Yadda za mu kauce wa ciwon hanta mai muguwar ɓarna
Yadda za mu kauce wa ciwon hanta mai muguwar ɓarna
Duk 28 ga watan Yulin kowacce shekara, rana irin ta yau kenan, ana tunawa da ɓarnar da ciwon hanta yake yi a duniya, ta hanyar ƙara wayar da kai.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce a duk minti 1 mutum biyu na mutuwa sanadin ciwon hanta duk da yake ana iya riga-kafin ciwon hanta nau'in Ba, wanda shi ne ya fi kisa a duk nau'o'in cutar.



