Man United ta ƙi sabunta kwantiragin Maguire, za a bayar da aron Bellingham

Asalin hoton, BBC Sport
Newcastle United na duba yiwuwar dawo da dan wasan tsakiya na Ingila Elliot Anderson, mai shekara 22, zuwa kulob din, bayan sayar da shi ga Nottingham Forest a shekarar 2024. (i Paper)
Har yanzu Manchester United na sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Jamus Angelo Stiller, mai shekara 24, amma ana sa ran Stuttgart ta nemi dan wasan mai shekaru 24 ya zarce €50m (£43.5m). (Sky Sports Germany)
Manchester United na sha'awar dan wasan tsakiya na Atletico Madrid, Conor Gallagher, don dan wasan mai shekaru 25 ya maye gurbin takwaransa na Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20. (Football Insider)
Dan wasan baya na Ingila Harry Maguire na iya barin Manchester United kyauta idan kwantiraginsa ya kare a bazara mai zuwa saboda har yanzu kulob din na Old Trafford bai yi wa dan wasan mai shekaru 32 tayin sabon kwantiragi ba. (Mail)
Aston Villa da Newcastle United na daga cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan Porto da Spain Samuel Omorodion, mai shekara 21, wanda a baya ya kusa komawa Chelsea kuma ya tattauna da Nottingham Forest. (A Bola Portuguese)
Dan wasan bayan Ingila Fikayo Tomori yana tattaunawa da AC Milan kan sabon kwantaragi, dan wasan mai shekaru 27 ya ce baya son barin kungiyar ta Seria A. (Fabrizio Romano)
Ana tunanin dan wasan Faransa Jean-Philippe Mateta, mai shekara 28, zai so barin Crystal Palace, inda ake sa ran zai iya komawa Manchester United, ko Newcastle United ko Tottenham. (Football Insider)
West Ham na zawarcin dan wasan gaban Netherlands Joshua Zirkzee, mai shekara 24, kuma za su iya kokarin dauakr shi a matsayin aro daga Manchester United a watan Janairu. (i Paper)
Borussia Dortmund iya bayar da aron dan wasan tsakiyar Ingila, mai shekara 20, Jobe Bellingham, wanda suka sayo daga Sunderland a bazarar da ta gabata a watan Janairu. (Football Insider)
Har yanzu dan wasan tsakiyar Ingila Samuel Alker, mai shekara 16 bai amince ya kulla yarjejeniya da Leeds United idan ya cika shekaru 17 a watan Maris ba, kuma yana jan hankalin Borussia Dortmund da Bayer Leverkusen. (Mail)











