Yadda karnuka ke cin gawarwakin mutanen da aka binne a Gaza

...
Bayanan hoto, "Ban amince ni ko yarana su zauna kusa da maƙabarta ba," in ji Rehab Abu Daqqa
    • Marubuci, Daga Fergal Keane
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliya ta musamman a Jerusalem

Yaran na jiyo karnuka na haushi a waje, kusa da dauɗaɗan robobin tanti.

Yayan Rehab Abu Daqqa bakwai sun taru a kan mahaifiyarsu. Ita ce wurin tsira na ƙarshe a rayuwarsu.

Yaran da mahaifiyarsu sun ga abubuwa da dama da ba za a iya faɗa wa wanda bai ga abin da suka gani ba.

Akwai wata kalma da za a iya kwatanta abin da yaro ke ji, sanin cewa taku kaɗan daga inda yake, dabbobi ke zaƙulo gawa daga kabari?

Kalamai ba za su misalta abubuwan muni da ke fitowa ba daga wannan maƙabartar gaggawa a Rafah.

Abin tsoro ne kalmomin da Rehab Abu Daqqa ta yi amfani da su.

GARGAƊI: Wannan rahoton na ƙunshe da bayanan da ka iya tayar da hankalin wasu masu karatu

Wannan daidai ne. Sai dai akwai ƙari kan haka, ta bayyana. Yaran sun ga karnuka suna cin gawawwaki.

Ƙafar mutum rataye a kan katanga. Eh haka, sun tsorata. Amma sun yi tawaye, sun kuma kasa fahimta.

Yaran da a baya suke da gida, suke zuwa makaranta, suna zaune cikin wadatar da iyalinsu ke da shi, a yanzu sun zama ƴan ci-rani a wurin da ke hararo masu mutuwa.

"A wannan safiya, karnukan sun zaƙulo wata gawa daga ɗaya daga cikin kabarurruka kuma suna cin gawar."

Daga dare zuwa wayewar gari, karnukan ba sa barinmu mu yi barci... yaranmu kawai suna riƙe ni saboda tsananin tsoro." In ji Rehab Abu Daqq.

Karnukan na zuwa ne da yawansu. Dabbobin gida da masu su suka mutu ko suka ɗaiɗaita, haɗi da mutanen Rafah da suka rasa matsuguni, dukkansu a yanzu suke farautar duk wani abu da za su iya kai wa baka.

Maƙabartar na da kabarurruka marasa zurfi inda mutane ke binne ƴan uwansu zuwa lokacin da za su iya ɗauke su domin yi masu sutura a yankinsu.

A wasu kabarurrukan, ƴan uwa na ajiye bululluka domin yi wa gawawwakin kandagarki daga karnukan.

Yara sun zama masu zanen kabari

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rehab Abu Daqq ta rame kuma a gajiye take. Bakinta da hancinta rufe da ƙyalle domin kare kanta daga warin da ke tashi daga kabarurrukan.

Ta yaba wa matasa maza da suka zo tun da farko domin sake binne gawarwakin da aka zaƙulo daga kabarurrukan a wannan safiya.

"Ban yarda cewa ni ko yarana su yi rayuwa kusa da maƙabarta ba. Ɗana yana aji na uku kuma a maimakon ya yi wasa, sai ya kasance yana zana kabari kuma a tsakiya, sai ya zana gawa. Waɗannan sune yaran Falasɗinawa... Me zan faɗa maka? Mummunan yanayi, wannan kalmar ma ba ta fayyace ma'anar ba."

Maƙabartar ɗaya ce cikin maƙabartun da ke Gaza da ta zama wurin mafaka ga mutanen da aka lalata gidajensu a yaƙin.

Akwai fiye da mutum miliyan 1.4 da suke cunkushe a Rafah - adadin ya ninka sau biyar na yadda garin yake kafin soma yaƙi.

Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Norwegian Refugee Council ta ƙididdige cewa akwai mutum dubu 22 a kowane murabba'in kilomita.

Tuni ma cututtuka ke yaɗuwa inda aka samu ɓarkewar gudawa da ciwon hanta nau'in hepatitis A da kuma sanƙarau - da kuma matsalar yunwa da ake fama da ita.

Yanayin da ake ciki a Rafah

Rafah wuri ne da ƴan gudun hijirar Gaza suka isa bangon ƙarshe, iyaka da Masar wadda aka rufe abin da ya hana galibin mutanen da suka ɗaiɗaita shiga.

Sun isa bayan da sojojin Isra'ila suka yi ta tura su daga nan zuwa can. Sau uku Rehab Abu Daqqa na tserewa kuma wataƙila sai ta tono gawar ƴan uwanta nan kusa idan har dakarun Isra'ila suka ci gaba da kai farmaki a Rafah.

Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce harin da sojoji ke kai wa a Rafah zai ɗore ko an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ko a a, domin wargatsa abin da ya kira bataliyar mayaƙan Hamas a birnin.

Hamas ta dage cewa ba za a iya cimma yarjejeniya ba ba tare da wani alƙawari na kawo ƙarshen yaƙin ba.

Mambobin majalisar gwamnatin haɗin gwiwa masu ra'ayin riƙau na gargaɗin Mista Netanyahu kan cimma yarjejeniya.

Ministan kuɗi, Bezalel Smotrich, mai rajin samar da ƙasar Isra'ila, ya yi kira da a "a yi rusau a Rafah, inda ya ce ba za a yi aiki rabi da rabi ba.

"Ina [ƴan gudun hijira] za su koma?" kamar yadda Dakta Rik Peeperkorn, daraktan yanki na hukumar lafiya ta duniya ya tambaya wanda a baya-bayan nan ya dawo daga Rafah.

...
Bayanan hoto, Dr Rik Peeperkorn daga WHO ya yi gargaɗi cewa kai farmaki a Rafah zai ƙara haifar da bala'in jin ƙai

Halin da ake ciki a Rafah ta fuskar lafiya

"Maganar da ake a yanzu harkar lafiya na cikin wani yanayi. Muna da ƙalubalen ruwa da tsaftataccen muhalli da na abinci. Akwai bala'in jin ƙai. A don haka, za a ƙara shiga matsalar jin ƙai ne...

Abin da muke tsammani shi ne ƙaruwar mace-mace da rashin lafiya idan sojoji suka yi kutse. Don haka, hakan na nufin ƙarin mace-mace da yaɗuwar cututtuka."

Dakta Peeperkorn ya yi aiki tsawon shekara bakwai a Afghanistan tare da Majalisar Ɗinkin Duniya kuma ba mutum bane mai saurin karaya.

Amma da muka haɗu a birnin Ƙudus, yana cikin yanayi na gajiya. Gajiyar mutumin da ya saba tashi kowace safiya ga tabbacin rikici wanda da alama ke cikin barazanar dagulewar lamura.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO tuni ta fara shirin samun ƙarin asibitoci domin taimaka wa mutane idan aka tilasta masu fita.

Amma me zai faru ga mutanen da ke cikin yanayin rai kwa-kwai-mutu kwa-kwai da tsofaffi, da marasa lafiya 700 da ake yi wa wankin ƙoda wanda suke samun kulawa a cibiyar da a baya take kula da mutum 50?

"Idan ka duba ɓangaren lafiyarmu, ya durƙushe, kuma kutsen sojoji na nufin za mu yi asarar ƙarin asibitoci uku... wataƙila an lalata su. Muna shiriyawa haka da wani tsari kamar na wucen gadi."

...
Bayanan hoto, Wani yaro na samun kulawa a asibitin European hospital da ke Rafah

Abokan aikina na BBC sun samar da shaidu masu tayar da hankali na yanayin da asibitoci ke ciki, suna naɗar bidiyon asibitocin a kowace rana. A asibitin European hospital a Rafah, an cunkusa iyalai a wuri ɗaya, a ƙarƙashin ƙasa da harabar asibitin. Suna dafa abinci a ɗakin marasa lafiya. Ƴaƴansu na karakaina a duhun kwararon asibitin suna wuce waɗanda suka ji rauni da ake tura su a keken guragu, wata tsohuwa na zaune tana kallo.

A ɗakin ba da agajin gaggawa, Yassin al Ghalban mai shekara 11 na kuka kan gadonsa. An yanke ƙafafuwansa bayan wani hari ta sama da aka kai. Ɗan uwansa tsaye a gefen gadonsa ya ce "yana rayuwa ne ta hanyar shan magungunan kashe zafi".

...
Bayanan hoto, Yassin al Ghalban mai shekara 11 na kwance kan gado a asibitin European Hosptital da ke Rafah

A maƙabartar, Rehab Abu Daqqa na kallon ƴaƴanta suna wasa a kusa da kabarurrukan. Karnukan sun tafi amma yaran suna kusa da mahaifiyarsu. Nan ba da daɗewa bane za ta sauya matsuguni saboda ba za ta iya jurewa ganin yaranta a irin wannan wuri ba.

Babu batun makoma a nan. Fata a Gaza ya bambanta ga kowa. Yana iya yankewa cikin daƙiƙa ɗaya idan aka kashe ɗan uwanka. Sannan kana rasa abin cewa yayin da tambayoyin yara ke taruwa.

Waɗanda suka ba da gudummawa Alice Doyard da Haneen Abdeen