Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wa zai lashe kofin La Liga na bana na 2022/23?
Ranar Juma'a 12 ga watan Agustan 2022 za a fara wasan La Liga kakar 2022/23 karo na 92 tun bayan da aka sauya fasalin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Za a fara ne da karawa tsakanin Osasuna da Sevilla, wadanda a bara a gidan Osasuna suka tashi 0-0, Sevilla ta ci 2-0 a gidanta.
Real Madrid ce ta lashe kofin kakar da ta wuce, kuma na 35 jumulla ba wadda ta kaita daukar kofin babbar gasar tamaula ta Sifaniya a tarihi.
Real Madrid za ta fara wasa ranar Lahadi, inda za ta ziyarci Almeria, wadda ta dawo buga La Liga a kakar nan.
Jadawalin wasannin makon farko a La Liga 2022/23
Ranar Juma’a 12 ga watan Agusta
Osasuna da Sevilla
Ranar Asabar 13 ga watan Agusta
Celta Vigo da Espanyol
Real Valladolid da Villarreal
Barcelona da Rayo Vallecano
Ranar Lahadi 14 ga watan Agusta
Cadiz da Real Sociedad
Valencia da Girona
UD Almeria da Real Madrid
Ranar Litinin 15 ga watan Agusta
Athletic de Bilbao da Real Mallorca
Getafe da Atletico de Madrid
Real Betis da Elche
Kungiyoyi 20 ne ke buga gasar La Liga
Kungiyoyi 20 ne ke buga gasar La Liga, har da 17 da suka kai bantensu a bara da sabbi guda uku da suka haura yin wasannin bana.
Ukun da suka samu gurbi a bana sun hada da biyu daga karamar gasar Sifaniya mai daraja ra biyu kai tsaye da ake kira Segunda Division da biyun da suka buga fafatar cike gurbi a kakar da aka kammala.
Kungiyoyin da suka samu gurbin buga La Liga daga Segunda Division
Kungiyar Almeria ce ta yi ta daya a gasa mai daraja ta biyu a bara, sannan Real Valladolid ta yi ta biyu, hakan ya sa kai tsaye suka samu tikitin buga La Ligar bana.
Almeria ta koma za ta fafata a La Liga, bayan kaka bakwai rabonta da wasannin, ita kuwa Valladolid kaka daya ce tsakaninta da buga La Liga.
Kungiya ta uku da ta samu gurbin buga La Liga a bana ita ce Girona, bayan da ta yi nasara a kan Tenerife 3-1 a wasan cike gurbi, kuma kaka uku ne rabonta da La Liga.
Kungiyoyin da suka bar La Liga a 2021/22
Levante ce ta fara barin La Liga a bara, bayan rashin nasara a hannun Real madrid da ci 6–0 ranar 12 ga watan Mayun 2022, hakan ya kawo karshen kaka biyar a gasar,
Alaves ce ta biyu, wadda ta bar La Liga a kakar da ta wuce, bayan da Levante ta doke ta 3-1 ranar 15 ga watan Mayun 2022, sannan ta yi ban kwana da wasannin bayan shekara shida ana fafatawa da ita.
Kungiya ta uku da ta bar La Liga a bara ita ce Granada, wadda ta yi candaras da Espanyol, ta ci karo da koma baya ne, bayan da Cadiz da kuma Mallorca suka ci wasanninsu ranar 22 ga watan Mayun 2022 ranar wasannin karshe kenan,
Kaka uku kacal Granada ta yi a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Za a yi hutu saboda gasar cin kofin duniya a La Ligar bana
Da yake za a fara gasar cin kofin duniya a Qatar tsakanin 21 ga watan Nuwamba zuwa cikin Disamba, za a yi hutu a gasar domin 'yan wasa su wakilci kasashensu.
Za kuma a yi hutu a gasar La Liga ta bana bayan an kammala wasannin makon jarshe ranar 8-9 a cikin watan Disambar 2022, za kuma a koma fafatawa ranar 31 ga watan Disamba.
Wannan shi ne karon farko da karkare La Liga a cikin watan Yuni, tun bayan kakar 2012–13.
Sabbin koci da aka samu a La Liga a bana
Espanyol ta dauki Diego Martinez ranar 31 ga watan Mayun 2022, bayan da Luis Blanco ke aikin rikon kwarya.
Valencia ta dauki Gennaro Gattuso ranar 9 ga watan Yuni, bayan da ta kori Jose Bordalas.
Athletic Bilbao ta dauki Ernesto Valverde ranar 30 ga watan Yuni, domin maye gurbin Marcelino, wanda ya ajiye aikin ranar 24 ga watan Mayun 2022.