Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko kwalliya za ta biya wa Barcelona kuɗin sabulu a cacar kashe kuɗin da ta jefa kanta duk da ɗumbin bashi?
A watan da ya gabata mataimakin shugaban fannin tattalin arzikin Barcelona Eduard Romeu ya ce yana bukatar Yuro miliyan 500 don "ceto kungiyar".
Yanzu, makwanni shida bayan haka, kungiyar na ta wadaƙa da kuɗi wajen sayan ƴan wasa.
Kimanin fan miliyan 100 ƙungiyar ta kashe wajen sayo dan wasan Leeds Raphinha da na Bayern Munich Robert Lewandowski, haka kuma tana zawarcin dan wasan Sevilla Jules Kounde da na Manchester City Bernardo Silva.
Kocin Bayern Julian Nagelsmann wanda ya fusata ya koka da cewa Barca ita ce kungiya daya tilo da ba ta da kudi amma za ta iya siyan kowane dan wasa, kamar yadda suma wasu manyan masana harkar wasanni suka kasa fahimtar yadda kulob din da ake bin bashin fam biliyan guda zai rika kashe haka. da yawa.
To sai dai wannan hasashe da ɗan kuskure a cikinsa.
A nan, mun binciki kakar kashe kudi ta Barca, kuma za mu yi bayani daki daki kan irin cacar da kulob din da ya tsinci kansa a Las Vegas a shirye-shiryen tunkarar Real Madrid ranar Asabar ɗin nan ya tsinci kansa a ciki.
A ranar 16 ga watan Yuni, mambobin Barca wadanda suka mallaki kulob din suka kaɗa kuri'ar amincewa da kyale shugaban kungiyar Joan Laporta ya aiwatar da wasu matakai na musamman na tattalin arziki, don tara makudan kudade.
Mataki na farko shi ne na sayar da kashi 10 cikin 100 na haƙƙin gidan talabijin na cikin gida a cikin shekaru 25 masu ga asusun saka hannun jari na Amurka da ake kira Sixth Street da ya biya kusan fam miliyan 200.
Kuma a ranar Juma'a kulob din ya sanar da cewa ya sake sayar da karin kashi 15 cikin 100 na hakkokin ga shi wannan kamfani, wanda ya ba ta £300m.
Akwai kuma shirye-shiryen sayar da kashi 49.9% na ayyukan cinikin kungiyar nan gaba kadan.
Wadannan matakai, za su samar wa kungiyar sama da £600m. Don haka, eh, Barça yanzu suna da kuɗi albarkacin matakan da suka dauka.
Bayan matsalolin da tsohon shugaban kasar Josep Maria Bartomeu ya bari, watakila hanyar da ta dace don sake gina Barca ita ce tafiyar da al'amura sannu sannu da kuma rage kashe kudi da dogara da yan wasa matasa.
Amma Laporta bashi da lokaci ko hakurin jiran lokaci.
Ba ya son a tuna da shi a matsayin "mutumin da ya taimaka wajen farfado da Barça ta hanyar kafa ginshiƙai don samun nasara a nan gaba".
A maimakon haka ya fi son a tuna da shi a matsayin wanda jarumin da ya farfado da martabar kungiyar nan take.
Bayan cin kofin Spaniya uku kacal a shekaru uku, ya kasa hakuri don samun nasara. Yana son ya lashe manyan kofuna, kuma yana son ya lashe su a yanzu. Don haka Laporta ya gabatar da wadannan sauye sauye don cimma wannan burin.
Amma ba za a iya raina girman cacar da ya sanya kansa ta kashe kudi duk da kalubalen da kungiyar ke ciki ba, don bamu sani ba ko Raphinha zai yunkuro ya taka rawar da ake tunanin zai taka, ko Lewandowski mai shekaru 34 zai taka rawa duk da shekaru ko Ousmane Dembele zai iya yin wani tasiri duk da yawan samun rauni. ko taurarin matasa irin su Pedri, da Gavi da Ansu Fati za su iya ci gaba da nuna kansu, sannan ko shima koci Xavi zai iya daidaita lamuran kungiyar.
Lokaci ne kawai zai nuna, kuma cacar ta fi girma saboda yarjejeniya ce ta lokaci ɗaya kawai.
Ko makawa babu sayar da kadarorin kungiya tare da zabga makudan kudin a bukatar gajeren lokaci dabara ce da ba za a iya maimaita ta ba.
Ba tare da kaucewa siddabarun da Laporta ke son yi ba, a fili take cewa kuma akwai bukatar Barca ta zama mafi inganci a kasuwar musayar 'yan wasa fiye da yadda muka shaida a 'yan shekarun nan. Alal misali shine sayan yan wasan da ba a bukata irin su Memphis Depay, da Martin Braithwaite, da Miralem Pjanic da Samuel Umtiti idan aka yi la'akari da yawan albashinsu, da kuma kwantirai mai tsayi da ake ba su.