Shugabannin Najeriya da suka rasu da dalilan mutuwarsu

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 7
Rasuwar tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ka iya tuna wa al'ummar ƙasar abubuwa da dama, kuma ƙila babba daga ciki shi ne rasuwar wasu shugabannin na baya da kuma halin da waɗanda ke raye suke ciki.
Najeriya ta yi shugabannin ƙasa 16 tun daga 1960 lokacin da ta samu ƴancin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.
Sai dai an yi ta samun sauyi tsakanin shugabannin, inda wasu na soja ne wasu kuma na farar hula. Wasu kuma sun yi mulki a duka ɓangarorin biyu.
Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari, su ne suka shugabanci Najeriya da kakin soja da kuma tafarkin dimokuraɗiyya.
Wannan maƙala ta yi duba kan shugabannin Najeriya da ke raye zuwa yanzu, da kuma waɗanda suka mutu.
Najeriya ta samu shugabanni biyar waɗanda suka rasu a kan mulki. Uku daga cikin su sun mutu ne sanadiyyar juyin mulki, ɗaya ya rasu sanadiyyar rashin lafiya sai kuma ɗaya wanda har yanzu babu tabbas kan sanadiyyar rasuwar tasa.
Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa

Asalin hoton, Getty Images
Abubakar Tafawa Balewa, shi ne firaiministan farko na jamhuriyar Najeriya daga ranar 1 ga watan Oktoban 1960 zuwa 15 Janairun 1966 lokacin da aka halaka shi, a lokacin juyin mulki na farko da sojoji suka yi.
Sojoji masu juyin mulki sun kashe shi tare da firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardauna da kuma wasu fitattun ƴan arewacin ƙasar.
Sai bayan kwana shida aka tsinci gawar Tafawa Balewa a wani wuri kusa da birnin Legas.
An haifi Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa a watan Disamba 1912 kuma ya rasu yana shekara 55.
Janar Johnson Aguiyi-Ironsi

Asalin hoton, Getty Images
Janar Johnson Aguiyi-Ironsi ya yi mulkin Najeriya daga 16 ga watan Janairu 1966 zuwa 29 ga Yulin 1966.
Shi ne shugaban mulkin soja na farko bayan juyin mulki na farko da ƙasar ta fuskanta.
An haife shi a garin Umuahia na jihar Abiya ranar 3 ga watan Maris na 1924, kuma ya rasu ranar 29 ga watan Yulin 1966.
Sojojin da suka yi masa juyin mulki ne suka kashe shi, a wani mataki da ake wa kallon ramuwar gayyar juyin mulki na farko a Najeriya.
Janar Murtala Muhammed

Asalin hoton, Getty Images
Mulkin Janar Murtala Muhammed na soja ya fara ne daga ranar 29 ga watan Yulin 1975 zuwa 13 ga watan Fabrairun 1976, inda ya hau mulki bayan juyin mulkin da aka yi wa Janar Yakubu Gowon.
Ɗan asalin jihar Kano ne da ke arewa maso yammacin ƙasar, wanda aka haifa ranar 8 ga watan Nuwamban 1938.
Ya rasu ranar 13 ga Fabrairun 1976 a lokacin da sojoji masu juyin mulki suka buɗe masa wuta.
An kashe shi ne a cikin motarsa yana da shekara 37 tare da babban mai tsaron sa Laftanar Akintunde Akinsehinwa da kuma direbansa Sgt Adamu Michika.
Janar Sani Abacha

Asalin hoton, Getty Images
Janar Sani Abacha ya yi mulkin soja tsawon shekara takwas daga 17 ga Nuwamban 1993 zuwa 8 ga watan Yunin 1998.
Shi ma ɗan jihar Kano ne da aka haifa ranar 20 ga watan Satumba na 1944, sannan ya rasu ranar 8 ga watan Yunin 1998 yana kan ganiyar mulki.
Duk da cewa babu cikakken tabbas kan sanadiyyar rasuwar tasa, an fi alaƙanta lamarin da bugun zuciya.
A cikin wata hira da ya yi da BBC a cikin shekara ta 2025, babban dogarinsa Manjo Hamza Almustapha ya ce "Abacha da Abiola sun yi mutuwa iri ɗaya".
An binne shi a ranar da ya rasu a gidansa da ke birnin Kano.
Umaru Musa Yar'Adua

Asalin hoton, Getty Images
Umaru Musa Yar'Adua na cikin shugabannin da suka mutu a kan mulki, wanda ɗan asalin jihar Katsina ne da ke arewacin Najeriya.
Ya fara mulki a matsayin zaɓaɓɓen shugaba daga ranar 29 ga watan Mayun 2007 zuwa 5 ga watan Mayun 2010.
An haife shi a shekarar 1951, kuma ya rasu a ranar 5 ga watan Mayu na shekarar 2010.
Ƴar'adua ya rasu ne a fadar shugaban Najeriya da ke Abuja bayan doguwar jinya.
Tsohon shugaban wanda ya rayu shekara 58 a duniya ya yi fama ne da matsanancin ciwon ƙoda na aƙalla shekara 10.
A cikin shekara uku na ƙarshen rayuwarsa an garzaya da shi asibiti a Jamus sau biyu, sannan ya riƙa zuwa Saudiyya neman magani.
A watan Nuwamban 2009 ya yi jinyar wata uku a wani asibiti da ke birnin Jeddah na Saudiyya ba tare da ya miƙa ragama ga mataimakinsa ba, wani abu da ya haifar da ruɗani a ƙasar.
Shugabannin da suka rasu bayan sauka daga mulki
Shugabanni Najeriya hudu ne suka rasu bayan sauka daga mulki kuma akasarin su sun rasu ne sanadiyyar jinya.
Nnamdi Azikiwe

