Mutumin da ya makale a tayar jirgin sama daga Afirka ta Kudu zuwa Holland ya isa lami lafiya

Asalin hoton, Getty Images
'Yan-sandan Holland sun ce sun sami wani mutum da ya makale a tayar jirgin sama wanda ya tashi tun daga Afirka ta Kudu ya sauka a Amsterdam a raye.
Jiragen sama na tafiyar sa'a 11 daga Johannesburg zuwa Amsterdam, kuma wannan jirgin na dakon kaya ana ganin ya yada zango ne sau daya kawai a Nairobi, Kenya.
Abu ne mai wuyar gaske ga mutumin da ya makale a tayar jirgin sama ya rayu a doguwar tafiya, saboda tsananin sanyi da kuma karancin iskar shaka a can sama
Ba a gane shekaru da kasar mutumin ba in ji 'yan-sanda.
Mai magana da yawun 'yan-sandan rundunar sojin Holland Joanna Helmonds ta gaya wa kamfanin dillancin labarai na AFP : "An samu mutumin da ransa a ramin tayar gaba ta jirgin, kuma aka ɗauke shi zuwa asibiti cikin hayyacinsa.
Ta ce "Abu ne mai matukar mamaki ganin cewa mutumin har yanzu yana raye, amma yanzu dai ana kula da mutumin a asibiti.''
Ta kara da cewa ana sa ran mutumin zai nemi mafaka a Holland, amma dai abu mafi muhimmanci a yanzu shi ne kula da lafiyarsa.
Mai magana da yawun kamfanin jirgin saman na dako Cargolux na Italiya ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, jirgin wanda ya taso daga Johannesburg zuwa filin jirgin Schiphol da ke Holland ranar Lahadi ya yada zango a Nairobi.
Abin da ba a sani ba shi ne ko a Afirka ta Kudu mutumin ya ɗane jirgin ko kuma a Kenya, amma dai yanzu 'yan sanda na gudanar da bincike a kai.











