Me ya rage wa jam'iyyun adawa a Najeriya?

Asalin hoton, Facebook/Atiku Abubakar/Peter Obi/Nasir El-Rufai
A ranar Laraba ne wasu manyan ƴan jam'iyyun adawa a Najeriya suka fice daga jam'iyyunsu kuma suka sauya sheƙa zuwa APC mai mulkin ƙasar.
Matakin da Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta da ke kudancin ƙasar ya ɗauka na ficewa daga PDP ya jefa jam'iyyar cikin ruɗani a jiharsa saboda yadda ya tafi da jiga-jigan ja'iyyar.
Bayanai sun ce gwamnan ya koma ne tare da manyan 'yan siyasa a jihar, ciki har da kwamishinoni, da 'yanmajalisa, da tsohon gwamnan jihar Ifeanyi Okowa, wanda ya yi wa PDP takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Sai kuma ɗanmajalisar dattawa daga jihar Kano da ke arewacin kasar, Sanata Abdurahman Kawu Sumaila, wanda ya fice daga NNPP kuma ya ce nan gaba akwai wasu ƴan NNPP ɗin da ke shirin ficewa zuwa APC.
A farkon shekarar nan an ga yadda wasu 'yanmajalisar tarayya suka fice daga jam'iyyar adawa ta Labour zuwa APC daga jihohin Kaduna, da Imo, da Cross River.
Tururuwa zuwa APC da 'yan'adawar ke yi na ƙara jefa manyan jam'iyyun da ke da ƙarfin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, inda tuni PDP da Labour da NNPP suke auka cikin rikicin shugabanci.
'Yansiyasar da ke sauya sheƙar kan bayyana dalilai daban-daban na komawa wata jam'iyya, amma masana sun sha bayyana cewa rashin alƙibla da kuma niyyar bauta wa masu zaɓe ne ke jawo sauye-sauyen jam'iyya a siyasar Najeriya.
Tawagar gwamnan Delta ta ce sai ranar Litinin za fita daga PDP a hukumance.
APC na farin ciki da bugun ƙirjin cewa ayyukan da take yi masu kyau ne ke ci gaba da janyo yan'adawa cikinta.
Abin da ya kamata jam'iyyun adawa su yi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk da cewa sauye-saueyen jam'iyya ba sabon abu ba ne a siyasar Najeriya, ana kallon faruwar hakan a yanzu a matsayin mafi tasiri saboda yadda duka manyan jam'iyyun adawa ke cikin rikici.
Farfesa Abubakar Kari masanin kimiyyar siyasa ne a Jami'ar Abuja kuma ya ce nan gaba idan ba a yi taka tsan-tsan ba Najeriya za ta iya komawa kasa mai jam'iyya ɗaya.
Sai dai PDP ta ce wannan mataki ba zai firgita su ba saboda masu sauya sheƙar "na sakin reshe ne suna kama ganye duba da yadda al'umma ke kokawa da irin salon mulkin gwamnatin APC".
"Wannan gagarumin koma-baya ne ga ga ɓangaren adawa, kuma koma-baya ne ga tsarin dimokuraɗiyya saboda hakan na ƙara wa jam'iyya mai mulki ƙarfi, kuma dimokraɗiyya ba ta ƙarko sai da jam'iyyun adawa masu ƙarfi," in ji Farfesa Kari.
Farfesa Kari ya ce shugaban ƙasa ya kamata a dinga yi wa irin wannan gangamin wajen yunƙurin ƙwace mulki, "amma saboda lalacewa da rashin haɗin kai na 'yan'adawa hakan ke faruwa".
Ko yaya 'yan'adawa za su shawo kan wannan matsalar?
Farfesa Kari ya ce: "'Yan'adawa su yi gagarumin yunƙuri domin ganin hakan bai ci gaba da faruwa ba, kuma su ma su fara zawarcin manyan 'yansiyasa daga APC ganin cewa ita ma jam'iyyar mai mulki tana fuskantar korafe-korafe da rashin gamsuwa da yadda abubuwa ke wakana."
Tuni tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya fara aikin zawarcin manyan 'yan'adawa a jam'iyyarsa ta SDP, wadda ya koma a watan Maris bayan ya bar APC.
Tsohon ɗantakarar shugabancin ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, ya tabbatar cewa yana tattaunawa da sauran 'yan'adawa domin yin haɗaka, amma PDP ta ce ba ta cikin tattaunawar.
"Ina da tabbas cewa ƴan Najeriya za su yi baƙin ciki idan har ba su da wani zaɓi sai jam'iyyar APC a zaɓen 2027," in ji Farfesa Kari.











