Chelsea na zawarcin Omorodion, Arsenal na son N'Guessan

Asalin hoton, Getty Images
A shirye Chelsea take ta mika tayin sama da Yuro miliyan 100 (£87m) don sayen dan wasan gaban Spain Samuel Omorodion mai shekaru 21 daga Porto a bazara mai zuwa. (Fichajes)
Wasu da ba a san ko su waye ba daga Hadaddiyar Daular Larabawa sun tuntubi manyan 'yan wasan kungiyar Manchester United Eric Cantona da Wayne Rooney da David Beckham domin neman sayan kungiyar. (Guardian)
Ana sa ran dan wasan gaban Argentina Lionel Messi, mai shekara 38, zai rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya da Inter Miami. (Fabrizio Romano)
Arsenal da Tottenham na daga cikin kungiyoyin Premier da ke son dauko dan wasan gaban Saint-Etienne dan kasar Faransa Djylian N'Guessan mai shekaru 17. (Cought Offside)
Dan wasan Getafe dan kasar Sipaniya Luis Milla, mai shekara 31, ya ja hankalin Aston Villa Unai Emery da kocin Atletico Madrid Diego Simeone a kakar wasa ta bana. (Fichajes)
Wakilan Barcelona sun kalli tsohon dan wasan gaban Ingila Mason Greenwood, mai shekara 21, a wasan da ya ci wa Marseille kwallaye hudu a karshen mako. (TBR Footbal)
Bournemouth ta shirya tsaf don ci gaba da karbar tayin dan wasan gaban Ghana Antoine Semenyo, mai shekara 25, a kasuwar musayar 'yan wasa a nan gaba. (Football Insider)
Newcastle da Aston Villa ne kan gaba cikin wadanda ke zawarcin dan wasan bayan Ecuador Joel Ordonez, mai shekara 21, daga Club Brugge. (Cought Offside)
Manchester United na shirin ba wa Casemiro sabon kwantiragi amma duk wata yarjejeniya za ta nemi rage albashin dan wasan tsakiyar na Brazil, mai shekara 33. (Football Insider)
Kyaftin din Manchester United Bruno Fernandes na tunanin barin kungiyar a karshen kakar wasa ta bana idan ba su samu ci gaba ba. Bayern Munich na son dauko dan wasan tsakiyar na Portugal mai shekaru 31. (Fichajes)










