Abin da ya sa tauraruwar Sharuhkhan ke ci gaba da haskawa duk da sauyin zamani

Khan

Asalin hoton, Getty Images

A watan jiya ne jarumin fina-finan Indiya Shah Rukh Khan ya yi bikin cika shekaru 30 a masana’antar shirya fina-finan ƙasar. Shrayana Bhattacharya, wanda ya rubuta littafi kan shaharar jarumin na Bollywood, ya bayyana dalilin da ya sa har yanzu yake cikin manyan jaruman fina-finai a duniya.

Ba abu ne mai sauƙi a iya bayar da wani ƙwaƙƙwaran dalili kan tsawon rayuwar Khan a masana'antar fim ba. Miliyoyin mutane suna ƙaunar jarumin ba tare da wata shakka ba har ta kai ga jama’a na kallonsa amatsayin uban gidan jarumai, ko taurari.

Amma me ya sa ake tsananin ƙaunar Khan ?.

Kamar a fina-finansa, amsar ita ce soyayya da jin dadi, Khan ya kasance yana bayyana wa duniya mafi kyawun abin da Indiya da Kudancin Asiya za su iya zama nan gaba. Yana nuna nahiyar da ya fito a matsayin wani yanki mai wadata da mutuntaka da zai iya rayuwa cikin farin ciki ba tare da wata damuwa ba.

Ga miliyoyin ƴan Indiya, shi ma ya kasance kan gaba a labarin ci gaban tattalin arzikin kasar.

A shekarun 1990 Khan ya fara bayyana a akwatunanmu na talabijin a daidai lokacin da Indiya ta shiga sahun kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya. Kuma ya ci gaba da bunkasa, da kuma taimaka wa wajen bunkasar tattalin arzikin kasar.

A wani bangare na sauye-sauyen tsarin kasuwanci a Indiya, kasar ta bude bangaren sadarwa don zuba jari ga ƴan kasashen waje wanda hakan ya ba wa kafafen talabijin na kasashen waje damar watsa shirye-shirye da fina-finai da harshen kasar, wadannan fashoshi sun rika watsa fina-finan Khan da wakokinsa da hirarrakinsa, har ta kai ga sun shiga gidaje fiye da duk wani shahararren fim da ya riga shi.

Yayin da Indiya ta sami 'yanci na tattalin arziki kamfanoni da dama sun shiga harkar, kuma sun riƙa ɗaukar Khan a matsayin jakadansu don tallata musu haja.

A wannan lokaci matsayin Khan ya tashi daga wani shahararren dangi da ke birnin Delhi zuwa tauraron duniya na kasar Indiya.

Yayin da ƴancin addini ke haɓaka a wannan lokaci, Khan ya zamo wani mai sassaucin ra’ayi da yawancin Indiyawa ke ƙoƙarin riƙewa.

Khan

Asalin hoton, Reuters

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masu suka dai sun ce rashin hakuri na karuwa a karkashin gwamnatin firaminista Narendra Modi ta Hindu mai kishin kasa, wadda ake zargi da mayar da musulmin Indiya saniyar ware.

An kama dan Khan, Aryan Khan, a shekarar da ta gabata, a kan shari’ar miyagun kwayoyi, kuma daga karshe an wanke shi, a wani lamari da da yawa ke gani a matsayin musguna wa fitaccen musulmin Indiya.

Duk da haka, magoya bayansa sun ƙi su riƙa kallonsa a matsayin wani mai tsatstsauran ra’ayin addini, maimakon haka, suna ganinsa a matsayin mai hikima, wayo, da nasara.

Tattaunawa game da hare-haren tsangwama kan addininsa da kuma yadda ake da mabiya addinai daban daban a danginsa na nuna cewa shi mai sassaucin ra’ayi ne.

Abu mafi muhimmanci ma shine jarumin na yin uzuri, da kuma amincewa da rauninmu na ƴan adam.

Yawanci Khan na fitowa ne a matsayin mai rauni da iya soyayya a fina-finai, ga jarumta mai rauni, miji mai rauni, musulmi mara ƙarfi, har ma da mugu mai rauni.

Khan gwanin iya soyayya ne a fim, mutane da dama na koyi da irin soyayyarsa a fina-finai.

Bayanai sun nuna cewa mata sun fi jin dadin rawar da yake takawa a Bollywood fiye da kowanne jarumi namiji.

Shahrukh Khan

Asalin hoton, Getty Images

Mutanen da ke kallon fina-finansa na jin daɗi sosai, koyaushe suna kwatanta kansu da yanayin da yake ciki, suna zubar da hawaye da yawa. Marubutan fina-finai sukan yi tsokaci kan yadda Khan ke iya sharba kuka fiye ma da yawancin jaruman duniya, yadda idanunsa idanunsa ke cika da hawaye su zama abun tausayi na sa mutane na tausayinsa, kuma ya shiga zuciyarsu ƙwarai.

Bayan fina-finai, hirar da ya yi a talabijin da lakcoci sun kara masa barkwanci da tawali'u.

Na san mutane da yawa da suka fi jin dadin hirarrakinsa fiye da fina-finansa. Waɗannan tattaunawar ta kafofin watsa labarai suna nuna mafi kyawun aikin jarumin.

A cikin duniyar da ba ta da tabbas da takurar gaske, Hotunan Khan na faranta wa mutane rai.

Bayan wani dan lokaci, jarumin yana da manyan fitattun fina-finai guda uku da aka tsara fitarwa a shekarar 2023. Masoyansa sun yi murna da farin ciki, amma kuma suna damuwa da yadda kafafen watsa labarai ke neman ganin mutane sun kaurace wa fina-finansa saboda addini.

Yayin da siyasa ta rikice ta tsananta, jarumin na da rawar takawa kan yadda za a iya hada kan jama’a.