Da gaske ƴansiyasar Arewa sun zama marayu bayan rasuwar Buhari?

Asalin hoton, X/Barau Jibrin
Kusan kowa ya amince cewa rashin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a siyasar Najeriya ba ƙaramin rashi ba ne, abin da ya sa wasu ke ganin 'yansiyasa daga arewacin ƙasar sun zama marayu.
Buhari ya shafe shekara 50 ana damawa da shi a harkokin mulkin Najeriya - tun daga watan Janairun 1983 da ya zama shugaban mulkin soja a karon farko.
Masana harkokin siyasa sun yi ta nazari kan ɗansiyasar da zai iya maye gurbin farin jini, da kima, da ƙuri'un da Buhari ya saba samu duk lokacin da ya tsaya takara hatta a lotukan da bai yi nasara ba.
Ganin cewa shi ne shugaban ƙasa na farko a jam'iyyar APC mai mulki, wasu na ganin kamar rashinsa zai jefa 'yan jam'iyyar cikin rashin uba a arewacin ƙasar.
Magoya bayan Buhari kan yi alfahari da cewa yakan samu ƙuri'a kusan miliyan 12 da yake samu duk lokacin da ya shiga zaɓe, baya ga yadda 'yansiyasa da yawa suka shiga alfarmar farin jininsa domin cin zaɓe a jam'iyyun APP, da CPC, da kuma APC.
Ƙwararren ɗanjarida Mannir Ɗan Ali ya ce rasuwar Buhari za ta haifar da sabon yanayin siyasa a arewacin Najeriya na kowa tsaya da ƙafarsa.
"Zamanin yin 'sak' ya wuce, duk wani ɗan siyasa da ke son tsayawa takara a nan gaba to sai ya tsaya da ƙafarsa, sannan kuma sai ya nuna abin da zai iya yi wa jama'arsa kafin su zaɓe shi." In ji shi.
Shi ma Gimba Kakanda, mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan bincike da alƙaluma a ofishin mataimakin shugaban ƙasar, ya yi imanin cewa rasuwar Buhari za ta haifar da sabon tsarin siyasa a arewacin Najeriya.
'Maganar adawa ce kawai'

Asalin hoton, @barauijibrin
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ranar Alhamis ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadarsa domin girmamawa da kuma bankwana da marigayi Muhammadu Buhari.
Yusuf Buhari na ɗaya daga cikin waɗanda suka wakilci iyalan tsohon shugaban ƙasar yayin taron, inda ya gabatar da jawabi.
Bayan taron ne kuma BBC ta zanta da mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin, ɗan APC wanda ya fito daga jihar Kano da ke jihar Kano a arewacin ƙasar game da batun ko da gaske sun zama marayu.
Ya yi fatali da hasashen yana mai cewa Shugaba Bola Tinubu ne ubansu a yanzu.
''Ba haka ba ne, muna da babban shugaba, shugaba Bola Tinubu," in ji shi. Ko lokacin da Allah ya sa Buhari ya zama shugaba ai tare suka yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Tinubu."
A cewar Barau Jibrin, ƙaddara ce ma ta sa Buhari ya riga Tinubu zama shugaban ƙasa a APC.
"Bola Tinubu ne ya zauna ya ƙirƙiro maganar kafa jam'iyyar APC, kuma ƙaddara ce ta sa Buhari ne zai fara shugabancin.
''Shugaban ƙasa na yanzu shi ya tsara komai, jam'iyyu huɗu suka dunƙule, da ACN da ANPP da CPC da kuma New PDP. Idan aka ce babu shugaba, wannan zance ne na adawa kuma babu gaskiya a cikinsa."














