Inter ta yi watsi da bukatar Neymar, Crystal palace na shirin rabuwa da Guehi

Neymar

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Inter Milan ta yi watsi da raɗe-raɗin cewa tana shirin sayen ɗan wasan Brazil Neymar, mai shekara 33, a watan Janairu, yayin da kwantiraginsa ke shirin ƙarewa a Santos. (Corriere dello Sport)

Crystal Palace na shirin cefanar da ɗan wasan bayan Ingila Marc Guehi a watdaan Janairu, kuma a halin yanzu ba Liverpool ce kan gaba a jerin ƙungiyoyin da ke bibiyar ɗan wasan mai shekara 25 ba, Barcelona da Real Madrid da Bayern Munich duk sun bayyana sha'awarsu. (The I paper)

Dan wasan tsakiya na Ingila da Crystal Palace Adam Wharton, mai shekara 21, ya kasance wanda Manchester United ta fi sha'awar ɗauka a watan Janairu, duk da cewa farashinsa zai iya kai wa kusan fam miliyan 70. (Teamtalk)

Everton ta yi watsi da tayinda Liverpool da Chelsea suka miƙa a bazarar da ta gabata kan ɗan wasan bayan Ingila Jarrad Branthwaite mai shekaru 23. (Mail)

Tottenham da Liverpool na zawarcin ɗan wasan gaban Bournemouth da Ghana Antoine Semenyo, mai shekara 25. (Talksport)

Kocin Manchester United Ruben Amorim na matuƙar sha'awar ɗaukar ɗan wasan bayan Italiya da Inter Milan Federico Dimarco, mai shekara 27, amma a halin yanzu ɗan wasan ya fi ba da fifiko kan ci gaba da zama a filin wasan San Siro. (Tuttosport)

Sunderland ba za ta miƙa wani sabon tayi kan ɗan wasan bayan Bologna da Colombia Jhon Lucumi ba a kasuwar musayar ƴan wasa ta watan Janairu, bayan da aka ki amincewa da tayin £24m da ta gabatar kan ɗan wasan mai shekara 27 a bazarar da ta gabata. (Sky Sports)

Har yanzu golan Barcelona Marc-Andre ter Stegen bai yanke shawara kan ko zai ci gaba da zama a ƙungiyar a watan Janairu ba, dan ƙasar Jamus mai shekara 33 ya na sha'awar taka leda kafin gasar cin kofin duniya ta bazara mai zuwa. (Florian Plettenberg)

Juventus na son dawo da ɗan wasan tsakiya na Italiya Sandro Tonali zuwa Serie A amma Newcastle ta kuduri aniyar ci gaba da riƙe ɗan wasan mai shekara 25. (Football Insider)

RB Leipzig ta lafta farashin Yuro miliyan 100 kan ɗan wasan Ivory Coast Yan Diomande mai shekara 18. (Sky Germany)

Ba a sa ran Wolves za ta yi wani gagarumin cefanen ƴan wasa a watan Janairu kuma mai yiwuwa ta iya riƙe manyan ƴan wasanta, ciki har da ɗan wasan tsakiya na Brazil Andre, mai shekara 24, wanda Juventus ta yi zawarci a bara. (Mail)