Me ya sa jam'iyyun hamayya a Najeriya suka kasa haɗewa don tunkarar 2027?

Asalin hoton, Social media
Har yanzu jam'iyyun hamayya a Najeriya na ci gaba da ƙiƙi-ƙaƙa kan kan yunƙurinsu na haɗewa waje guda domin tunkarar zaɓen 2027.
A baya-bayan nan an jiyo tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi na nesanta kansa daga duk wani yunƙurin da ake yi na haɗakar a yanzu, kodayake daga baya ya musanta hakan a wata sanarwa da ya fitar.
A watan Janairun da ya gabata ne, wasu jiga-jigan 'yan siyasar ƙasar suka yi wani taro a ofishin jam'iyyar SDP, wanda ake tunanin ba zai rasa nasaba da tattauna yadda za a yi haɗakar ba.
A baya ma an ga tsohon gwamnan jihar Mallam Nasir El-Rufai - wanda a yanzu yake adawa da gwamnatin Tinubu - a harabar jam'iyyar ta SDP, wani abu da wasu ke hasashen komawarsa jam'iyyar kodayake bai bayyana hakan ba.
Haɗakar jam'iyyun hamayya dai wani muhimmin mataki ne a yunƙurin adawa na wace mulki, musamman a ƙasa irin Najeriya, da jam'iyya mai mulki ke da ƙarfi.
Ko a shakarar 2015 ma, haɗewar jam'iyyun hamayyar ne suka kawar da jam'iyyar mai mulki a lokacin wato PDP.
To sai dai alama a wannan lokacin haɗewar na neman zame wa jam'iyyun hamayyar wani ƙalubale.
Fama da rikice-rikicen cikin gida
Jam'iyyun hamayyar na fama da rikice-rikicen cikin gida, lamarin da masana ke gani a matsayin wani abu da ke yi wa yunƙurin haɗewar tasu barazana.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Jam'iyyar PDP, wadda ita ce babbar jam'iyyar hamayya a ƙasar, a baya-bayan nan an ga yadda wasu jiga-jiganta suka riƙa musayar yawu.
Gwamnan jihar Bauchi - wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnanonin PDP, ya riƙa musayar kalamai na ministan birnin Abuja, kuma tsohon gwamnan jihar Rivers - wanda shi ma jigo ne a jam'iyyar.
Haka ma jam'iyyar LP ta Peter Obi, na fama da rikicin shugabancin jam'iyyar.
Yayin da jam'iyyar NNPP da Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi wa takara - ta tsinci kanta cikin rikicin shugabancin jam'iyyar na ƙasa, lamarin da ya yi tasiri a jihar Kano inda ke jam'iyyar ke da gwamna ɗaya tilo a ƙasar.
Wani abu da masana da masu sharhi ke kallo a matsayin sakin layi da jam'iyyu hamayarr suka yi.
Auwal Musa Rafsanjani, shugaban ƙungiyar SICLAC, kuma mai sharhi kan al'amuran siyasa ya ce jam'iyyun sun saki layi kan abin da ya kamata su yi a matsayinsu na 'yan adawa.
''Abin da ya kamata su yi shi ne idan gwamnati ta zo da wani ƙuduri musamman a majalisa sai su zauna su yi nazari, domin su ga alfanu hakan ko akasin haka''.
Rafsanjani ya ƙara da cewa a yanzu jam'iyyun ba sa mayar da hankali wajen kawo abin da ya shafi c gaban tattalin arziki ko yaƙi da cin hanci da rashawa, ko dawo da martabar ƙasar.
''Aikin shi ne su taimaka wajen ganin an inganta dimokraɗiyya da aikin gwamnati don tabbatar da nasarar dimokraɗiyya da inganta rayuwar al'umma'', in ji Rafsanjani.
'Idan aka tafi a haka ba inda za su je'
Masana da ƙungiyoyin farar hula na fargabar cewa matsarwa jam'iyyun suka kasa magance wannan matala to sun dab da rugujewa.
Dakta Kole Shettima na ƙungiyar MacAthur a Najeriya, kuma mai sharhi kan al'amuran siyasa a ƙasar ya ce jam'iyyun hamayyar sun zama tamkar ƙungiyoyi ne masu gasa a tsakaninsu, maimakon mayar da hankali wajen haɗewar.
''Jam'iyyun yanzu ba kamar na da ba ne, yawanci ƙungiyoyi ne da ake kafawa da nufin samun mulki, kowa ƙwalamarsa ita ce ya zama shugaban ƙasa ko ya riƙe kujera kaza'', in ji mai sharhin siyasar.
Kole Shettima ya ce wannan dalilin da ya sa jam'iyyun suka kasa zama wuri guda domin su yi abin da ya fi wa ƙasa alƙairi domin tunkarar jam'iyya mai mulki a babban zaɓen ƙasar da ke tafe nan da shekara biyu masu zuwa.
''Kowa yana yi ne don raɗin kansa, ba don al'umma ba, inda domin al'umma suke yi ai ba sai mutum ya zama shugaban jam'iyya ko shugaban ƙasa ba ko ya riƙe wani matsayi ba'', in ji shi
Masanin siyasar ya ce matsawar jam'iyyun hamayyar suka tafi a haka, to jam'iyyar APC ce za ta ci gaba da mulki, domin kuwa babu inda za su je a cewarsa.
A nasa ɓangare, shi kuwa Farfesa Tukur Abdulƙadir na jami'ar jihar Kaduna, cewa ya yi a halin da ake ciki jam'iyyun hamayyar ba su da ƙarfin da za su iya tunkarar jam'iyya mai mulki a zaɓen 2027.
''Idan ka duba jam'iyyar LP yadda take fama da rigimar shugabanci, har kotun ƙoli ta je, sanna jam'iyyar NNPP wadda jiha guda kawai take da rinjaye, don haka tasirinta ba shi da yawa a siyasance'', in ji shi.
Malamin jami'ar ya ce in dai aka tafi a haka, to akwai sauran rina a kaba dangane da haɗuwar jam'iyyar da za ta tunkari APC a 2027.
A wani ɓangaren jam'iyyun sun zargin APC mai mulki a ƙasar da yunƙurin haifar da rikice-rikice a cikinsu domin hana su sukunin da za su iya fuskantarta da ƙarfi har su ƙwace mulki.
A watan Disamban da ya gabata ne kakakin tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP, Paul Ibe, ya zargi jam'iyyar APC da haddasa rikici a jam'iyyarsu ta PDP mai adawa.
Me APC ke cewa?
Jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar ta ce musanta zargin, to sai ta ce jam'iyyun hamayyar ba za su su iya haɗewa wuri guda domin karɓe mulkin ƙasar a hannunta ba.
A wata hira da BBC a kwanakin baya babban daraktan yaɗa labarai na APC, Mallam Bala Ibrahim ya ce "PDP a matsayinta na babbar jam'iyyar adawa ba za daina zarginta ba kan ruɗanin shugabancin da take ciki har sai an sake dawowa lokacin zaɓe a 2027".
Kafin haka, Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume ya nemi ƴan siyasar arewacin ƙasar su jira har zuwa 2031, kafin su nemi takarar shugabancin ƙasar, lamarin da ya janyo cecekuce.










