Manhajar AI ta DeepSeek za ta sa Kamfanonin fasahar Amurka su farga - Trump

Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana bunƙasar kamfanin ƙasar China mai suna DeepSeek a matsayin abin da zai sa kamfanonin fasaha na Amurka su farga, bayan bayyanar ƙirƙirarriyar basirarsu ta AI ta tilasta faɗuwar hannayen jari.

Farashin hannayen jari a manyan kamfanonin fasaha kamar Nvidia ya fadi, wanda ya janyo wa kamfanin haɗa ƙwaƙwalwar kwamfuta na Amurka, Nvidia asarar kusan dala biliyan dari shida.

Abin da ya girgiza sashen fasahar shi ne iƙirarin da DeepSeek suka yi na cewa an samar da samfurin R1 ne da wani kaso na farashin abokan hamayyarsa, inda ya sanya alamar tambaya game da makomar mamayar da Amurka ta yi wa ƙirƙirarriyar basirar AI da kuma girman jarin da kamfanonin Amurka ke shirin sanyawa a ɓangaren fasahar.

DeepSeek ya zama manhajar kyauta da aka fi saukewa a wayoyi a Amurka mako guda bayan ƙaddamar da manhajar.

Da yake mayar da martani game da labarin, Trump ya ce cigaban baya-bayan nan da ake samu a fannin ƙirƙirarriyar basira ta China zai iya kasancewa abu mai kyau ga Amurka.

'' Idan za ku iya samar da shi da rahusa, kuma za ku iya yin shi ƙasa da yadda aka saba kuma ku samu sakamako mai kyau a ƙarshe, ina tunanin wannan abu ne mai kyau a gare mu,'' a cewarsa ga manema labarai a cikin jirgin shugaban ƙasa na Air Force One.

Ya kuma ce wannan gagarumar nasarar ba ta dame shi ba, inda ya kara da cewa Amurka za ta ci gaba da kasancewa babban jigo a fannin.

DeepSeek na samun ƙarfin yin aiki ne daga samfurin open source DeepSeek-V3, wanda masu bincikensa suka ce an horar da shi da kimanin dala miliyan shida, ƙasa da biliyoyin da abokan hamayyarsu suke kashewa. Sai dai wasu da dama a fannin na AI sun musanta hakan.

Bayyanarsa na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta takaita sayar da fasahar da ke haɓaka ƙirƙirarriyar Basira ta AI ga kasar China.

Domin cigaba da aikinsu ba tare da samun wannan fasahar daga Amurka a kai a kai ba, masu ƙirƙirar AI a China sun rarraba ayyukansu ga juna kuma sun yi gwaje-gwaje da dama da sabbin dabarun samar da fasahar.

Hakan ya sa aka fara samar da ƙirƙirarriyar basirar da ba sa bukatar kayyakin kwamfuta da ake amfani da su a baya.

Hakan kuma na nufin farashinsu bai kai yadda ake tunani a baya ba, wanda hakan ke da yiwuwar sauya masana'antar.

Wa ya kafa DeepSeek?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Liang Wenfeng ne ya kafa kamfanin a shekarar 2023 a Hangzhou, wani birni da ke kudu maso gabashin China.

Ɗan kimanin shekara 40 ɗin, wanda ya karanci fannin injiniyan lantarki , shi ne kuma ya kafa asusun hannun jarin da ke goyon bayan DeepSeek.

A kwanakin baya an gan shi a wani taro tsakanin ƙwararru a fannin da kuma firimiyan China Li Qiang.

A wata hira da ya yi da The China Academy a watan Yulin 2024, Mista Liang ya ce ya yi mamaki kan yadda aka karɓi samfurin baya na ƙirƙirarriyar basirarsa.

'' Ba muyi tsammanin farashi zai zama wani babban al'mari ba.'' inji shi.

'' Muna yin abu ne dai-dai ikonmu, mu ƙirga ƙuɗin da muka kashe mu kuma sanya farashi bisa hakan.''

Bayan faduwar hannayen jari a kasuwannin a ranar Litinin a Amurka, hannayen jari a kamfanonin ƙirƙirarriyar basirar AI da ke Japan kamar Advantest, da Softbank da Tokyo Elctron sun faɗi warwas a ranar Talata, wanda ya taimaka wajen rage ma'aunin kasuwar na Nikkei 225 ya saura da kashi 1.4.

Wasu daga cikin kasuwanni a Asiya na rufewa saboda hutun sabuwar shekarar da ake amfani da wuta.

Wasu kasuwannin ƙuɗi na China za su rufe daga Talata, kuma za su sake buɗewa a ranar 5 ga watan Fabrairu.

Bayan ƙaddamar da samfurin DeepSeek-R1 a farkon watannan, kamfanin ya yi taƙamar cewa suna aiki kafaɗa da kafaɗa da ɗaya daga cikin sabbin samfurin OpenAI idan za ayi aiki da shi a fannin lissafi, ƙundin saƙonni na na'ura (Coding) da kuma iya fahimtar ɗan Adam.

Mutane masu muhimmanci da dama, ciki har da shugaban ƙirƙirarraiyar basirar OpenAI, Sam Altman sun yaba wa fasahar DeepSeek, wadda ya ƙira 'samfuri mai ban sha'awa, musamman kan abin da suka iya samarwa a wannan farashin'', duk da dai ya ce kamfaninsa na OpenAI ''zai samar da samfurin da suka fi wannan'' nan gaba.

'' Iya yin goggaya da AI samfurin Amurka da DeepSeek ya yi, duk da rashin samun kayyayakin aiki, na nuna ƙirƙirar sabbin hanyoyi da amfani da bayanai yadda ya kamata zai iya maye gurbin rashin samun wasu kayyayakin aiki, inji Marina Zhang, malama a jami'ar fasaha da ke Sydney, wadda ta mayar da hankali kan manyan kamfanonin fasaha da ke China.

Ion Stoica, ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa kamfanin Databricks, kuma shugaban kamfanin ya shaidawa BBC cewa rahusan da DeepSeek ke da shi zai karfafawa ƙarin kamfanonin da zasu rungumi amfani da AI a kasuwancinsu.

'' Idan hakan ya faru, wannan ragin farashin zai hanzarta cigaban AI, inji shi.

'' baki ɗaya dai kasuwan AI zai faɗaɗa cikin sauri, kuma darajar kasuwar zata bunƙasa cikin hanzari.''

Kamfanin na China na iƙirarin cewa za'a iya horar da samfurin su da fasahar da ke habaka kirkirarriyar Basira ta AI na musamman guda 2,000, ba kamar samfurin da akeyi a baya ba da aƙalla ake amfani da fasahar da ke habaka kirkirarriyar Basirar guda 16,000.

Sai dai ba kowa ba ne ya gamsu ba. Wasu na da shakku kan wasu abubuwan da DeepSeek sukayi iƙirari, ciki har da jigo a fannin fasahar zamani Elon Musk.

Ya mayar da martani ne kan wani abu da aka wallafa da ke iƙirarin DeepSeek na da aƙalla fasahar da ke haɓɓaka AI (chips) na kamfanin Nvidia guda 50,000 wanda a yanzu an haramta shigar da shi China, inda ya ce :'' ba shakka.''