El-Rufai bai isa ya sa mu bar PDP ba - Sule Lamido

Tsohon gwamnan Jigawa da ke arewacin Najeriya kuma jigo a jam'iyyar PDP Alhaji Sule Lamido ya yi wa tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai raddi kan tayin da ya yi wa ƴansiyasa su bi shi zuwa sabuwar jam'iyyarsa ta SDP.
A makon da ya gabata ne Malam Nasir El-Rufai ya sanar da sauya sheƙa daga jam'iyyarsa ta APC zuwa SDP.
A hirarsa ta musamman da BBC bayan ficewarsa APC, Malam Nasir El-Rufai duk da cewa bai ambaci sunan Sule Lamido ba amma ya yi kira ga Alhaji Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban ƙasa da Peter Obi da Rotimi Amaechi da Rauf Aregbesola da ma dukkan shugabannin adawa su bi shi zuwa sabuwar Jam'iyyarsa ta SDP.
Sai dai Alhaji Sule Lamido tsohon gwamnan jihar Jigawa ya yi kakkausan suka kan tayin na Malam Nasir El-Rufa'i inda yake nuna cewa ba shi da akidar siyasar ci gaba da kishin al'umma da har zai yi kira ga 'yan PDP su bi shi sabuwar jam'iyyarsa.
"Yanzu ba don raini ba, saboda Allah, ya zai kalle mu a PDP ya ce zai kira mu wata jam'iyyar siyasa. Jam'iyyar da muka yi ta PDP ita ce ta haife shi."
"Ya za a yi a ce jika ya ce kakansa bai san komi ba," in ji Sule Lamido.
A cikin martaninsa, Sule Lamido ya ce El-Rufai ya taɓa cewa babu manya a Najeriya a siyasa, su ne manya don saboda a lokacin yana gwamna. Su ne masu aiki da iko ta ko'ina.
"Amma ya wayi gari ya ce ya fadawa Buhari, Yanzu ai ba za ka kalle ni ka ce na bi umarnin Buhari ba, idan dai har haka ne bai kamata ya je wajen Buhari ba tun da ya ce su ne manya," in ji Sule Lamido.
Sule Lamido wanda ya ce ya taba sakataren jam'iyyar SDP, ya ce shi bai ga laifin jam'iyyarsa ta PDP ba a yanzu.
"Duk rikicin da PDP take ciki, a nan aka haife shi. Idan ya ce PDP ta mutu to a nan ne asalinsa, nan ne aka haife shi."
"Za a ce El-Rufai ministan PDP ne, duk bin da ka mallaka duniya PDP ce," a cewar Sule Lamido
"Ba a iya kada Tinubu cikin fushi"
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sule Lamido ya ce idan da har zai bar PDP da tun lokacin da aka kafa hadakar da ta haifar da APC ya fice daga jam'iyyar.
"Idan ban je APC a 2014 ba da aka gayyace ni, su sun tafi cikin fushi, PDP ta yi laifi, a yanzu kuma me APC ta yi musu?
Ya ce ana magana ne kan APC ta gaza, kuma dama tun farko yana cikin masu sukar cewa ba ta iya ba.
Ya ce shugabanci ba a yinsa a cikin fushi ko haushi ko wani buri na son zuciya.
A cewarsa ana shugabanci ne cikin hakuri da hangen nesa da yin abu domin neman zaman lafiyar mabiya da kuma kasa bakidaya.
"Idan ka ce za ka yi amfani da fushinka don biyan wata bukata, ba za ka taba hukunci kan kasa ba sai don son ranka.
"Idan dai ana son kawar da Tinubu, to babu maganar fushi."
"Ba za a yaƙe shi ba kan ko don ya ɓata min rai, ko don ina jin haushinsa ko don ramuwa, don ya san maganin fushi," in ji Sule Lamido.
A cewarsa "abin da ya kamata a yi shi ne a sa kishin kasa a gaba, maimakon nuna fushi da wani"
"A yi tafiyar a matsayin nuna kasa a idon duniya ba ta tafiya daidai, sannan mulkin da ake yi a Najeriya ba a kyautawa haƙƙin dan'adam da zaman lafiyarsa ba a yin daidai."
"Sai a kira a zo a gyara wadannan abubuwan."











