Yadda masu bayar da gudumawar maniyyi ke haihuwar ɗaruruwan yara barkatai

Asalin hoton, Getty
- Marubuci, James Gallagher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health and science correspondent
- Marubuci, Catherine Snowdon
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health reporter
- Lokacin karatu: Minti 6
Wasu mazan suna da ƴaƴa da yawa ta hanyar bayar da gudunmuwar maniyya da suke yi. A wannan makon BBC ta kawo rahoton wani mutum da aka gano maniyyinsa na ɗauke da wasu ƙwayoyin halitta da za su iya ƙara barazanar kamuwa da ciwon daji ko kansa a tsakanin ƴaƴan da ya haifa.
Wani abin damuwa game da binciken da aka yi kan mutumin dai shi ne an tura maniyyin mutumin zuwa ƙasashe 14 kuma an haifi ƴaƴa 197 da shi. Wannan na cikin manyan abubuwan da aka bankaɗo game da abin da ke faruwa saboda bayar da gudunmuwar maniyyi ga masu buƙatar haihuwa.
Bayar da gudunmuwar maniyyi wata hanya ce ta bai wa mata damar haihuwa, musamman a tsakanin waɗanda suka yanke ƙaunar haihuwar, ko masu fatan haihuwa ba tare da sun yi aure ba, ko masu auren jinsi, ko kuma waɗanda ke da burin samun ƴaƴa ba tare da sun yi wata mu'amular aure da namiji ba.
Yawan masu neman a basu gudunmuwar maniyyi domin haihuwa na ƙara yawaita a Turai inda ake hasashen nan da 2033 zai zamo kasuwa mai jarin fan biliyan biyu, kuma an gano Denmark ce ƙasar da ta fi kowacce yawan masu bayar da maniyyi a duniya.
Me ya sa wasu masu bayar da gudunmuwar maniyyi suka tara ƴaƴa da yawa, me ya sa maniyyin Denmark da ake yi wa laƙabi da ''Viking sperm" ya samu karɓuwa sosai a kasuwar bayar da maniyyi ta duniya?
Mafi yawan maza ba su da maniyyi mai kyau
Idan kai namiji ne, muna baka haƙuri domin akwai yiwuwar maniyyin ka ba shi da kyau sosai yadda har za ka iya bayar da gudunmuwa ga masu neman haihuwa. Daga cikin maza 100 da ke zuwa domin bayar da maniyyi, ƙasa da biyar ne kacal ke da maniyyi mai kyau.
Da farko dai ana buƙatar ka samar da maniyyi mai yawa ta yadda za a iya yin gwajin da ya kamata a kai, wannan kuma na nufin ya kamata maniyyin ka ya zamo mai ƙarfi sosai yadda zai yi gudu yadda ake so.
Ana kuma gwaji domin tabbatar da cewa maniiyin ka zai jure ajiyar da za a yi masa ba tare da ya lalace ba.
Kana iya samun haihuwa har shida amma kuma ka gaza cika sharuɗɗan bayar da gudunmuwar maniyyi domin haihuwa.

Asalin hoton, Getty Images
Kowacce ƙasa tana da dokokinta a kan bayar da gudunmuwar maniyyi, amma a Birtaniya dole mai bayar wa ya zamo tsakanin shekara 18 zuwa 45 kuma wanda baya ɗauke da cutar HIV da ciwon sanyi ko kuma duk wata cuta da za a iya gadon ta, kamar ciwon sikila.
Wannan ne ya sa aƙalla rabin maniyyin da ake rabawa masu neman haihuwa a Birtaniya ana shigo da shi ne daga ƙasashen waje.
Amma ilimin halittar ɗan Adam ya tabbatar da cewa kowanne miniyyi ɗaya zai iya samar da ciki, don haka a lokaci ɗaya namiji zai iya samar da miliyoyin ƙwayar maniyyi.
Maza na zuwa asibiti sau ɗaya ko sau biyu a kowanne mako idan suna son bayar da maniyyin su, wanda kuma zai iya ɗaukar tsawon wata ɗaya ana yi.
Sarah Norcross, daraktar wata ƙungiya mai gangamin wayar da kai game da bayar da gudunmuwar maniyyi ta ce ƙarancin masu bayar da maniyyi ya janyo ana yawan amsa daga mutanen da aka tantancen ingancin nasu maniyyin.
Akwai maniyyin da aka fi buƙata

