Man United ta yi wa Fernandez farashi, Liverpoool na zawarcin Williams

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta ƙaƙaba farashin fam miliyan 40 kan kyaftin ɗin ta Bruno Fernandes, mai shekara 31, a daidai loakcin da ake alaƙanta Bayern Munich da ɗan wasan tsakiyar na Portugal. (Teamtalk)
Liverpool na shirin miƙa tayin yuro miliyan 90 don siyan ɗan wasan gaban Sifaniya da Athletic Club Nico Williams, mai shekara 23. (Fichajes)
Ana kuma sa ran Liverpool ɗin za ta nemi ɗan wasan bayan Borussia Dortmund da Jamus Nico Schlotterbeck, mai shekara 25 a bazara mai zuwa. (Sports Illustrated)
Barcelona na nazari kan ɗan wasan Juventus da Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 25, wanda kwantiraginsa zai ƙare a bazara mai zuwa. (AS)
Har ila yau, Bayern Munich ta ce za ta iya siyan Vlahovic, yayin da zakarun na Jamus, ke fargabar cewa wata ƙungiya na iya neman ɗauke ɗan wasan gaban Ingila, Harry Kane, mai shekara 32. (Mirror)
Dan wasan Ingila da Nottingham Forest Elliot Anderson, mai shekara 22, na cikin jerin sunayen ƴan wasan da Newcastle ke sha'awar ɗaukowa a bazara (Mail)
Real Madrid sanya ido kan ɗan wasan baya na Bayern Munich Dayot Upamecano, mai shekara 26, inda kwantiragin ɗan ƙasar Faransan zai ƙare a bazara mai zuwa (Fichajes - in Spanish)
Real Madrid za ta iya aika Endrick, mai shekara 19, zaman aro a watan Janairu, amma ba yi wa West Ham kallon makomar da ta fi dacewa da ɗa wasan na Brazil. (Team Talk)
Barcelona na nazari kan ɗan wasan gaban Hoffenheim da Kosovo Fisnik Asllani, mai shekara 23, wanda zai iya barin ƙungiyar ta Jamus a bazara mai zuwa. (Sky Germany)
Ɗan wasan tsakiya na Red Bull Salzburg, Bobby Clark, mai shekara 20, wanda a halin yanzu yake zaman aro a ƙungiyar Derby da ke gasar Championship, yana shirin sauya sheƙa zuwa Celtic mai riƙe da kofin Premier na Scotland a watan Janairu. (Time)
Real Madrid na shirin ƙarɓar tayi da dama kan ɗan wasan gaba Gonzalo Garcia a watan Janairu. Ɗan wasan mai shekarua 21 ya taka rawar gani a gasar Club World Cup, amma a halin yanzu ya kasa samun tagomashi a kakar wasan bana. (Marca)










