Karnuka suna iya gane idan mai su ya galabaita ta numfashinsa

Asalin hoton, Queen's University, Belfast
Karnuka sun sake tabbatar da cewa sun damu da ire-iren halayen da muke ciki - wannan karon sun yi hakan ne ta hanyar gwajin kimiyya kan sansano ko shakar wani abu.
Masana kimiyya sun gano cewa karnuka suna iya gane idan masu su sun yi jigata ta hanyar numfashi ko gumin jikinsu.
An bai wa karnuka hudu horo - bayan da masu su suka amince - domin su "zabi" daya daga cikin gwangwanaye uku da ke dauke da abubuwan sansanawa.
Kuma a gwaje-gwaje fiye da 650 cikin 700 da aka gudanar, sun yi nasarar gane samfurin gumi ko numfashin da aka dauka daga jikin mutumin da ya yi matukar gajiya.
Masu binciken, na Jami'ar Queen's da ke Belfast, suna fatan sakamakon binciken, wanda aka wallafa a mujallar Plos One, zai taimaka wajen bayar da horo ga karnukan da za su taimaka don yi wa mutum maganin damuwa.
Karnuka suna fahimtar abubuwan da ke faruwa a kewayensu ta hanyar shakar iska.
Tuni dai ake amfani da basirarsu ta iya sansano abubuwa wajen gano miyagun kwayoyi da rashin lafiya, ciki har da cutar kansa da ciwon suga har ma da cutar korona.
"Muna da shaidu da dama da ke nuna cewa karnuka suna iya sansano wasu cututtuka da dan adam yake fama da su - sai dai ba mu da isassun shaidun cewa karnukan za su iya sansano mabambantan yanayi na dabi'a ko halayyar dan adam," a cewar jagorar bincike Clara Wilson.

Asalin hoton, Victoria Gill
Mutum 36 ne suka amince a dauki yanayin gajiyarsu kafin da kuma bayan sun yi wani lissafi mai matukar wahala.
Kowanne gwangwani yana dauke da samfurin gumi ko numfashinsu da aka dauka kafin da kuma bayan sun yi lissafin inda bugawar jini da zuciyarsu ta karu.
Kuma idan karnukan suka tsaya kyam a kusa da samfurin gumi ko numfashin mutumin da ke nuna "jigata", ana ba su abincin da suka fi kauna domin nuna godiya.











