Jaruman Kannywood da suka rasu a 2025

Kamar yadda masana'antar Kannywood ke ta ƙoƙarin rarrafawa ta sake tashi domin koma yadda take a baya, inda a bana ta fitar da ƙayatattun fina-finai, a wani ɓangaren kuma, masana'antar ta yi rashe-rashe da dama a baa.
Dama masu iya magana na cewa ana bikin duniya ake na ƙiyama, kuma hakan aka yi a masana'antar domin wasu jaruman suna cikin taka rawa a wasu fina-finai ne suka rasuwa, sai dai a maye gurbinsu da wasu jaruman.
Masana'antar ta rasa wasu jarumai fitattu da suka daɗe suna taka rawa a masana'antar, ciki har da waɗanda suka yanke wa masana'antar cibiya tun a farkon da aka ƙirƙire ta, sannan akwai wasu ƙananan jaruman da suka rasu ba tare da sun yi fice ba.
Wannan ya sa kamar yadda muka rairayo wasu nasarori da ma jaruman da haska, sai muka waiwayi jaruman da suka rasu a masana'antar a wannan shekarar.
Baba Karkuzu

Asalin hoton, Ali Nuhu Mohammed
Abdullahi Shuaibu, wanda aka fi sani Karkuzu fitaccen jarumi ne na fina-finan da Hausa da ya daɗe yana nishaɗantar da al'umma.
Ya fara yin fice ne a fim ɗin da ya fito mai suna "Karkuzu na Bodara," wanda aka yi a tsakankanin 1980.
Suna cikin jaruman da suka fara assasa fina-finan Hausa a arewacin Najeriya kafin matasan jaruman suka taso.
Ya rasu ne a ranar 25 ga watan Maris na wannan shekarar ta 2025 yana da shekara 94.
Ya rasu ne a birnin Jos na jihar Filato bayan fama da jinya na tsawon lokaci, inda har makancewa ya yi.
Malam Nata'ala
A ranar Lahadi 2 ga watan Nuwamba ne Allah ya yi wa Mato Yakubu, wanda aka fi sani da Malam Nata'ala Mai Sittin Goma ya rasu.
An haife shi ne a Rijiyar Damuwa da ke ƙaramar hukumar Potiskum ta Jihar yobe, ya fara karatun Allo a Yola ta Jihar Adamawa a 1979.
Ya rasu ya bar mata 3 da yara da dama, sannan ya rasu ne bayan dogon jinya da ya sha.
An yi jana'izarsa a ranar Litinin 3 ga watan Nuwamba a jihar Yobe.
Umar Maikuɗi

Asalin hoton, rikadawa1/Instagram
A watan Mayun wannan shekarar ta 2025 ne jarumi Umar Maikudi (Cashman) ya rasu a Zaria da ke jihar Kaduna.
Marigayin ya fito a shirin 'Labarina' mai dogon zango, sannan ya kasance shugaban ƙungiyar masu shirya shirya-shirya ta Najeriya MOPPAN.
Ya rasu ya bar mata da yara.
Baba Hasin

Asalin hoton, Iyalai
A ranar Asabar 27 ga watan Afrilun wannan shekarar ne kuma fitaccen jarumin fina-finan Kannywood Muhammad Shuaibu wanda aka fi sani da Baba Hasin da ke fitowa a matsayin dattijo ya rasu.
Jarumin ya rasu ne yana da shekara 68 a duniya bayan shafe tsawon lokaci yana jinya a Asibitin Malam Aminu Kano da ke jihar Kano.
Ya rasu ya bar mata biyu da ƴaƴa 17.










