Za a rage farashin maganin insulin na ciwon suga - WHO

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayar da sanarwar bullo da wani shiri da ke yunkurin rage matukar tsadar farashin maganin insulin na masu ciwon suga.
Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya tana son ganin sauran kamfanonin sarrafa magunguna sun samar da makamancin insulin, wanda za ta gwada ingancinsa.
Tun bayan gano shi a shekarar 1923, farashin insulin ya rika tashi a Amurka daga dala daya kan 'yar kwalbar allurar ruwan maganin zuwa kimanin dala 300.
A cewar Hukumar Lafiya akwai mutane kimanin miliyan 20 da ke fama da larurar ciwon suga nau'i na biyu kuma suna bukatar allurar insulin akai-akai don su rayu.
Mutum miliyan 54 a fadin duniya da ke fama da lalurar ciwon suga nau'i na 2 na amfani da insulin ne kadai idan cutar ta yi tsanani.
Mukhtari Adamu Bawa na BBC ya tuntubi Dr. Bashir Mijinyawa, wani likita a birnin tarayyar Najeriya Abuja, kan ko yaya yanayin ciwon suga yake a kasar.
Latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron hirar:








