Rabin masu cutar Ebola aka san da zamansu

Asalin hoton, Reuters
Kimanin kashi 50 ikin 100 na wadanda suka kamu da cutar Ebola ne a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo aka iya ganowa inji jami'in gwamnatin kasar mai kula da yadda ake tunkarar matsalar da cutar ta haifar.
Jami'in mai suna Jean-Jacques Muyembe ya gargadi jama'ar kasar cewa barkewar cutar da ke faruwa a yanzu na iya kai wa shekara uku kafin a iya shayo kanta.
Ya kuma ce wani mutumin garin Goma da ya mutu a cikin makon nan a kusa da iyakar kasar da Rwanda na da 'ya'ya 10, kuma wasu mutanen daban sun kamu da cutar daga gareshi kafin mutuwarsa.
Annobar cutar Ebola ta kashe fiye da mutum 1,800 a shekarar da ta gabata.
Rikicin siyasa da ke ruruwa a yankin ya kara dagula kokarin magance annobar.
A farkon wannan makon, kasar Rwanda ta rufe iyakarta da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongon na wani takaitaccen lokaci saboda fargabar da ake yi cewa cutar na iya bazuwa zuwa cikin kasar.
Mene ne Ebola?

Asalin hoton, BSIP/Getty images
Ebola wata cuta ce da a farko shigarta jikin dan Adam ke sa masa zazzabi farad daya da kasala mai tsanani da ciwon gabobin jiki da kuma kaushi a makogwaro.
- Daga nan sai amai ya biyu baya da atini kuma jini zai rika zuba daga cik da wajen jikin mai kamuwa da cutar
- Mutane na kamuwa da cutar ne bayan sun taba jikin wanda ke fama da cutar ta hanyar ruwan ciwo ko jinin da ke fita daga fatar mai fama da cutar, ko ta bakinsa ko ta hancinsa; ko kuma ta taba jini ko bayan gida ko dukkan wani ruwan jikinsa.
- Yawanci masu kamuwa da cutar na mutuwa ne daga rashin isasshen ruwa a jikinsu da kuma yadda sassan jikinsu ke daina aiki
Shin akwai rigakafinsa kuwa?
Akwai rigakafin cutar Ebola. Rigakafin na iya bayar da kariya cikin kashi 99 cikin 100, kuma an bai wa kimanin mutum 161,000 rigakafin.
Amma ba kowa ne akan bai wa wannan rigakafin ba - akasari akan ba wadanda aka san sun taba wadanda ke fama da cutar ne kai tsaye, da kuma wadanda suma suka taba su. Abin damuwa shi ne wasu mutanen sun ki amincewa su karbi allurar rigakafin.

Asalin hoton, AFP
Wasu mutanen sun ce suna da dalilai da suka hana su karabar allurar rigakafin, ciki har da:
- Addinin da suke bi ya hana su karbar dukkan allurar magani
- Wasu na ganin ba sa bukatar rigakafin
- Wasu ma ba su yarda cewa akwai cutar ta Ebola ba sam-sam
Kamfanin hada magunguna na Merck ne ya samar da allurar rigakafin a yayin da cutar ta barke a yankin Afirka ta Yamma.
Amma saboda karancinsa, hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta umarci da arika amfani da wata allurar rigakafin da kamfanin Johnson & Johnson suke samarwa.










