Wani kare ya kai kansa asibiti domin jinya
Wani kare da ke dingishi ya kai kansa asibitin dabbobi sannan ya nemi a taimaka a duba farcen kafarsa da yake ciwo.
Hoton CCTV da aka nuna lokacin da ake yi masa tiyata ya karade shafukan intanet a birnin Juazeiro do Norte na kasar Brazil.
Ya nuna karen yana dingishi yayin da yake shiga asibitin sannan ya zauna a kusa da wani bango.