Mene ne ciwon suga kuma ta yaya za ku iya kauce masa?

Asalin hoton, Getty Images
Ciwon suga cuta ce mai tsanani ta rayuwa wadda ke kashe mutane sama da miliyan a kowace shekara - kuma kowa na iya kamuwa da ita.
Cutar na faruwa ne lokacin da jiki ya kasa sarrafa dukkanin suga (glucose) da ke cikin jini; Matsalolinsa na iya haifar da bugun zuciya da bugun jini da makanta da cutar ƙoda da kuma abin da zai haifar da yanke wani barin jikin mutum.
Kuma cutar ta kasance babbar matsala da ke girma - kimanin mutane miliyan 422 suna fama da ciwon suga a duniya - sau hudu kenan fiye da shekaru 40 da suka wuce, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
Duk da haɗarin da ke tattare da wannan cutar, rabin mutanen da ke da ciwon suga ba su sani ba.
Amma sauya yadda mutum ke rayuwa iya hana kamuwa da cutar a lokuta da yawa ta hanyoyin kamar haka:
Me ke janyo ciwon suga?
Idan muka ci abinci, jikinmu yakan sarrafa nau'ukan abinci masu samar da kuzari zuwa sukari (glucose). Sinadarin insulin wanda tumburƙuma ke samarwa shi yake isar wa jiki saƙon cewa ya kamata ya yi amfani da wannan sukarin domin samar da kuzari a jiki.
Ciwon sukari yana faruwa ne lokacin da ba a samar da sinadarin insulin ba ko kuma ba ya aiki yadda ya kamata, wanda ke sanyawa sukari ya taru a cikin jininmu.

Asalin hoton, Getty Images
Menene nau'ikan ciwo suga?
Akwai nau'ukan ciwon suga da yawa.
A cikin nau'in ciwon suga na 1, tumburƙuma na daina samar da sinadarin insulin, don haka suga (glucose) ke taruwa a cikin jini.
Masana kimiyya ba su san ainihin dalilin da ya sa hakan ke faruwa ba amma sun yi imanin cewa kwayoyin halittan gado na iya yin tasirin kan hakan ko kuma sakamakon ƙwayar cuta da ke lalata kwayoyin halitta masu samar da sinadarin insulin a cikin tumburƙuma.
Kusan kashi 10 cikin 100 na masu ciwon suga suna da nau'in na 1.
A cikin nau'in ciwon suga na 2, tumburƙuma ba ta samar da isasshen sinadarin insulin ko kuma sinadarin jiki ba ya aiki yadda ya kamata.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan yanayin yakan shafi masu matsakaicin shekaru da tsofaffi, ciki har da matasa masu kiba da masu yawan zama, da daidaikun mutane daga wasu ƙabilu, musamman Kudancin Asiya.
Wasu mata masu juna biyu za su iya kamuwa da ciwon suga na ciki lokacin da jikinsu ba ya iya samar da isasshen sinadarin insulin gare su da jariransu.
Nazari daban-daban ta amfani da ma'auni daban-daban sun kiyasta cewa kashi 6 zuwa 16 na mata masu juna biyu na iya kamuwa da ciwon suga na ciki.
Suna buƙatar sarrafa matakan sukarinsu ta hanyar abinci da suke ci da motsa jiki, ko amfani da sinadarin insulin don hana shi haɓaka zuwa nau'in na 2.
Haka kuma, ana iya gano mutane da suke gab da kamuwa da ciwon suga- ƙarin yawan suga (glucose) a cikin jini ke nan wanda kuma ka iya haifar da ciwon suga.
Mene ne alamun ciwon suga?

