Turawa biyar da suka bai wa harshen Hausa gudunmowa

Wasu turawa da suka bai wa harshen Hausa gudunmowa

Asalin hoton, Google

Lokacin karatu: Minti 5

A duk lokacin da aka yi maganar ci gaban harshen Hausa dole ne a yi batun rubutu da karatu a cikin harshen.

A yanzu haka harshen Hausa na cikin manyan harsunan duniya da ake amfani da su a kafafen yaɗa labara a duniya da shafukan sada zumunta.

An fara karatu da rubutu irin na boko a cikin harshen Hausa tun a ƙarni na 19, kamar yadda tarihi ya nuna.

Akwai Turawa da dama da suka bai wa harshen Hausa gudunmowa wajen haɓakarsa ta hanyar karatu da rubutu.

Wasu daga cikinsu sun taɓa zuwa ƙasar Hausa inda suka yi rayuwa da Hausawa, suka fahimci al'adu da ɗabi'unsu.

A wannan maƙala mun rarrayo muku wasu Turawa biyar da suka bayar da gudunmowarsu wajen haɓaka harshen Hausa a duniya.

Paul Newman (Masanin harshe)

An haifi Paul Newman - wanda Ba'amurke ne masanin harsunan Afirka - a shekarar 1933.

Ya koyar da Jami'ar Yale da ke Leiden a Amurka.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A yanzu haka Newman shi ne babban Farfesa a sashen kimiyyar harshe na Jami'ar Indiyana ta Amurka, bayan da ya jagorancin sashen na tsawon wa'adi biyu.

Newman ya taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka hanyar harshen Hausa da ma wasu harsunan Afirka ta hanyar rubuce-rubucensa.

Ya taɓa zuwa ƙasar Hausa inda har ya taɓa koyarwa a sashen nazarin harsunan Najeriya a Jami'ar Bayero da ke Kano, kamar yadda Farfesa Aliyu Muhammad Bunza na Jami'ar Dan Fodio da ke Sokoto ya bayyana.

Ayyukansa

Wasu daga cikin rubuce-rubucen da ya yi a harshen Hausa sun haɗa da:

  • 1977. Sabon ƙamus Na Hausa Zuwa Turanci
  • 2000. The Hausa Language: An Encyclopedic Reference Grammar. New Haven.
  • 2002. Chadic and Hausa Linguistics: Selected Papers of Paul Newman, with Commentaries
  • 2007. A Hausa–English Dictionary. New Haven
  • 2022. A History of the Hausa Language. Reconstruction and Pathways to the Present
  • 2004. Klingenheben's Law in Hausa. Köln: Rudiger Köppe Verlag.
  • The Hausa Negative markers', Great Vowel Tone classes and Exention in The Hausa verbal System.

Dakta Sani Dauda Ibrahim wani masanin kimiyyar harshe a Kano ya shaida wa BBC cewa Paul Newman ya bayar da gagarumar gudunmowa wajen haɓaka harshen Hausa.

Ya ce littafin da ya rubuta a 2018 mai suna 'The Comprehensive Bibliography of Chadic and Hausa Linguistics', ya kasance jigo a fagen ilimin nazarin harsuna.

Dakta Sani ya ce abin da littafin ya ƙunsa shi ne ya tattaro duka ayyukan da aka yi cikin harsunan gidan Chadi da Hausa tun daga 1790 zuwa 2018.

''Wani abin mamaki shi ne an tattara maƙaloli da littafai da ayyukan bincike na digiri na ɗaya da na biyu da na uku da aka yi sama da 3,500, amma daga ciki kusan 2,000 duk a kan harshen Hausa aka yi su'', a cewar Dakta Sani Dauda.

Bayan ya tattara waɗannan bayanan sai kuma ya sake rubuta wani littafi a 2022 mai suna ''A History of the Hausa Language. Reconstruction and Pathways to the Present''.

Dakta Sani ya ce abin da ya sa Newman ya rubuta wannan littafi shi ne har yanzu babu wani littafi da aka rubuta da ya bibiyi tarihin harshen Hausa a shekarun da suka wuce, ya yi bayani, da halin da harshe ke ciki a yanzu, matsayinsa da darajarsa da tasirinsa ya kuma bayyana inda harshen ya nufa a yanzu.

''Ya faro ne tun daga haruffan Hausa da ginin jimla da darajarsa a yau da kuma inda ya nufa'', in Dakta Sani Dauda Ibrahim.

G P Bargery

An haifi George Percy Bargery ranar 1 ga Oktoban 1876, wanda fitaccen masanin harshe ne kuma baturen mishan ɗan asalin Ingila.

Bayan ya kammala Jami'ar Landan, Bargery ya fara aiki da cocin ƴanmishan a 1899.

Ya shiga jerin mishan da ke aiki da turawan mulkin mallaka, inda aka tura shi arewacin Najeriya, inda ya yi aiki har zuwa 1910.

A tsawon lokacin da ya ɗauka a rewacin Najeriya ya koyi harshen Hausa - wanda shi ne harshen da aka fi magana da shi a yankin - har ma ya yi rubuce-rubuce a cikinsa a matakin karatunsa na digiri na uku.

Ya koma Ingila da zama na dindindin a shekarar 1957, inda Daular Birtaniya ta karrama shi da lambar yabo ta OBE.

