Abin da Tinubu ya faɗa min a Kaduna - Sule Lamido

Alhaji Sule Lamido

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Daya daga cikin dattawan babbar jam'iyyar hamayya ta PDP, Sule Lamido, ya ce za su ci gaba da yin gwagwarmaya duk da yadda aka gan shi suna hira da gaisawa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a kwanan nan.

Sule Lamido, wanda tsohon gwamnan jihar Jigawa ne, ya shaida wa BBC cewa abotarsa da Tinubu ba za ta hana shi ƙoƙarin haɗa kan 'yansiyasar Najeriya ba domin ci gaba da adawar da za ta kawo ci gaban kasar.

A ranar Juma'a ne aka ga Lamido da Tinubu suna wasa da dariya yayin ɗaurin auren ɗan Abdulazizi Yari da suka halarta a Kaduna, abin da ya fara jawo cecekuce tsakanin mabiya harkokin siyasar Najeriya.

Haka nan, an ga tsohon Mataimain Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ma ya kai wa Lamidon ziyara a makon da ya gabata, wanda suka daɗe a PDP tare kafin Atikun ya sanar da komawa ADC.

"Ni da Atiku mun yi PDP, lokacin yana mataimakin shugaban ƙasa ni kuma ina ministan harkokin waje. Mene ne laifi idan 'yan Najeriya suka taru domin tattauna yanayin ƙasarsu?" in ji shi.

'Ni da Tinubu mun san juna sosai'

Sule Lamido na cikin 'yan jam'iyyar adawa ta PDP da suka fi yin kakkausar suka ga APC mai mulki tun daga lokacin marigayi Muhammadu Buhari.

Sai dai alaƙarsa da Shugaba Tinubu ta daɗe, wadda ta faro tun shekarun 1990 da suka yi jam'iyar SDP tare.

Yayin haɗuwa tasu a masallacin Sultan Bello na birnin Kaduna ranar Juma'a da ta gabata, an ga su suna hira da raha tsakaninsu. Da aka tambaye shi kan me suka tattauna ya ce:

"Mun san junanmu sosai amma mun jima ba mu haɗu ba, kuma yanzu shi ne shugaban Najeriya.

"Na ce masa ka yi fes da kai wallahi. Shi ma ya ce min haka ka sauya? Sule ina son ka saboda kana da amana. Muka yi raha muka tafi."

'Haɗa kan ƴan'adawa'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai Sule Lamido ya ce daga cikin abubuwan da suka saka a gaba shi ne haɗa kan 'yan'adawa domin ci gaba da yi wa gwamnatin APC hamayya.

Duk da cewa Atiku da wasu jiga-jigan PDP sun sanar da ficewarsu daga jam'iyar zuwa ADC, Lamido ya ce yana nan a jam'iyyar amma yana mu'amala da sauran 'yan'adawa.

"Ba Atiku kaɗai ba wanda yanzu ba ma jam'iyya ɗaya, muna tattaunawa da mutane da dama wadanda a baya mun yi jam'iyya ɗaya amma yanzu kuma mun raba gari, dukkanmu 'yan Najeriya ne muna kuma so kasarmu ta ci gaba," in ji shi.

Game da jam'iyyar tasu ta PDP kuma, Sule ya ce suna aikin neman sulhu domin sasanta rikicin da ya dabaibaye ta.

"Ko shakka babu muna ta faɗi-tashin ganin mun yi sulhu a inda ya kamata a yi, sannan muna waya da tuntuba domin Najeriya ta ci gaba, kuma mu abin da muke yi ba domin kanmu muke ba don al'ummar kasar muke yi," a cewar tsohon gwamnan.

"Ba ni ba, duk wani ɗan Najeriya yana da haƙƙi a kan Shugaba Tinubu, kuma idan an ga yana ba daidai ba babu laifi a faɗa masa gaskiya."