Ta ya za mu daƙile cutar haukan karnuka?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Onur Erem
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 6
Gargaɗi: Wannan labarin na ƙunshe da bayanan raunukan da aka samu daga cizon karnuka
Ciwon haukan karnuka ya zama wata barazana a duniya, inda take kashe kusan mutum 60,000 a kowace shekara, kuma Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO na alaƙanta kashi 99 cikin 100 na matsalar da cizon karnuka da kuma raunukan da aka samu sakamakon cizon.
Duk da cewa akwai riga-kafin cutar - da ake bai wa mutum da zarar kare ya cije shi, musamman wanda aka ciza a fuska ko kusa da jijiya - ba koyaushe yake aiki ba.
Nirmal mai shekara huɗu na wasa a ƙofar gidansu da ke garin Arakkonam, lokacin da kare ya cije shi a watan Yuli.
Karen ya cije yaron a baki jim kaɗan bayan mahaifinsa ya shiga gida, don wani uzuri''
“Na shiga gida ne domin na sha ruwa,” kamar yadda mahaifinsa Balaji ya shaida wa wata kafar yaɗa labarai a ƙasar.
“Bayan na dawo, na gan shi da raunuka a bakinsa, yana ta zubar da jini mai yawa.”

Asalin hoton, BALAJI FAMILY
An kai Nirmal asibiti, inda ya ɗauki tsawon kwana 15 yana ana yi masa magani.
Sannu a hankali ya riƙa samun sauƙi, har zuwa lokacin da aka sallame shi.
To amma bai jima da komawa gida ba ya fara nuna alamun cutar haukan karnuka.
Nan take aka sake mayar da shi asibiti, inda aka gano cewa cutar ta shafi hanyoyin isar da saƙon ƙwaƙwalwarsa. Kwana biyu bayan haka ya ce ga garinku nan.
A wasu lokutan, wasu ƙananan yara kan ji tsoron faɗa wa iyayensu idan kare ya cije su, lamarin da ke hana su samun allurar riga-kafin cutar haukan kare a kan kari.
A birnin Mumbai, karnuka sun ciji mutum aƙalla miliyan 1.3 tsakanin shekarun 1994 zuwa 2015, kuma 434 daga ciki sun mutu sakamakon cutar.
To sai dai ba cizon ne kaɗai hatsarin da karnukan ke haifar wa mutane ba.
Gidauniyar Kula da Dabbobi ta Duniya (ICAM), ta ce wasu matsalolin da karnukan ke haifarwa sun haɗa da hatsari a kan tituna, da hana dabbbobi da mutane gudanar da al'amransu a kan layi ko tituna.
Sabon salo da Turkiyya ta ɗauka mai cike da ce-ce-ku-ce
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yawan karnukan da ake kiwo na ƙaruwa a Turkiyya, inda gamayyar ƙungiyar likitocin dabbobin ƙasar ta ƙiyasta cewa akwai karnuka kimanin miliyan 6.5 a ƙasar.
Kuma karnukan sun kashe fiye da mutum 100 a ƙasar cikin shekara biyu da suka wuce, ko dai kai-tseye ko ta hanyar haddasa hatsarin ababen hawa, kamar yadda hukumar kiyaye aukuwar haɗura ta ƙasar ta bayyana.
A ƙarshen watan Yulin da ya gabata, gwamnatin ƙasar ta amince da wata doka da ta tilasta janye karnukan da ke yawo a titi zuwa cikin gidaje nan da shekara huɗu masu zuwa, inda dokar ta tanadar da hukuncin ɗaurin gidan yari ga duk wanda ya bijire mata.
“Suna far wa ƙananan yara, da manya da tsofaffi da sauran dabbobi,” in ji shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan bayan ya aike wa majalisar dokokin ƙasar ƙudurin dokar. “Suna haifar da hatsura kan tituna.”
Tun 2004, a dokance dole ƙananan hukumomin ƙasar su karɓi riga-kafi, kuma su ɗauki karnukan da ke unguwanni su yi musu riga-kafin sannan su sake mayar da su unguwannin da suke.
Hakan na nufin kashi 70 cikin 100 na karnukan na buƙatr riga-kafin, in ji Dakta Gülay Ertürk na ƙungiyar likitocin dabbobin ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
A ƙarƙashin sabuwar dokar, za a riƙa fiɗiye karnuka tare da yi musu riga-kafi, sannan kuma a riƙa killace su a wani wuri a maimakon mayar da su kan tituna ko layuka.
Hukumar kula da kariyar dabbobi ta ƙasar, ta yi gargaɗin cewa tsarin zai laƙume kudi mai yawa, sannan kuma killace su a wuri guda zai sa manyan karnuka su hana ƙanana cin abinci, sannan kuma sai cutar ta yaɗu cikin sauri.
Sabuwar dokar ta fuskanci jerin zanga-zangar adawa a ciki da wajen Turkiyya.
Mun tuntuɓi hukumomin Turkiyya, amma ba mu samu amsa ba kafin haɗa wannan rahoto.
Wace hanya ce mafi dacewa ta rage yawan karnuka?
Dakta Hiby ta Gidauniyar Kula da Dabbobi ta ICAM ta ce fiɗiye dabbobin tun suna ƙanana zai taimaka wajen rage yawan karnukan.
Wannan hanyar za ta rage yawan hayyafar karnukan, saboda idan kare ya mutu ko ya ɓata zai yi wuya a sake haifo wani.
Ta ƙara da cewa abin da ba a gane ba shi ne, ''Janye karnukan daga kan titi, ba tare da magance haihuwarsu ba, ba zai hana su ci gaba da ƙaruwa ba''.
Karnuka kan haihu a kowane lokaci na shekara, kuma karya ɗaya kan iya haifar kusan 'ya'ya 20 a shekara.
Don haka janye su a kan titi tare da killace su wuri guda ba zai rage yawansu ba, a cewarta.
Dokar Majalisar Dinkin Duniya kan 'yancin ƙananan yara, ta bayyana ƙarara cewa dole ne a bai wa ƙananan yara kariya daga cutarwar dabbobi.
Nasarorin da aka samu a duniya
Bosnia-Herzegovina da Thailand a baya-bayan nan sun samu nasarar rage yawan karnukan da ke ƙasashen ta hanyar tattarasu wuri guda da fiɗiya da riga-kafi.
Gidauniyar Kula da Dabbobi ta Bosnia ta ce tattarawa da riga-kafin da fiɗiya ya haifar da raguwar karnukan da kashi 85 a babban birnin ƙasar Sarajevo, tsakanin 2012 zuwa 2023.
Gidauniyar kula da dabbobin na gudanar da wani gangamin wayar da kai kan alfanun fiɗiye karnukan ga masu su.
An samu ƙaruwar asibitocin fiye da ninki biyu, lamarin da ke ƙara samar da wadatuwar kula da karnukan.
Bayan samun nasarar shirin a birnin Sarajevo , an faɗaɗa shi zuwa wasu biranen ƙasar.
Shekara guda bayan haka a Thailand, Gidauniyar kula da karnuka ta Soi ta zama ƙungiya ta farko a tarihin ƙasar, da ta fara fiɗiya da riga-kafin dabbobi kusan miliyan guda a cikin shekara 20.