Asalin hoton, Getty Images
Nnamdi Azikiwe ya mulki Najeriya daga ranar 1 ga watan Oktoban 1963 zuwa 16 ga watan Janairun 1966.
Shi ne shugaban ƙasar Najeriya na farko, kuma ɗaya daga cikin 'yan gwagwarmayar neman 'yancin kan ƙasar.
An haife shi ranar 16 ga watan Nuwamban 1904 a garin Zungeru da ke cikin jihar Neja a yanzu.
Ya rasu ranar 11 ga watan Mayun 1996. Ya rasu ne a Asibitin koyarwa na jami'ar Najeriya da ke Enugu bayan doguwar jinya yana da shekara 91 a duniya.
Gwamnati mai ci a lokacin, ta Janar Sani Abacha ta yi masa jana'iza ta ban-girma, inda a ƙarshe aka binne shi a garin Onitsa ranar 16 ga watan Nuwamban 1996.
Shehu Shagari

Asalin hoton, Getty Images
Shehu Shagari, shi ne shugaban farar hula na farko wanda kuma ya kafa Jamhuriya ta biyu bayan juyin mulkin farko da aka yi.
Mulkinsa ya fara ne daga 1 ga watan Oktoba na 1979 zuwa 31 ga watan Disamban 1983.
An haife shi ranar 25 ga watan Fabrairun 1925 kuma marigayin ya rasu ne a ranar Juma'a 28 ga watan Disamban 2018 a asibitin kasa da ke Abuja inda ya yi jinya.
Bayanai sun ce Shehu Shagari ya yi fama ne da ciwon Limoniya kuma an garzaya da shi asibiti bayan da jikinsa ya yi zafi.
Sojoji ne suka tuntsurar da gwamnatin Shagari a shekara ta 1983 jim kaɗan bayan fara wa'adin mulkinsa na biyu.
Alhaji Shehu Shagari yana cikin 'yan siyasar jamhuriya ta farko, da suka yi ministoci a gwamnatin Tafawa Balewa tsakanin 1960 zuwa 1966 da sojoji suka yi wa gwamnatin juyin mulki.
Ernest Shonekan

Asalin hoton, Getty Images
Cif Ernest Shonekan ya mulki Najeriya daga 26 ga watan Agustan 1993 zuwa 17 ga Nuwamban 1993 a matsayin shugaban riƙon ƙwarya.
Janar Ibrahim Badamasi Babangida ne ya miƙa masa mulki sanadiyyar matsin lamba da ya riƙa sha bayan soke zaɓen da aka yi na 12 ga watan Yunin 1993.
Ya kwashe wata uku ne kacal a matsayin shugaban Najeriya kafin sojoji suka yi masa juyin mulki, inda Janar Sani Abacha ya zama shugaban ƙasa.
An haife shi a jihar Legas ranar 9 ga watan Mayun 1936 kuma ya rasu 11 ga Janairun 2022.
Bayanai sun ce tsohon shugaban na Najeriya ya kwashe kimanin wata biyu a asibiti kafin rasuwar tasa.
A cikin sanarwar da iyalansa suka fitar sun ce "ya rasu ne kawai bayan kwana sun ƙare yana da shekara 85."
(Janar) Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images
Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ɗaya ne cikin biyu da suka yi mulkin soja da na dimokuraɗiyya.
Ya hau mulkin farko a matsayin soja daga watan Janairun 1983 har zuwa Agustan 1985. Sai kuma aka zaɓe shi a 2015, inda ya yi wa'adin shekara huɗu sau biyu kuma ya sauka ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Rashin lafiya ta tsananta ga Buhari ne ba da jimawa ba bayan kama mulki a wa'adinsa na farko a matsayin shugaban ƙasa farar hula.
A tsawon mulkinsa na shekara takwas ya kwashe lokaci a karo daban-daban yana jinya a Birtaniya.
Bayan saukar sa daga mulki ya koma garin haihuwarsa Daura da zama na kimanin kusan shekara biyu, inda daga baya ya koma gidansa na Kaduna a farkon shekara ta 2025.
Mutane da dama sun soki gwamnatinsa saboda gazawa wajen bayyana wa al'umma rashin lafiyar da ke damun sa.
Shugabannin da ke raye
Mutum biyar ne suka mulki Najeriya tun bayan shiga Jamhuriya ta Huɗu daga 1999 zuwa yanzu.
Daga cikinsu, Olusegun Obasanjo, da Goodluck Jonathan, da Bola Tinubu ne ke raye a halin yanzu, yayin da Umaru Musa Yar'Adua, da Muhammadu Buhari suka rasu.
A gefe guda kuma, akwai Janar Yakubu Gowon da Janar Ibrahim Babangida da Janar Abdulsalami Abubakar, waɗanda ke raye.
Lokuta da kuma tsawon mulkinsu:
- Yakubu Gowon - 1966 zuwa 1975
- Janar Ibrahim Babangida - 1985 zuwa 1993
- Janar Abdulsalami Abubakar - 1998 zuwa1999
- Olusegun Obasanjo - 1999 zuwa 2007
- Goodluck Jonathan - 2010 zuwa 2015
- Bola Tinubu - 2023 zuwa yanzu











