Ashe karnuka suna kukan murna?

Ashe karnuka suna kukan murna?

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Karnuka suna iya yin kukan murna idan suka sake haduwa da masu su, a cewar wani bincike da masana na kasar Japan suka yi.

Masana kimiyya sun yi amannar cewa karnuka suna zubar da 'hawaye na murna' sakamakon fitar da sinadarin oxytocin.

Masaniyar halayyar dabbobi kuma likatarsu Katey Aldred daga Birtaniya ta ce sosuwar ran karnuka gaskiya, sai dai za a dauki tsawon lokaci kafin a samu cikakken bayani kan hakan.