Asalin hoton, Getty Images
Kusan fiye da miliyan na karnukan da aka kama a babban birnin ƙasar, Bangkok aka kama su.
An fara wannan dogon aikin ne a wani ƙaramin tsibirin Phuket a 2003.
An yi nasarar rage yawan karnukan daga 80,000 zuwa 6,000 a Phuket.
Bayan samun nasarar a nan, sai aka faɗaɗa shi zuwa Bangkok, wanda ke da yawan karnuka a ƙasar.
Ƙasashen da har yanzu ke fama

Asalin hoton, Getty Images
A baya-bayan nan jami'ai a Moroko sun fara ɗaukar matakin rage yawan karnukan ƙasar.
Duk da cewa gwamnati ba ta bayar da dalilin hakan ba, wasu na ganin watakila hakan baya rasa nasaba da muradin ƙasar na karɓar baƙuncin gasar kofin ƙasashen Afirka ta 2025, da kuma kasancewarta cikin masu karɓar baƙuncin Gasar Kofin Duniya ta 2030.
Ƙungiyoyin fararen hula a Moroko sun yi ƙiyasin cewa ƙasar na da yawan karnuka da suka kai miliyan uku, kuma a kowace shekara ana rage kusan 500,000.
Kuma da yawa daga cikin waɗannan karnuka na far wa jama'a tare da haifar musu da guba.
Rage yawan karnukan ba zai iki ba, a cewar Mista Izddine saboda ''karnukan na hayayyafar ƙarin 'ya'ya, wanda kuma hakan ke ƙara yawan karnuka''.
Mun kuma tuntuɓi gwamnatin Moroko, biranen Casablanca da Marrakesh, sai dai duka ba su ce komai ba game da batun, kafin haɗa wannan rahoton.