Ayyukansa

Bargery ya kasance ɗaya daga cikin Turawan da suka hidimta wa harshen Hausa.

Ya rubuta ƙamusan Hausa zuwa Turanci a shekarar 1934, inda ya fassara kalmomin Hausa masu yawa zuwa harshen Turancin.

''Wannan ƙamusun na da kalmomi fiye da 30,000'', in ji Farfesa Bunza.

Ƙamusun ya yi fice sosai tare da samun ƙarɓuwa, lamarin da ya kai ga har sai da Jami'ar Landan ta ba shi digirin girmamawa a 1937.

Bargery ya ci gaba da koyar da harshen Hausa a Jami'ar Landan, inda har ya zama farfesa a harshen Hausa.

Baturen ya rubuta maƙaloli masu yawa cikin harshen Hausa da aka tattara a Jami'ar ta Landa.

Graham Furniss

Ya taɓa riƙe shugaban Hausa a Jami'ar Landan, ana kuma yi masa laƙabi da ''Uban Hausa'', kamar yadda Farfesa Bunza ya bayyana.

An haifi Graham a Indiya, ya kuma kasance malamin Ingilishi a yankin Casamance da ke kudancin Senegal, kafin ya yi digirinsa na farko a 1968.

Bayan kammala digirinsa na farko kan harshen Hausa da tarihin zamantakewar Hausawa, ya tafi zuwa Kano domin yin digirinsa na uku kan waƙoƙin al'umomin garin, wanda ke arewacin Najeriya.

Yayin da da yake digirinsa na uku, a kwalejin Abdullahi Bayero da Kano - wadda daga baya ta koma Jami'ar Bayero - ya riƙa koyar da ɗaliban digirin farko na wucin gadi.

Bayan kammala digirinsa na ukun, ya fara koyarwa a sashen nazarin harsuna da kimiyyar harshe na jami'ar Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Ya koma Landan a 1979 inda ya riƙa koyar da Hausa a Jami'ar Landan, musamman fannonin furuci da rubutun adabi da kuma al'ada, waɗanda su ya fi ƙwarewa a kai.

Ya riƙe muƙaman shugaban sashen nazarin Afirka da shugaban sashen harsuna, sannan shugaban cibiyar nazarin harsuna duka a Jami'ar ta Landan.

Ayyukansa

Furniss ya yi rubuce-rubuce masu yawa a harshen Hausa da suka ƙunshi waƙoƙi da zube da wasannin kwaikwayo.

An kuma wallafa rubuce-rubucen nasa a sigar tatsuniyoyi da rubutattun waƙoƙi, da maƙaloli, yayin da wasu wasannin ƙwakwayon da ya rubuta aka shirya tare da gabatar da su a gidan talbijin.

Philip J. Jagger

Philip Jaggar, Farfesa ne masanin kimiyyar harshe a Jami'ar Landan, kuma wanda ake ɗauka matsayin sha kundum harshen Hausa.

Ya kwashe wata biyu yana koyar da harshen Hausa da sauran harasa dangin harsunan gidan Chadi kuma masanin harsunan Afirka.

Baturen ɗan ya samu digirinsa na biyu da na uku a Jami'ar California da ke Amurka a 1985.

Ayyukansa

Philip J. Jagger ya kwashe shekaru masu yawa, yana koyar da harshen Hausa da kimiyyar harshe a kwalejin Abdullahi Bayero da ke Kano (Wadda daga baya koma Jami'ar Bayero).

Haka kuma ya koyar da harshen Hausa a jami'o'in Hamburg da ke Jamus da Jami'ar UCLA ta Amurka, da kuma Jami'ar Landan.

Farfesa Aliyu Muhammad Bunza ya ce Philip J. Jagger ya rubuta wani littafin Nahawun Hausa da ya ce har yanzu babu kamarsa a fannin nahawun Hausa.

''Ya kuma rubuta wani littafi kan Hausawa Maƙera'', in ji Farfesa Bunza.

A.H.M Kirk-Greene

An haifi Anthony Hamilton Millard Kirk-Greene a Tunbridge Wells a Kent da ke Ingila a ranar 16 ga watan Mayun 1925.

Ya taɓa aiki a matsayin matuƙin jirgi a rundunar sojin Indiya daga 1943 zuwa 1947 lokacin yaƙin duniya na biyu.

Daga baya ya koma jami'ar Cambridge da ke Ingila, inda ya yi digiransa na farko da na biyu, kafin ya yi wani digirin na biyu a Jami'ar Oxford.

Kirk-Greene ya shiga ayyukan turawan mulkin mallaka a matsayin jami'in mulki, inda har ya zama babban kwamishinan gunduma a arewacin Najeriya.

A wannan lokaci ne ya soma sha'awar rayuwa da al'adun Hausawa da ma harshensu har ya koya ya kuma ƙware a kai.

Bayan samun ƴancin kan Najeriya, Kirk-Greene ya zama babban malami a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a jihar Kaduna daga 1961 zuwa 1965.

Farfesa Bunza ya ce Baturen - wanda daga baya ya koma Jami'ar Oxford - ya yi rubuce-rubuce masu yawa da suka taimaki harshen Hausa.

''Laƙabin da ake yi masa a Jami'ar Oxford shi ne Nigerianist (Dan Najeriya), saboda duk abin da ya shafi Najeriya babu abin da bai sani ba,'' a cewar Farfesa Bunza.