Cutuka 10 mafiya haɗari ga ɗan'adam da hanyoyin kauce musu

Cutuka

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 6

Akwai nau'ikan cutukan da ke kama mutane a lokuta daban-daban bisa wasu dalilai na rashin lafiya.

Wasu cutukan ana warkewa, yayin da wasu kuma suke zama ajalin wanda ya kamu da su.

Waɗansu cutukan ana warkewa idan aka sha magani, akwai kuma waɗanda sai mutuwa ce kawai ke raba mutum da su.

Akwai nau'in cutuka mafiya hatsari da ke kawo saurin salwantar rai idan aka kamu da su.

Kan haka ne muka tattauna da likitoci domin jin cutuka mafiya haɗari ga rayuwar ɗa'adam da kuma hanyoyin da ya kamata a bi domin kauce wa kamuwa da su, da ma yadda za a bi da su idan tsautsayi ya sa an kamu da su.

Cutar Ebola

...

Asalin hoton, Getty Images

Dakta Salihu Ibrahim Kwaifa, ƙwararren likita da ke zaune a Abuja, ya ce cutar Ebola na haddasa mutuwar wanda ya kamu da ita da kashi fiye da 90 cikin 100.

Daga nan sai amai ya biyo baya da atini kuma jini zai riƙa zuba daga ciki da wajen jikin wanda ya kamu da cutar.

Dakta Hassan Biba na Asibitin Biba da ke jihar Kaduna ya ce Irin waɗannan cutaka galibi sukan haifar da zubar jini daga jikin wanda ya kamu da su, don hake ne suka da haɗarin gaske.

Cutar cizon karnuka (Rabbies)

Karnuka

Asalin hoton, Getty Images

Ciwon haukar karnuka ya zama wata barazana a duniya, inda cutar ke kashe kusan mutum 60,000 a kowace shekara, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO.

WHO na alaƙanta kashi 99 cikin 100 na matsalar da cizon karnuka da kuma raunukan da aka samu sakamakon cizon.

Ƙwararren likitan ya ce kawo yanzu cutar ba ta da magani, kuma tana da saurin kisa.

Amai da gudawa

...

Asalin hoton, Getty Images

Dakta Kwaifa ya ce cutar amai da gudawa na ɗaya daga cikin cutuka mafiya kisa da zarar sun kama mutum.

''Matsawar ba a samu kulawar gaggawa ba, idan kwalara ta kama mutum to za ta iya zama ajalinsa'', in ji shi.

A nasa ɓangare Dakta Hassan ya ce cutar amai da gudawa na daga cikin cutukan da ke haddasa mutuwar farat ɗaya ga wanda ya kamu da ita.

Cutar kansa

Cutar kansa na cikin jerin cutuka mafiya hatsari ga mutane, idan an kamu da su.

Akwai nau'ikan cutar kansa, da dama da ke kama mutane, kuma mafi yawan nau'ikan cutar ba su da magani, kodayake akwai ƙalilan masu magani, a cewar Dakta Kwaifa.

Dakta Hassan ya ce galibi waɗanda suka kamu da cutar kansa kan mutu saboda rashin sanin yadda za su tafikar da cutar, ga kuma wahala da tsardar maganin cutar.

Cutar bugun zuciya

Wani mutum riƙe da ƙirjinsa

Asalin hoton, Getty Images

Ƙwararren likitan ya ce, akwai abubuwan da ke janyo cutar kamar idan zuciya tana buga jini ya tafi da ƙarfi, wato kama hawan jini ke nan.

HIV/AIDs

HIV ko AIDs cuta ce da ke karya garkuwa jiki. Cuta ce da kawo yanzu ba ta da magani, sai dai na rage kaifinta, a cewar Dakta Kwaifa.

Mutanen da suka kamu da HIV/AIDs garkuwar jikinsu kan yi rauni ta yadda kowace irin cuta za ta samu sauƙin shiga jikinsu.

Cutar asma

wata mai cutar asma riƙa da maganin shaƙa

Asalin hoton, Getty Images

Kodayake akwai magunguna masu inganci da ke rage kaifin tarin fuka, amma Dakta Kwaifa ya ce akwai yanayin da idan cutar da tashi kuma ba a samu kulawa ba, tana iya haifar da rasa rai.

Cuta ce ta sarƙewar numfashi haɗe da tari da ke shafar yadda iska ke shiga da fita daga huhu.

Ciwon suga

Ciwon suga cuta ce mai tsanani wadda ke kashe mutane sama da miliyan a kowace shekara, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.

