Barcelona da Real Madrid na son Guehi, Man United na zawarcin Hjulmand

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Sporting Morten Hjulmand, mai shekara 26, ya zama babban burin Manchester United, don karfafa tsakiyar tsakiyarta kuma kungiyar ta Premier tana da kwarin guiwar samun dan kasar Denmark din kan kudi kusan fam miliyan 50. (Teamtalk)
Masu Fulham sun shaida wa kociyan kungiyar, Marco Silva, bukatar su ta sabunta kwantiraginsa, wanda ya kunshi batun sakin fan miliyan 15. (The Athletic)
Barcelona da Real Madrid na sa ido sosai kan dan wasan bayan Ingila Marc Guehi, mai shekara 25, wanda ba zai tsawaita kwantiraginsa da Crystal Palace ba bayan karshen kakar wasa ta bana. (Fichajes)
Dan wasan Porto dan kasar Sipaniya, Samu Omorodion, mai shekara 21, yana cikin jerin wadanda Tottenham ke zawarcinsu. (TBR Football)
Arsenal na ci gaba da kokarin sabunta kwantiragin dan wasan baya na Netherlands Jurrien Timber, mai shekaru 24. (GiveMeSport)
Dan wasan baya na Everton dan kasar Ukraine Vitalii Mykolenko, mai shekara 26, yana jan hankalin kungiyoyi a Spain da Italiya. (Footmercato)
Kungiyoyin Premier Chelsea, da Aston Villa, da Brighton da Brentford sun tura wakilai, inda suka kalli dan wasan Strasbourg Guela Doue, mai shekara 23, duk da cewa kulub din na Faransa zai bukaci fam miliyan 26 kan dan wasan bayan na Ivory Coast. (Cought Offiside)
Leeds na sha'awar sayen dan wasan tsakiyar Maccabi Tel Aviv dan kasar Mali Issouf Sissokho, mai shekara 23, a watan Janairu. (Africafoot)
Aston Villa na sa ido sosai kan dan wasan Real Sociedad da Japan Takefusa Kubo, mai shekara 24, wanda ya yanke shawarar barin La Liga a watan Janairu. (Fichajes)










