Waɗanne matakai jami'o'i ke bi wajen ba da digirin girmamawa?

Asalin hoton, Farouk/Kperogi
A ƙarshen makon nan ne muhawara ta kaure a tsakanin masu hulɗa da kafafen sada zumunta dangane da bai wa shahararren mawaƙin nan, Dauda Kahutu Rarara digirin digirgir na girmamawa.
Ra'ayoyin masu mahawarar ya kasu gida biyu - wani ɓangare ke cewa sam wanda aka girmama ɗin bai cancanta ba, inda ɗaya ɓangaren kuma yake da ra'ayin cewa Rarara ya cancanci karramawar sai dai kuma fitowa da jami'ar ta yi ta barranta kanta da batun ya sauya musu tunani.
BBC ta yi nazari dangane da matakan da jami'o'i ke bi wajen zaƙulo mutanen da suka cancanci karramawa da digirin digirgir.
Mene ne digirin girmamamawa?

"Digirin girmamawa ko kuma Honoris Causa kamar yadda yake a Turanci, shi ne digiri na digirgir da ingantacciya, tabbatacciya kuma sananniyar jami'a take bai wa wasu waɗanda suka yi wa al'umma aiki a fannonin rayuwa daban-daban", kamar yadda Farfesa Uba Abdallah ya shaida wa gidan jaridar Alƙalanci.
Matakan da jami'o'i ke bi

Asalin hoton, Getty Images
BBC ta tuntuɓi Malam Ibrahim Sheme wani marubuci a Najeriya kuma ma'aikaci a jami'ar koyo daga gida ta National Open University of Nigeria.
Kuma ya shaida cewa Jami'a ce kaɗai za ta ita tantance wanda ya dace ta ba digirin girmamawa. Kuma akwai tsarin da ake bi kamar haka:
- Kafa kwamitin ƙwararru:
Kafin jami'a ta bai wa wani mutum digirin girmamawa dole ne da farko ta kafa wani kwamiti na ƙwararru wanda zai yi nazarin mawaƙin da ya dace.
A irin wannan kwamitin ne za a kawo sunayen mutane daga fannin rayuwa daban-daban walau dai waƙa ko rubutu ko ma bautawa al'umma domin tantance mutanen da ya kamata jami'ar ta girmama ɗin.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sannan dole ne ƴan kwamaitin su bayar da gamsassun dalilan da dangane da mutanen da za a girmama ɗin ta yadda duk wanda ya ji dalilan shi ma zai gamsu.
- Cancanta:
Ɗaya daga cikin dalilan da jami'o'i ke bi wajen karrama wasu mutane da digirin girmamawa shi ne dole ne wanda za a karrama ɗin ya zama abin koyi da hange ga al'umma ciki kuwa har da ɗaliban ita wannan jami'a.
Jami'o'i kan kalli irin gudunmowar da wanda za a karrama ya bayar ga al'umma ta hanyar kimiyya, fasaha, ilimi, kasuwanci da sauran ayyukan bautatawa al'umma.
- Ba a bai wa masu riƙe da muƙaman siyasa:
Farfesa Uba Abdallah, tsohon shugaban jami'ar koyo daga gida, ya ce a ƙa'idar jami'o'in Najeriya kamar yadda kwamitin shugabannin jami'i'in ƙasar suka zartar ba a bai wa mai riƙe da muƙamin siyasa digirin girmamawa.
"Kwamitin shugabannnin jami'a bai yarda da shi shi ne sun haramta bai wa duk wani mai riƙe da muƙamin siyasa a ba shi digirin girmamawa ba. Misali a kamar a ce gwamna. sun hana wannan saboda za a ga kamar siya ya yi. Amma idan ya sauka aka duba ayyukan da ya yi to za a iya ba shi," kamar yadda Farfesa Abdallah ya shaida wa gidan jaridar Alƙalanci.
Ko ana iya sayen digirin girmamawa?
Farfesa Abdallah Uba Adamu ya ce lallai akwai wani digirin girmamawar da sayar da shi ake yi.
"Akwai wanda sayan sa ake yi kai tsaye...idan kana da kuɗi dubu ɗari uku ko huɗu ko biyar ko dubu ɗari shida idan kana da su ka kai sai a ba ka. Akwai jami'o'in da suke da abin tsoro waɗanda ake da shakku a kansu to su ne suke yin wannan. Amma ba kasafai ake samun su a Najeriya ba. Ana samun su a Caribbean Island...Sai su ce za su ba ka wannan digirin...",kamar yadda Farfesa ya shaida wa Alƙalanci.
Wallahi ko ƙwandala ban bayar ba - Rarara

Asalin hoton, RARARA/INSTAGRAM
Fitaccen mawaƙin nan na arewacin Najeriya, Dauda Kahuru Rarara wanda a ƙarshen makon nan aka karrama shi da digirin girmamawa ya ce saɓanin abin da jama'a da dama ke faɗi cewa kuɗi ya bayar aka ba shi digirin na karramawa.
"Wallahi tallahi ban bayar da ko ƙwandala ɗaya ba bayar ba. Han ransuwa na ji Aisha (matarsa) ta ce za ta ce za ta ɗan yi wani dangane da abinci da za ta bayar a wurin taro. Ni mutanen nan kawai sun ce min za su yi taron karrama ni ranar kaza a wuri kaza idan ina da mutane na gayyato." In ji Rarara a hirarsa da kafar watsa labarai ta DCL.
Dangane da martanin da Rarara ya mayar kan masu ce masa bai dace da digirin na karramawar ba kasancewar bai yi karatun boko ba.
"Ni da na sauke Alƙur'ani sau biyu ɗaya a gaban mahaifina. To mene ne kuma zai gagare ni." In ji Rarara.
Martanin European American University
Jami'ar European American University wadda rahotanni suka ce ita ce ta bai wa Dauda Kahuru Rarara da wasu mutum uku digirin girmamawa ta ce sam ba ita ba ce.
Jami'ar wadda ta wallafa sanarwar tata a shafinta na website ta ce "karramawar ƙarya: Ba mu da masaniyar ba da digirin karramawa ga Dauda Kahutu Rarara."
Jami'ar ta ce ba ta ma amince da wani taron yaye ɗalibai a Abuja ba ballantana mu karrama wani, inda ta ce al'amarin kawai damfara ce.
Har wayau jami'ar ta ce ba ta da masaniyar sauran mutanen da aka bai wa digirin na girmamawa baya ga Rarara da suka haɗa da Alhaji Ahmed Saleh Jnr, da Mustapha Abdullahi Bujawa da kuma Tarela Boroh.











