Dalilin da zai sa na fice daga PDP — Sule Lamido

Alhaji Sule Lamido tsohon gwamnan Jigawa
Lokacin karatu: Minti 2

Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya PDP na iya rasa wani babban jigonta inda tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya ce zai iya ficewa daga jam'iyyar idan har ba a magance rikicinta ba.

Alhaji Sule Lamido, ya ce matsawar ba a samu mafita a jam'iyyar PDP ba, zai duba jam'iyyar da zai yi kawance.

Tsohon gwamnan jihar Jigawa ya ce akwai matukar takaici yadda wasu ke kokarin lalle sai an kai jam'iyyar PDP kasa.

Cikin wata hira da ya yi da BBC, tsohon gwamnan na Jigawa ya ce idan har abubuwa suka ki tafiya yadda ya kamata, zai dauki matakin da yake gani ya fiye masa.

Ya ce," Zan fara duba Najeriya sannan kuma na kalli Jigawa wato jiha ta, sai na ga mene ne ya fi dacewa, sai mu yi ban gishiri in ba ka manda, sannan kuma kawance zan kulla da jam'iyyar da nake gani tafiye min."

Sule Lamido, ya ce " Ban ce ga jam'iyyar da zan iya komawa ba, domin akwai jam'iyyu da dama, zan tsaya na tace sai kuma mu ƙulla kawance."

"Dakatar da ni almara ce"

Babban jigon a jam'iyyar ta PDP, ya kuma tabo batun dakatarwar da jam'iyyar ta PDP ta yi masa daga kwamitin amintattu inda ya ce wannan wani al'amari ne tamkar almara saboda wadanda suka dauki matakin ba su san yadda aka kafa jam'iyyar ba.

Ya ce," A PDP ga baki daya yanzu a Najeriya, ba ni da sa'a, sannan kuma a PDP a yanzu babu wanda ya san yadda aka yi ta shekaru 27 da suka wuce, mafi yawanci a yanzu wadanda suke jam'iyyar PDP, masu girbi ne a gonar PDP bayan ta nuna aka girbe ake biyan bukata."

Alhaji Sule Lamido, ya ce," Akwai takaici a ce 'ya'ya ko jikoki su cewa kakansu wai ya bar gidansu, to ya je ina? Gidan gajiyayyu?".

A kwanakin baya Sule Lamido, ya shaida wa BBC cewa, an yi masa kora da hali a hedikwatar jam'iyyar ta PDP.

Ya ce, "Na zo hedkwatar PDP ne domin mallakar fom na takarar shugabancin PDP, amma na samu ofishin da ya kamata in je a kulle, da na tambaya sai aka ce min a hannun gwamnan Adamawa ne zan samu fom ɗin. Yanzu ana nufin sai na je Yola ne zan samu fom na takarar?"

Yanzu haka dai wasu na zargin akwai masu saka hannu a rigimar PDP, inda wasu ke zargin babbar jam'iyyar ƙasar ta APC, na yunƙurin jefa ta cikin rikici da hana ta sukuni ballanta ta shirya shiga zaɓe, zargin da APC ta sha musuntawa.