Abacha da Abiola sun yi mutuwa iri ɗaya - Almustapha
Yayin da ake gudanar da bukukuwan ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar Dimokraɗiyya ta Najeriya, tsohon dogari ga tsohon shugaban ƙasa, Janar Sani Abacha ya ce akwai abubuwa masu yawa dangane da al'amarin wannan rana da zai tattauna a kansu nan gaba.
Sai dai kuma ya ɓara kan zargin da ake yi wa tsohon maigidan nasa dangane da rushe zaɓen ranar 12 ga watan Yunin 1993.
Toson shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida a littafin tarihinsa da ya rubuta, ya yi da-na-sanin rushe zaɓen inda ya ɗora laifin kan Janar Sani Abacha.
Ga wasu abubuwa da Manjo Hamza Al-Mustapha ya shaida wa BBC dangane da ranar ta 12 ga watan Yuni da ma sauran batutuwa da suka shafi dimokraɗiyya.
Zargin Abacha da rusa zaɓen 12 ga Yuni

Asalin hoton, Getty Images
Da aka tambayi Manjo Hamza Almustapha dangane da abin da zai ce kan zargin da tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida ya yi a littafinsa da ya rubuta, sai ya ce:
"...Lokacin da aka ƙaddamar da littafin ba a gayyace ni ba. Kuma ban karanta ba saboda haka ba na son cewa komai a kan maganar. Sai nan gaba.
Shi batun 12 ga watan Yuni ta fi ƙarfin duk yadda jama'a ke tunanin al'amarin saboda abin da ya faru jama'a ba su sani ba. Ni kuma ba yanzu zan faɗi abin da ya faru ba" In ji Almustapha.
Mene ne ya yi ajalin Abacha?

Asalin hoton, Getty Images
An tambayi Manjo Hamza Almustapha dangane da haƙiƙanin yadda tsohon mai gidan nasa ya rasu, sai ya ce
"Wannan wata magana ce babba da na yi ta a Okputa Panel. Yadda Abiola ya mutu haka ma Janar Abacha wato zuciyarsu ta kumbura fiye da yadda ake tunani."
Kuɗaɗen da ake zargin Abacha da sacewa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tsohon dogarin marigayi shugaban Najeriya na soji, Manjo Hamza Al-Mustapha, ya musanta cewa Abacha ya kwashi kuɗaɗen Najeriya zuwa kasashen waje.
"A wannan lokacin akwai abubuwa da dama domin ana yin mulki ne cikin uƙuba da wahala babu ma kuɗin. To sai muka je Libya tare da waɗansu mutane da dama domin mu ga yadda suke gudanar da abubuwansu saboda Libya ta daɗe da takunkumai da yawa. Ta shekara 11 da takunkumai.
Ɗaya daga cikin abubuwan da aka kwaikwayo shi ne a samu kamfanoni na ƴan ƙasa gwamnati ta ba su jari su je suna sayo kaya suna sayarwa jama'a da araha kamar yadda yake a Libya. Waɗannan abubuwan muka kwaikwayo kuma Allah da ikonsa ƴan Najeriya ba su tagayyara ba.
Amma na san bayan ya mutu waɗansu mutanen maimakon su dawo da kuɗaɗen abu da yawa ya faru. An ɗora masa ƙarerayi da yawa. Ba na jin kuɗaɗen da ake cewa an dawo da su gida da sunan Abacha ne.
Asusun ƴan ƙasa da yawa aka zuba kuɗaɗen a cikin domin yin waccan harka ta saye da sayarwa domin a taimaki Najeriya a tabbatar abubuwa sun yi araha. Wasu sun dawo da su wasu kuma sun yi ruf-da-ciki.
Kuma abin da ya kamata a tambaya shi ne shin Abacha ya taɓa fita ƙasar waje? Shin kuɗaɗen da ake dawo da su akwai sa-hannunsa a kai. Ko kuma akwai kuɗin da aka gani aka ce da sunan Abacha ne? Babu". In ji Manjo Almustapha.
'Ra'ayina kan mulkin dimokraɗiyya a Najeriya'

Manjo Hamza Almustapha ya ce dimokraɗiyyar Najeriya ta samu ci gaba saboda kwashe shekaru 26 ana yin dimokraɗiyyar.
Sai dai kuma ya ce dangane da yanayin rayuwar ƴan Najeriya ba a samu wani cigaba ba bisa la'akari da matsalolin tsaro da talauci da ƙuncin rayuwa da aka jefa ƴan ƙasar.
"Samun dimokraɗiyya abu ne na ci gaba amma kuma muzanta wa ƴan ƙasa da mulki maras ma'ana da amfani da dimokraɗiyyar ta hanyar da ba ta dace ba wannan ba ƙaramin cibaya ba ne." In ji Almustapha.
Ko Almustapha zai yi takara?
Sai Manjo Hamza Almustapha ya ce "Insha Allahu. A baya gwaji na yi amma yanzu da gaske zan nema. Shi ya sa ma muka tattauna da ƙasashen waje da cewa su saka ido a Najeriya musamman dangane da abin da ya shafi zaɓe. Saboda rubuta sakamakon zaɓe ake yi."
Ko Almustapha zai shiga haɗakar ƴan hamayya?
"Ni wannan ba ruwana da haɗaka saboda akwai abin da na gani ya saɓa da aƙidu irin namu. Idan aƙida ta saɓa irin tamu to ba na so na zo a yi abin kunya a ƙasa da zai zubar mana da ƙima saboda da hannuna a ciki.
Masu cewa jam'iyyar APC na amfani da irinmu wajen hana su shiga haɗaka, wallahi ban ga mutumin da zai sa ni yin abin da zai cuci ƙasa ba. Sannan babu wasu kuɗi masu yawa da za su sa na yi abun da zai cuci ƴan Najeriya." In ji Hamza Almustapha.
Da kuma aka tambaye shi ko idan hali ya yi zai iya janye wa Atiku Abubakar takarar shugabancin ƙasa, sai ya ce " ai ba ma na jin tafiya za ta haɗa mu saboda haka babu dalilin tambayar."












