin, Alex Rufino, ya ce yaran sun kasance ne a ɗaya daga cikin yankin dajin mafi duhu, wanda ke ƙunshe da manyan itatuwa.

Ya ce akwai ganyaye masu guba da yawa a wurin, kuma yanki ne wanda ba a cika zuwa ba.

Baya ga ƙoƙarin kauce wa namun daji masu haɗari, yaran sun kuma fuskanci ruwan sama da aka rinƙa shatatawa da kuma tsallake haɗarin ƴan fashi waɗanda kan yi ta'annati a cikin dazukan.

Shugaban ƙasar ya ce akwai lokacin da yaran suka yi artabu da kyarkeci.

Yadda jirgin na Cessna 206 ya faɗakan itace kan ya yi ƙasa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Jirgin Cessna 206 wanda yaran suka yi haɗari a ciki

Sai dai Rufino ya ce yaron da ya kai shekara 13, wanda ya taso a cikin al'umma mazauna irin wannan yanki dole ne ya kansance yana da dabarun ruyuwa a cikin irin wannan yanayi.

Wani shugaban al'umma a yankin da iyayen yaran suka samo asali ya ce "yaran sun taso ne a wurin kakarsu."

"Sun yi amfani ne da dabarun da suka koya daga kakannisu wajen tsira daga halin da suka shiga."

Ceto mai cike da ƙalubale

A lokacin da ake gudanar da aikin ceto, al'umma sun rinƙa sukar gwamnati saboda tafiyar hawainiya da aikin ke yi.

An yi wa shugaban ƙasar ca, bayan da aka wallafa cewa an ceto yaran a shafinsa na twitter, alhali kuwa ba hakan ba ne.

Gwamnati ta jefa takardu 10,000 ɗauke da bayanai kan yadda mutum zai tsira a a cikin daji mai haɗari, sannan an ɗauki muryar kakarsu, inda aka rinƙa kunnawa ta lasifika daga cikin jerage masu saukar ungulu a cikin dajin domin tabbatar wa yaran cewa ana neman su.

Jagoran tawagar masu binciken, Janar Pedro Sanchez ya ce akwai wasu lokuttan da masu ceton suka gifta kusa-kusa da yaran ba tare da sun gan su ba.

A lokacin da aka ga yaran, kimanin sojoji 150 da kuma masu aikin sa-kai 200 ne suka bazu a cikin dajin suna neman su, wanda ya kai faɗin murabba'in kilomita 300.

A ranar Juma'a, bayan kwashe wata guda ana nema, wani kare mai taimakawa wajen neman yaran ya gano su.

Wani bidiyo ya nuna yadda aka ɗauki yaran cikin jirgi mai saukar ungulu, aka ratsa ta tsakankanin dogayen itatuwa da su zuwa sama, inda daga nan aka kai su Bogota, babban birnin ƙasar.

Daga nan ne kuma motocin ɗaukar marasa lafiya suka ƙarasa da su zuwa asibiti domin samun kulawa.

Iyalan yaran sun nuna godiya ga masu aikin ceto, haka nan shio ma shugaban ƙasar.

Yayin da da dama daga cikin al'ummar ƙasar ta Colombia, waɗanda akasarinsu mabiya addinin kirista ne, ke alaƙanta tsirar yaran da 'Ikon Allah,' Mr Rufino, masani kan mazaunan yankin ya ce yadda suka rayu a dajin na da alaƙa ne da 'sabon da suka yi da rayuwa a irin waɗannan dazuka.'

"Ba ganyaye ne kawai a cikin dajin ba, akwai rauhanai waɗanda suka saba da al'ummar yankin, suna rayuwa a tare kuma suna taimaka wa juna,: in ji shi.

Ya ƙara da cewa "abu ne mai wuyar fahimta, na san da haka, amma wannan wata dama ce ta neman ilimi kan abubuwa daban-daban da suka shafi abubuwan da ke rayuwa a duniya."

"Mahaifiyarsu (wadda ta mutu bayan haɗarin) ta zame musu kariya. Kuma sai yanzu ne za ta kwanta ta huta." In ji shi.