Asalin hoton, Allan Pacey
Daga cikin ɗimbin mazan da suka gabatar da kansu domin bayar da gudunmuwar maniyyi ga masu buƙata, kaɗan ne ke cika ƙa'ida, don haka ana iya kamata yanayin da irin yadda ke faruwa a manhajar haɗa aure ta yanar gizo... da yawa sun nema, amma kaɗan ke samu.
Masu neman mai bayar da maniyyi suna da zaɓin sauraron muryar mai maniyyin da suke so, su kuma tantance ko wane aiki yake yi - Injiniya ne ko lebura? har ma suna iya neman a nuna masu hoto domin gano yadda yake a zahiri, ko mai ƙiba ne ko siriri.
"Idan mai bayar da maniyyi kyakkyawa ne, dogo mai kyaun jiki, mai jin harsuna bakwai kuma ɗan ƙwalisa, to ya fi wanda baya da irin wannan kamanni karɓuwa,'' in ji Farfesa Allan Pacey, wani ƙwararre mai cibiyar ajiye maniyyi a Sheffield.
Yadda maniyyin 'Viking' na Denmark ya karaɗe duniya

Asalin hoton, Getty Images
Denmark ta yi ƙaurin suna kan samar da cibiyoyin ajiye maniyyi kuma ta shahara wajen samar da maniyyi mai inganci sosai.
Ole Schou, mai shekara 71 kuma shugaban cibiyar ajiye maniyyi ta Cryos International inda ake sayar da maniyyi ɗaya da ya kai 0.5ml a kan €100 (£88) ya ce yadda aka ɗauki harkar bayar da maniyyi a Denmark ya banbanta da yadda abin yake a sassan duniya.
"A nan ba a kallon lamarin a matsayin wani abin ƙyama ko tsangwama. Mafi yawan masu bayar da maniyyi suna kuma bayar da jini ga mabuƙata.'' in ji Ole Schou.

Asalin hoton, Cryos International
Yadda ake rabon maniyyi
Wani abu da bincike ya bankaɗo shi ne yadda maniyyin da aka ajiye a Denmark ke karaɗe duniya, inda aka tura shi zuwa cibiyoyin haɗa maniyyi 67 a ƙasashe 14.
Ƙasashe na da dokokinsu, inda a lokuta da dama sau ɗaya kacal ake bari mutum ya bayar da maniyyin sa.
Wasu lokuta kuma ana la'akari ne da yawan ƴaƴan da aka haifa da maniyyin mutum, wanda zai sa a daina yarda ya ƙara bayar wa.
Amma babu dokar da ta hana a samu mutum ɗaya da ya bayar da maniyyinsa domin haihuwar ƴaƴa a ƙasashe da yawa in dai ba a karya dokar ƙasashen ba.
Wannan ya sa ake samun masu bayar da maniyyi da aka haifar wa ƴaƴa masu yawa a ƙasashe da yawa. Duk da cewa mutum ba ya iya gane yawan ƴaƴan da aka haifa da maniyyin nasa.
"Maza da yawa sun bayar da maniyyin su amma ba su san cewa daga wannan bayarwar ɗaya da suka yi, ana iya haihuwar ƴaƴa da yawa a ƙasashe da yawa ba,'' in ji Sarah Norcross.

Asalin hoton, Getty
Bayan bincike ya gano yadda wani mai bayar da maniyyi da ƴaƴansa 197 ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar kansa saboda ƙwayar halittarsa da suke ɗauke da ita a jiki, hukumomi a Belgium sun nemi ƙasashen Turai su kafa cibiyar nazari kan yadda ake bayar da maniyyi don neman haihuwa a Turrai.
Hukumomi a Turai ma sun buƙaci a ƙayyade yawan haihuwar da maniyyin namiji ɗaya za yi, inda suka nemi a dakatar da mutum da zarar an haifi yara 50 da maniyyin sa.

Asalin hoton, Getty
Ana bayyana damuwa kan yaran da ake haihuwa ta hanyar haɗa maniyyin wani . Wasu a cikinsu ba za su ji daɗin hanyar da aka samar da su ba, yayin da wasu ba za su damu ba.
Haka nan shi wanda ya bayar da maniyyin ba zai san wajen da za a haifi ƴaƴansa ba.
Amma Mr Schou na Cryos ya bayyana fargabar cewa ɗaukar matakin rage yawa ƴaƴan da za a haifa da maniyyin mutum ɗaya zai iya sa mutane su fara bayar da maniyyin nasu ta bayan fage.