Cutar na faruwa ne lokacin da jiki ya kasa sarrafa dukkanin suga (glucose) da ke cikin jini.

Kuma cutar ta kasance babbar matsala mai girma, wani rahoton WHO a 2023 ya ce kimanin mutum miliyan 422 ke fama da ciwon suga a duniya.

Ciwon ƙoda

Ƙoda

Asalin hoton, Getty Images

Ciwon ƙoda, ciwo ne da ke barazana ga lafiyar al'umma a duniya, saboda girma da kuma tsananinsa.

Alƙaluman WHO sun nuna cewa cikin mutum guda cikin 10 a duniya na iya zama da ciwon ƙoda wanda ya nuna girman barazanar ciwon a duniya.

Dakta Kwaifa ya ce idan cutar ƙoda ta yi tsanani, tana kai matakin da dole sai an yi wa mutum dashen wata ƙodar.

Ciwon hanta

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce a duk minti ɗaya mutum biyu na mutuwa sanadin ciwon hanta duk da cewa ana samun riga-kafin ciwon hanta nau'in Ba, wanda shi ne ya fi kisa a duk nau'o'in cutar.

Dakta Hassan ya ce kodayake ana iya warkewa daga cutar hanta nau'in C, amma ba a iya warkewa daga nau'in B.

Matakan kauce wa kamuwa da cutuka masu hatsari

allura
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Samar da cibiyoyin bincike: Dakta Hassan Biba ya ce matakin farko da ya kamata a ɗauka wajen kauce wa kamuwa da waɗannan cutuka, shi ne gwamnati ta samar da cibiyoyin gwaje-gwajen manyan cutuka a sassan ƙasar daban-daban.

''Hakan zai sa likitoci su gano cutukan da wuri a jikin mutunen da suka kamu, ta yadda za su iya yaƙi da cutukan'', in ji shi

Gangamin wayar da kai: Likitan ya ce wani mataki na kauce wa kamuwa da iri-iren waɗannan cutuka, shi ne gwamnati da ƙungiyoyi su riƙa shirya gangamin wayar da kai game da illolin waɗannan cutaka.

''Haƙiƙa hakan zai taimaka, saboda a gangamin za a riƙa faɗa wa mutane kada ku yi kaza, don idan kun yi za ku kamu da cuta kaza, sannan za su ji yadda ake ɗaukar cutukan, wanda kuma hakan zai sa su kauce wa kamuwa da su'', in ji shi.

Yawaita zuwa gwaje-gwaje - Dakta Salihu Kwaifa ya ce matakin da mutane za su iya ɗauka shi ne su riƙa zuwa asibiti lokaci zuwa lokaci domin yin gwaje-gwajen lafiya.

''Yana da kyau mutum ya riƙa zuwa asibiti aƙalla sau ɗaya a kowace shekara domin yin gwaje-gwajen lafiya, a nan ne lokitoci za su ba shi shawarwari da ya kamata'', in ji shi.

Shi ma Dakta Hassan Biba ya ce idan mutum yana zuwa asibiti ana yi masa gwaji hakan zai sa ya san wace cuta yake ɗauke da ita domin kiyaye abubuwan da ba ta so.

Sauƙaƙa hanyoyin gwaje-gwaje - Dakta Hassan Biba ya ce ya kamata gwamnati ta samar da wata gidauniya da za ta riƙa tallafa wa mutanen da suka je domin yin gwaje-gwajen manyan cutuka.

''Ire-ire waɗannan gwaje-gwaje suna da tsada, amma idan aka samar da wata gidauniya, kamar inshorar lafiya da za ta riƙa tallafawa wajen ɗaukar nauyin koda wani ɓangare na kuɗin gwajin, hakan zai sauƙaƙa gwajin', a cewarsa.

Yekuwar riga-kafi - Dakta Salihu Kwaifa ya ce cutuka masu saurin yaɗuwa da ke cikin wanann rukucni ana iya kauce musu ta hanyar yin riga-kafi.

''Kamar cutar amai da gudawa da Ebola da sauransu idan suka ɓarke, abin da ya kamata a yi shi ne gaggauta yin yekuwa tare da samar da riga-kafinsu, domin yi wa al'umma''.

Ya ƙara da cewa a hanyar yin riga kafin za a iya kauce wa kamuwa da cutuka masu yawa, saboda a cewarsa da dama cikin waɗanan cutuka irin su cutar hanta nau'in B da cutar haukar karnuka, duk na da riga-kafi.