Yadda fasinja ya fitsare wata mata a jirgin sama

Asalin hoton, ANI
Shugaban kamfanin Tata Sons na ƙasar India ya nuna ɓacin ransa kan wani lamari da ya faru inda wani mutum da ke cikin maye ya yi fitsari kan wata fasinja a cikin jirgin sama mallakar kamfanin.
Lamarin ya faru ne a ƙarshen watan Nuwamba a cikin jirgin na Indiya amma sai a makon da ya gabata ne aka bayar da rahoton faruwar lamarin.
Labarin faruwar lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce matuƙa kan yadda aka yi jirgin ƙasar Indiya ya bari wannan lamari ya faru.
An kama mutumin a ƙarshen makon da ya gabata haka kuma an kore shi daga wurin aikinsa da yake yi a Amurka.
A wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, shugaban kamfanin Tata Sons Chandrasekaran ya bayyana cewa ya kamata a ce jirgin saman ya yi sauri wurin mayar da martani kan lamarin da ya faru.
"Za mu duba mu gyara komai domin ganin mun kiyaye afkuwar irin waɗannan lamuran a nan gaba," in ji shi.
Batun nasa na zuwa ne kwana guda bayan shugaban kamfanin Air Indiya Campbell Wilson ya bayyana damuwarsa kan irin wahalar da kwastomar jirginsu ta sha kan wani abu da wani fasinja ya yi mata.
Lamarin ya faru ne a ranar 26 ga watan Nuwamba a sashen masu zama a babbar kujera ta jirgin saman.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wanda ake zargin mai suna Shankar Mishra ana zarginsa da yi wa wata mata yar shekara 72 fitsari.
"Kayana da takalmana da jakata duka sun jiƙe da fitsari," kamar yadda matar da ka ayi wa fitsarin ta rubuta a takardar koken da ta aika wa Mista Chandrasekaran washe gari.
Matar ta ce ta buƙaci ma'aikatan jirgin da a sauya mata kujera, amma an shaida mata cewa babu wata kujerar, sai dai a maimakon haka aka sauya mata da wata ƙaramar kujera da ma'aikatan jirgin suke amfani da ita.
Ta yi zargin cewa hasali ma ma'aikatan jirgin ne ma suka kai mata mutumin ba da son ranta ba domin ya ba ta haƙuri.
Matar ta bayyana tafiyar da suka yi a jirgin a ranar a matsayin abin da ya fi ɗaga mata hankali a rayuwa, inda ta ce kamfanin jirgin abin da ya yi mata kawai shi ne mayar mata da wani ɗan kaso na kuɗin tikitin ta.
Sai dai akwai wani likita ɗan Amurka da ake kira Sugata Bhattacharjee da ya tallafa mata da kuɗi wanda a jirgin ya zauna ne a kusa da ita.
Ya bayyana wa kafar watsa labarai ta NDTV cewa shi ma kansa ya rubuta takardar koke zuwa Air Indiya a ranar da lamarin ya faru amma babu matakin da aka ɗauka.
Bayan faruwar lamarin, sai Air Indiya ya kafa wani kwamiti na ƙasa da ƙasa domin gudanar da bincike kan Mista Mishra.
Bayan mako biyu, sai ta saka wani takunkumi na kwanaki 30 a kan shi - tsawon takunkumin da aka saka na ɗaya daga cikin abubuwan da suka jawo tashin hankali bayan da labarin ya bazu.
Bayan iyalan matar da aka yi wa fitsari sun shigar da ƙara, sai kamfanin jirgin ya gabatar da ƙara a gaban ƴan sanda kan lamarin a ranar 28 ga watan Disamba.
An kama Mista Mishra a Bangalore a ranar Asabar inda ake zarginsa da laifuka ciki har da cin zarafi ta hanyar lalata da kuma rashin ɗa'a a bainar jama'a.
Daga baya sai aka kai shi Delhi aka kuma gurfanar da shi a gaban kotu wadda daga baya ta aika shi gidan yari na makonni biyu.
Kafin a kama shi, Mista Mishra ya fitar da sanarwa ta hanyar lauyansa inda ya ce ya sa an wanke jakar matar da kuma kayanta kwanaki biyu bayan faruwar lamarin











