Buhari ya yi ƙoƙarinsa amma ya bar baya da ƙura - Baba Ahmed

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Lokacin karatu: Minti 3

Ɗaya daga cikin jami'an ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya, Hakeem Baba-Ahmed ya ce duk da cewa kowa ya amince cewa marigayi Muhammadu Buhari mutum ne mai gaskiya amma yana da nasa kura-kuran ta fuskar jagoranci.

Kamar kowane shugaba da ya bar mulki, masu lura da al'amura da ma ɗaiɗaikun 'yan Najeriya na ci gaba da waiwaye kan salon mulkin da marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya gudanar.

Buhari ne mutum na farko da ya doke shugaban ƙasa mai-ci a Najeriya bayan samun nasara kan Goodluck Jonathan na PDP a zaɓen 2015 ƙarƙashin jam'iyyar APC, kuma ya yi wa'adi biyu har zuwa 2023.

Ɗaya daga cikin abubuwan da 'yan'adawa suka dinga siffanta salon mulkinsa shi ne "baba go slow" wato shugaba mai yin abubuwa sannu a hankali.

Sai dai Buhari ya taɓa mayar musu da martani da cewa: "To su da suka yi saurin ina suka je?"

Magance matsalar tsaro na kan gaba-gaba cikin alƙawuran da Buharin ya yi kafin zaɓe, amma tana cikin abubuwan da wasu ke sukar sa da cewa ba ta magantu ba.

"Allah ya yi masa rahama ƙila ba haka ya yi niyya ba, amma dai haka aka ƙare shekara takwas din nan ana wayyo wayyo," a cewar Hakeem Baba Ahmed, ɗaya daga cikin jami'an ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya.

APC da magoya bayanta na cewa gwamnatin Buhari ce ta karya lagon ƙungiyar Boko Haram ta hanyar dawo da ikon wasu ƙananan hukumomi ƙarƙashin gwamnati Najeriya bayan ƙungiyar ta ƙwace su a jihar Borno.

Sai dai Hakeem ya nuna cewa gwamnatin ta Buhari ta gaza wajen magance wasu matsalolin na tsaro.

"Ya yi maganin 'yan Boko Haram ɗin nan cikin wata uku, amma da ya kai su Borno da Yobe sai ya bar su a can ya dawo, ba su rabu da mu ba," in ji shi.

Buhari ya yi takarar shugaban ƙasa karo biyar a tarihi kuma sai a na huɗu ya yi nasara, wadda ta biyo bayan dunƙulewar jam'iyyun adawar da suka kafa APC a 2014.

'Dalilin da ya sa muke sukar Buhari a yanzu'

Muƙarraban gwamnatin Buhari

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Marigayi Shugaba Buhari kenan lokacin da yake saka hannu kan kasafin kuɗin 2023 ranar 3 ga watan Janairun shekarar
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Daga cikin nasarorin da gwamnatin Buhari take alfahari da su akwai yaƙi da Boko Haram, da bunƙasa noma, da ayyukan gina layukan dogo.

Sauran sun ƙunshi daƙile almundahana a ma'aikatun gwamnati ta hanyar fito da tsarin asusun bai-ɗaya na TSA, da shirin rage talauci na N-Power, da kafa sabuwar dokar man fetur ta PIA.

"Lokacin da Buhari ya sake dawowa ya nemi a zaɓe shi karo na biyu, wasu daga cikinmu mun ce kada a zaɓe shi. Dalili shi ne mun ce ba mu ga alamun sauyi ba na wahalhalun da aka sha," kamar yadda Hakeem ya bayyana.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne Buhari ya miƙa wa Bola Tinubu mulki, wanda shi ne karo na uku a tarihin Najeriya da shugaban farar hula ya miƙa wa na farar hula mulki.

"Lokacin da Tinubu ya fara mulki 'yan Najeriya na cikin wahala. Shi ya sa wasu daga cikin gwamnatin ta Tinubu ke ce wa 'yan Najeriya ba su ne suka haifar da matsalolin da ake ciki ba."

Hakeem ya ce suna fito da gazawar gwamnatin Buhari ne a yanzu kawai saboda a koyi darasi.

A cewar Hakeem: "Duk wanda ya yi shugabanci dole ne a yi magana a kansa, Idan Buhari ya yi daidai dole ne tarihi ya auna shi a inda ya yi ƙoƙari da inda ya gaza, saboda ko ba mu faɗa ba dole wasu za su faɗa. Muna so a faɗa ne domin 'yan gaba su ji kuma su gyara, ba wai don ba mu son sa ba.

"Irin mutanen da ya bai wa muƙamai, da kuma salon mulkinsa na bai wa mutum abu ba tare da saka ido ba, waɗannan ne suka taru suka zamar masa matsala."

Amma ko da me zai dinga tuna mulkin Buharin?

"Zan dinga tuna shi a matsayin bawan Allahn da yake da niyya mai kyau sai dai Allah bai ba shi iko ya aikata niyyar nan ba. Ya so ya gyara Najeriya amma bai yi nasara ba."