Asalin hoton, Getty Images
Mafi yawan alamomin da ke nuna kamuwa da ciwon suga sun haɗa da;
Jin ƙishirwa sosai
Yin fitsari fiye da yadda aka saba, musamman da daddare
Jin gajiya sosai
Rama ba tare da wani dalili ba
Cutar sanyi maras jin magani
Rashin gani da kyau
Rashin warkewar yanka a fata
A cewar Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Biritaniya, a cikin nau'in ciwon suga na 1 alamun kamuwa da cutar suna nunawa ne a farkon yaruntar mutum ko samartaka har ya yi tsanani.
Mutanen da suka fi fuskantar hatsarin nau'in ciwon suga na 2 sun haɗa da waɗanda suka haura shekaru 40 (ko 25 ga mutanen da ke kudancin Asiya) ko kuma masu iyaye ko ƴan'uwa da ke da cutar, ko masu ƙiba, ko kuma sun fito ne daga Asiya ta Kudu da ƴan China, da ƴan yankin Caribbean ko kuma asalin bakar fata na Afirka.
Zan iya kauce wa ciwon suga?
Samun cutar suga ya dogara ne da ƙwayoyin halittar mutum da kuma muhallinsa, amma za ka iya taimaka wa kanka wajen rage sukarin da ke cikin jini ta cin abinci mai lafiya da kuma yawan motsa jiki.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mataki na farko da mutum zai iya bi shi ne nisantar abincin ko abin sha da aka sarrafa mai yawan sukari.
Sukarin da aka sarrafa da kuma hatsin da aka sarrafa suna da ƙarancin sinadaran gina jiki kasancewar an cire abubuwa masu amfani kamar 'fiber' da sinadaran gina jiki na bitamin daga cikin su.
Misalan irin waɗannan su ne fulawa da burodi na yau da kullum da farar shinkafa da farar taliya da su lemon kwalba ko na gwangwani, da alawa da dai sauransu.
Abincin mai lafiya ya haɗa da ganyayyaki da ƴaƴan itatuwa da wake da hatsin da ba a sarrafa bab.
Akwai kuma abubuwan ci nau'in gyaɗa da kifi nau'in sadin da salmon da mackerel da dai suaransu.
Yana kuma da kyau a dinga bayar da tazara wajen cin abinci da kuma ƙaurace wa cin abinci a lokacin da mutum ba ya jin yunwa, waɗannan abubuwa ne masu mahimmanci.
Motsa jiki na iya taimakawa wajen rage yawan sukari a cikin jini.
Tsarin Kiwon Lafiya na Biritaniya (NHS) ya bayar da shawarar mosta jiki na tsawon sa'o'i 2.5 a mako guda, wanda zai iya haɗawa da tafiyar sassarfa da kuma hawa matakala.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙiba maras cutarwa kan iya rage yawan suga da ke jinin mutum, idan mutum na buƙatar rage ƙiba, to ya gwada yin hakan a hankali, kamar rage tsakanin 0.5kg zuwa 1kg a mako.
Kuma yana da mahimmanci mutum ya guje wa shan taba kuma ku lura da yawan kitsen cholesterol ɗin jiki don rage hatsarin cututtukan zuciya.
Mene ne matsalolin ciwon suga?
Yawan sukari a cikin jini na iya yin mummunan illa ga hanyoyin jini.
Idan jini ba ya gudana da kyau a cikin jikin mutum, ba zai kai ga sassan jikin da ke buƙatarsa yadda ya kamata ba, wanda hakan ke ƙara hatsarin lalacewar wasu gaɓoɓi (rashin jin zafi), da daina gani da kuma ciwon ƙafa.
Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ta ce ciwon suga shi ne babban abin da ke kawo makanta, da cutar ƙoda da bugun zuciya da shanyewar jiki da kuma yanke wasu ɓangaren jikin mutum.

Asalin hoton, Getty Images
A cikin shekarar 2016, an kiyasta mutuwar mutane miliyan 1.6 ta hanyar ciwon suga kai tsaye.
Mutane nawa ne ke da ciwon suga?
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, adadin masu fama da ciwon suga ya ƙaru daga miliyan 108 a shekarar 1980 zuwa miliyan 422 a shekarar 2014.
A cikin shekarar 1980, ƙasa da kashi 5 cikin 100 na mutane sama da shekara 18 na da ciwon suga a duniya - a cikin shekarar 2014, adadin ya kasance kashi 8.5 cikin 100.
Ƙungiyar kula da masu ciwon suga ta Duniya ta kiyasta cewa kusan kashi 80 cikin 100 na manya da ke fama da wannan cuta suna cikin ƙasashe masu matsakaicin hali da masu ƙaramin karfi, inda yanayin cin abinci ke canzawa cikin sauri.
A manyan kasashe kuma da suka suka ci gaba, ana danganta ciwon da talauci da cin abinci mai arha da kuma abincin da aka sarrafa.














