Kofi biyar ko shida Real Madrid ke harin dauka a kakar 2022/23

Ranar Laraba Real Madrida za ta fafata da Eintracht Frankfurt a UEFA Super Cup na bana da za su kara a Helsinki a Finland.

Shi ne kofin farko da Real Madrid ke fatan dauka a bana daga biyar ko shidan da take son lashewa a kakar nan ta 2022/23.

Ana buga UEFA Super Cup tsakanin wadda ta dauki Champions League a bara da wadda ta lashe Europa League.

Daga nan Real Madrid za ta fara kakar bana ta La Liga a wasan farko da za ta ziyarci Almeria ranar Lahadi.

Real Madrid ce ta lashe La Liga a kakar da ta wuce, kuma na 35 jumulla, saboda haka ita take rike da kofin kenan.

Kofi na gaba da Real Madrid za ta yi hari a kakar nan shi ne na Champions League da za a fara wasannin farko na cikin rukuni daga 6 zuwa 7 ga watan Satumbar 2022.

Real Madrid ce ta dauki kofin zakarun Turai a kakar da ta kare kuma na 14 jumulla, bayan da ta yi nasara a kan Liverpool a Faransa.

Spanish Super Cup yana daga cikin wanda Real ke fatan dauka a kakar nan, wanda ake buga wa a Saudi Arabia, Real ce mai rike da kofin na 12 jumulla.

Ana buga gasar tsakanin biyun farko a La Liga da wadanda suka buga wasan karshe a Copa del Rey a kakar da ta wuce.

Kenan a cikin watan Janairu za a kece raini a Spanish Super Cup tsakanin kungiyoyi hudu, wato Real Madrid da Real Betis da Barcelona da kuma Valencia.

Daga nan za a buga kofin zakarun nahiyoyin duniya wato World Cup Cup, kofin da ake karawa tsakanin zakarun nahiyoyi da suka zama zakaru a kakar da ta gabata.

Haka kuma Real Madrid na sa ran daukar Copa del Rey a bana.

A kakar da ta wuce Karim Benzema ne ya lashe takalmin zinare a matakin wanda ke kan gaba a cin kwallaye a La Liga a kuma Champions League a bara.

Shin kofi nawa kuke ganin Real Madrid za ta dauka a bana?

Ko kwallaye nawa Benzema zai zura a raga a kakar 2022/23.