Mece ce makomar PDP bayan ficewar Atiku?

Asalin hoton, Getty Images
Masana da masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin ficewar tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar daga jam'iyyar adawa ta PDP zai iya shafar tagomashinta a zaɓuka masu zuwa.
A ranar Laraba ne Atiku ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar da ya yi wa takarar shugaban ƙasa sau biyu, yana mai cewa saboda da yadda ta "sauka daga kan manufar kafa ta".
Sai dai PDP wadda ita ce babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, ta mayar da martani, inda ta haƙiƙance cewa ficewarsa ba za ta haifarmata da wani giɓi ba.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoton tsohon mataimakin shugaban ƙasar bai bayyana jam'iyar da zai koma ba, amma ya ɗauki matakin ne ya shiga yunƙurin 'yan'adawa na dunƙulewa a inuwar jam'iyyar ADC domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu na APC a babban zaɓe na 2027.
Wannan ne karo na uku da Atiku ke barin PDP tun bayan shigarsa a 1998 - lokacin da ya lashe zaɓen gwamnan jihar Adamawa, inda daga baya ya zama abokin takarar shugaban ƙasa na Olusegun Obasanjo a jam'iyyar.
Babu wani giɓi
Mataimakin sakataren yaɗa labarai na na PDP na ƙasa, Ibrahim Abdullahi, ya yi iƙirarin cewa Atiku na ɗaya daga cikin waɗanda ke haddasa fitina a cikin jam'iyyar.
''Ba yau ba ne karo na farko da ya fita, ba zai yiwu jam'iyya ta kasance kamar domin mutum guda aka yi ta ba," kamar yadda ya faɗa wa BBC.
'Ɗaya daga cikin abubuwan da ake ƙorafi a Najeriya shi ne jam'iyyar PDP ta kasance kamar wata ƴa ce ga Atiku Abubakar wadda yake amfani da ita a duk lokacin da yake so'', In ji shi.
Malam Abdallahi ya ce ficewar Atiku ficewar Atiku ba ta dame su ba duk da cewa shi ne ya zo na biyu a takarar shugaban ƙasa da ya yi wa jam'iyyar sau biyu.
"Ko a jikinmu, PDP ba ta damu da wannan ba saboda an yi tsohon shugaban ƙasar da ya yaga katinsa na PDP kuma ya fita amma sai ga shi ya dawo.
''Za ka ga cewa ƴaƴan jam'iyyar musamman waɗanda suka more jam'iyyar su ne suke yi wa mata zagon ƙasa,'' in ji shi.
Lokuta uku da Atiku ya bar PDP

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Atiku Abubakar ya shafe kusan shekara 40 a fagen siyasar Najeriya, inda ya fara neman takarar shugaban ƙasa tun daga shekarar 1993 a jam'iyar SDP.
Ya yi takarar gwamnan jihar Adamawa a shekarar 1990, ya sake yi a 1996 duka ba tare da nasara ba, inda daga baya ya samu nasara a 1998.
Sai dai kafin a rantsar da shi ne kuma tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya zaɓe shi a matsayin abokin takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP a 1999.
1. Bayan kammala wa'adi biyu a matsayin mataimakin shugaban ƙasa, Atiku ya so ya yi takara a PDP, amma da al'amura suka gagara ya koma jam'iyyar Action Congress (AC) kuma ya yi mata takarar shugaban ƙasa a 2007.
Ya sake komawa PDP tare da ƙalubalantar shugaba mai-ci a lokacin Goodluck Jonathan wajen neman tikitin takara, amma bai yi nasara ba.
2. Kafin zaɓen 2015, Atiku ya sake tsallakwa zuwa jam'iyyar haɗaka ta APC bayan jam'iyyun CPC da ANPP da ACN sun dunƙule. A nan ma ya shiga zaɓen fitar da gwani ba tare da yin nasara ba.
Ya koma PDP a 2017 tare da yin nasarar samun tikitin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2019, sannan ya sake yi mata takarar a 2023.
3. Yanzu da ya sake ficewa daga PDP, ana sa ran zai koma jam'iyyar haɗaka ta Africa Democratic Congress (ADC), wadda ya shiga gaba-gaba wajen ƙullawa.
'Ba laifi ba ne'
Wannan mataki da tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya ya ɗauka, masana siyasa na ganin matsalar da jam'iyyar PDP ta daɗe tana fama da ita, ita ce ta jawo ficewarsa.
Dakta Yakubu Haruna Ja'e malami ne a Jamiar Jihar Kaduna, kuma ya ce wannan ba shi ne karo na farko da ake samun wani jigo da ya fice daga jam'iyyarsa ba.
''idan ka duba marigayi Muhamadu Buhari shi ma ya yi takara a jam'iyyar ANPP, ya koma CPC, ya dawo APC kuma a haka ya ci zaɓe''.
''Idan aka koma shi ma Atikun ya yi yawo a jam'iyyu abinda ya nema ya ga cewa ba zai samu ba, babu laifi a siyasa ya fita ya je inda ya ga za a ba shi takara yadda yake buƙata,'' in ji shi.
Tun dai bayan sanar da dunƙulewar da Atiku da wasu ƴan siyasa suka yi a ƙarƙashin jam'iyyar ADC, jam'iyyar hamayya ta PDP ta nuna cewa ba ta lamunta da tsarin ba, kasancewar Atikun bai sanar da ficewarsa daga jam'iyyar a hukumance ba.











