An haramta amfani da wuta a matsayin hanyar sharar daji a Brazil

Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin Brazil ta haramta amfani da wuta a matsayin hanyar sharar daji har sai bayan kwanaki 60.

Wannan ya zo ne a matsayin wani mataki na shawo kan wutar dajin da ke ci a dajin Amazon.

Shugaba Bolsanaro na kasar ne ya sa wa dokar hannu, wanda shugaban ya sha caccaka a ciki da wajen kasar dangane da gazawa wajen kare dazukan kasar.

Ana sa ran za a sanar da wasu sabbin matakai na kare muhalli a kasar a mako mai zuwa.

Dajin Amazon yana da girman murabba'in kilomita miliyan 5 da rabi, shi ne dajin da ya fi kowanne girma a duniya, kuma dajin yana a kasar Brazil ne da ke kudancin nahiyar Amurka.

Idan aka kwatanta, dajin ya fi girmar nahiyar Turai baki dayanta.

Ana wa dajin Amazon take da cewa shi ne 'mabubbugar iskar da dan'adam ke shaka' ta duniya.

Yana kunshe da nau'ukan tsirrai da halittu daban-daban kimanin miliyan 3.

Akwai mutane kauyawa miliyan daya da ke zama a kungurmin dajin.

Dajin yana taka muhimmiyar rawa wajen zuke sanadarin Carbon mai illa ga dan'adam.