Mece ce gaskiyar dala miliyan 200 da Amurka ta bai wa Najeriya domin Kiristoci?
Asalin hoton, BBC COLLAGE
Sa-insa da faɗi-in-fada sun kaure a Najeriya tun bayan da rahotanni suka ɓulla cewa Amurka ta bai wa Najeriya kyautar dala miliyar 200 domin a gina wa Kiristoci asibitoci da cibiyoyin lafiya a Najeriya.
Wannan batu dai ya yi matuƙar tayar da ƙura musamman a tsakanin Musulmi da ke ganin Amurkar na da wani shiri.
Hakan dai na zuwa ne watanni uku bayan da shugaban Amurka ya ayyana Najeriya a cikin jerin ƙasashe " da ake da damuwa a kansu" sakamakon zargin yi wa "Kiristoci kisan gilla" da ya yi.
Ƙungiyar da ke fafutukar ƴancin al'ummar Musulmi a Najeriya, MURIC ta fito ta yi alawadai da batun ware Kiristoci domin a tallafi sha'anin lafiyarsu wanda ta ce hakan zai kara wagegiyar ɓarakar da ke tsakanin Musulmi da Kirista a Najeriya.
Yanzu tambayoyin da al'ummar Najeriya ke neman amsarsu su ne:
Shin Amurka ta bai wa Najeriya kuɗi? Nawa ne kuɗin? Sannan ko an ware wasu kuɗi na musamman ga harkar lafiyar mabiya addinin Kirista?
Ko Amurka ta bai wa Najeriya tallafi?
Asalin hoton, BBC GRAB
Ministan Lafiyar Najeriya, Farfesa Mohammed Ali Pate ya amince da cimma yarjejeniyar samun tallafin ƙasar Amurka wanda ya ce ba yau aka fara ba.
" An kusa shekara 20 tun daga 2003 zuwa yau, Amurka na bayar da tallafi a ƙasashe daban-daban na duniya ciki har da Najeriya. Kuma a baya wannan tallafi na zuwa ne ta hanyar ƙungiyoyi daban-daban."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"A cikin shekara 2025, a watan Jabairu sai gwamnatin Amurka ta sauya tsarinta ta ce ta daina bayar da tallafi ga kasashe...cikin ikon Allah a Satumba sai suka sake dawowa suka ce suna son su ci gaba da ba mu tallafi na shekara biyar wato zuwa 2030," in Farfesa Pate.
Farfesa Pate ya shaida wa BBC cewa yarjejeniyar kiwon lafiya ce tsakanin ƙasashen guda biyu, inda suka amince su zuba dalar Amurka biliyan biyar da miliyan 100.
Yayin da Amurkar za ta zuba dala biliyan biyu, Najeriya kuma a nata ɓangaren za ta zuba dala biliyan uku da miliyan 100 wanda hakan zai kasance ta hanyar kasafin kuɗin ƙasar a fannin kiwon lafiya a tsawon shekaru biyar wato daga 2025 zuwa 2030.
Ministan ya lissafa hanyoyin da Amurkar za ta bi wajen bai wa Najeriya waɗannan kudaɗe.
"Dala biliyan biyu nasu ne za su saka inda za su sayi magunguna kamar na HIV ko na TB ko na Maleriya. Sannan wasu daga cikin kuɗin za su bayar ne ta hanyar ɗaukar ma'aikatan lafiya da safara da kaikomon magunguna da kuma kulawa da abubuwa da tallafa wa marasa ƙarfi a fannin lafiya a mataki na farko," in ji Pate.
Me za a yi da tallafin?
Ministan na lafiya na Najeriya, Farfesa Pate ya ce za a tafiyar da wannan tallafin haɗin gwiwa ne a kan wani tsari da gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi suka rattaɓa hannu a kai tun shekarar 2023 da ke son inganta kiwon lafiya a ƙasar da ake kira da "Health Sector Renewal Initiative.
" Wannan zai inganta shirin lafiya a matakin farko da haɓaka tsarin insorar lafiya da horas da ma'aikatan lafiya da kuma daƙile cutuka masu yaɗuwa da kula da masu cutukan HIV da tarin TB da kuma zazzaɓin cizon sauro da ceton rai mata masu juna biyu."
Wane ne zai amfana da tallafin?
Farfesa Pate ya ce "dangane da wuraren (garuruwa da al'ummar) da za a sa wannan tallafi na Amurka to bayanan za su fito kwana 90 daga lokacin da aka sanya hannu a kan wannan yarjejeniyar."
To sai dai ministan ya ce " mu a gwamnatin Najeriya burinmu shi ne duk faɗin Najeriya, duk ɗan Najeriya...ya zama sun amfana da wannan (tallafi) yadda babu wani ɓangare ko wani wuri da za a hana su. Misali idan maganin maleriya aka samu ya zama kowane ɗan Najeriya ya amfana."
Dangane da lokacin da za a fara aiwatar da shirin, Farfesa Pate ya ce ana sa ran ranar 1 ga watan Afrilun 2026 ne tallafin na Amurka zai fara zuwa hannun Najeriya, inda su kuma za su yi taro na masu ruwa da tsaki a watan Maris.
Gaske ne an ware $200,000 ga asibitocin Kirista?
Mohammed Ali Pate ya ce su dai a Najeriya, a iya saninsu babu wannan batu a lokacin da suka rattaɓa hannu a wannan yarjejeniya a ƙarshen makon da ya gabata.
"Mu dai a cikin yarjejeniyar da muka sakawa hannu babu wannan maganar cewa wani addini zai amfana da tallafin.
Abin da ke ciki shi ne kashi 10 cikin 100 na kuɗin da Amurka za ta saka za a kashe shi ne ga ƙungiyoyin lafiya da ke kiran haɗin kai tsakanin addinai da ake kira "Inter-Faith Groups" kuma wadanda sun haɗa da daga dukkan addinai ba tare da banbanci ba. Kuma harkar rashin lafiya ai Musulmi na yi sannan Kirista ma na yi."
Daga ina batun fifita Kirista ya fito?
Asalin hoton, US Home Department
Ministan ya ce shi dai ba shi da masaniyar daga ina wannan batu ya taso ba amma dai abin da ya sani shi ne a yarjejeniyar da suka cimma babu wannan zancen.
To sai dai bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa ma'aikatar cikin gida ta Amurka ce ta fitar da sanarwar da ke kaikomo a tsakanin Amurkawa, inda sanarwar ta nuna tallafin na Amurka zai tafi ga harkar lafiya ta mabiya addinin Kirista a Najeriya.
" Dala miliyan 200 domin tallafa wa cibiyoyin lafiya fiye da 900 na Kiristoci."
Ana dai ganin cewa sanarwar ba za ta rasa nasaba da burin shugaban Amurka, Donald Trump na ganin ya daɗaɗa wa magoya bayansa da ke bin addnin Kirista a cikin gida waɗanda ake ganin ya rasa goyon bayansu a baya-bayan nan.
Bugu da ƙari, wasu na tunanin cewa ma'aikatar cikin gidan ta yi hakan ne domin ka da barazana da kumfar bakin da Amurkar ta yi kan zargin da ta yi wa Najeriya na yi wa Kiristoci kisan kiyashi.
"Idan aka wayi gari Amurka ta bai wa Najeriya tallafi watanni uku bayan zarge-zargen da ba a iya ɗaukar matakin da ya gamsar da masu kururuta batun ba," in ji wani mai sharhi da ba ya son a ambaci sunansa.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai