APC ke da hannu a rikicin PDP - Aminu Wali

Jigo a jam'iyyar PDP, Aminu Bashir Wali
Lokacin karatu: Minti 3

Ɗaya daga cikin ƴan kwamitin amintattu kuma dattijo a babbar jam'iyyar hammaya ta Najeriya, PDP, Ambassada Aminu Wali, ya zargi jam'iyyar APC da ke mulki a Najeriya da cewa ita ke rura wutar da ta hana jam'iyyarsu zama lafiya, ake ta samun rikici a cikinta.

A hirarsa da BBC, Ambassada Wali wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka ƙirƙiro jam'iyyar ta PDP ya ce sun tabbata ba haka kawai jam'iyyar ta samu kanta a wannan hali ba da hannun APC ba. ''Ka tabbata cewa tilas APC suna da ruwa da tsaki a cikin rgingimun da ke faruwa a cikin wasu jam'iyyu a Najeriya.

''Kwanaki kwamitin zartarwar ba ta dare gida biyu ba sai daga baya aka zo aka yi musu faci da ƙyar suka gyaru,'' in ji shi.

Ya ce ba abu ne da daman zai fito fili ba cewa APC ta fito ta nuna cewa tana da hannu a rikicin ko kuma ta bayyana cewa ga abin da take yi.

Amma su suna da yaƙinin cewa ita ce take tayar da zaune tsaye a wasu jam'iyyun na hamayya domin, yana ganin ta hanyar rarraba kan ne ita APC take ganin za ta kankane siyasar ƙasar.

Ya ce APC tana haddasa rikicin ne da rabuwar kai a wasu jam'iyyun na hamayya ta hanyar amfani da wasu daga cikin shugabanni da 'yan jam'iyyun na hamayya.

Dattijon ya yi nuni da abubuwan da tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, a jam'iyyar tasu ta PDP, inda yake zarginsa da kasancewa ɗaya daga waɗanda APC take amfani da su a PDP tana dagula musu al'amura.

''Abin da Wike ya faɗa tun kafin zaɓe har aka zo zaɓe kowa ya sani ba wai a ɓoye yake ba, amma har yanzu ya ce shi yana cikin jam'iyya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

To a nan duk mai hankali ya san duk abin nan da waɗanda suke taka dokokin jam'iyya suka yi wurgi da jam'iyya to suna da wani ɗaurin gindi wanda ya wuce na jam'iyyarmu,'' in ji shi.

Aminu Wali ya ce kasancewar su dattijai a jam'iyyar ba abin da za su iya illa su bayar da shawara kuma suna bayarwa, amma ba dokar jam'iyya ba ta ba su ikon ɗaukar matakin hukuntawa ko ladabtar da waɗanda ke hana wa jam'iyyar ruwa gudu ba.

Ya ce kwamitin zartarwa ne na jam'iyyar yake da wannan iko kuma kasancewar shugabancin jam'iyyar na riƙo ne to yana da ƙa'ida - ''to ya kamata a koma a bi ƙa'idar nan,'' in ji shi.

Ya ce idan da an bi ƙa'idar nan yana ganin ƙila da duk waɗannan rikice-rikice da jam'iyyar ta PDP take fama da su da wataƙila ba su faru ba.

Ya ce an kafa kwamitoci daban-daban don daidaita al'amura a jam'iyyar to amma har yanzu kwamitocin ba su kawo wani abu ba kuma wasu ma ba su fara aiki ba - hasali ma a cikin gwamnoni wasu ba sa shiri, wasu gwamnonin ba sa shiri da 'yan kwamitin zartarwar.

Dattijon na PDP ya ce halin da jam'iyyar take ciki a yanzu ba wanda zai ce ga inda suka dosa, domin zai iya cewa babu shugabanci a jam'iyyar a yanzu. Amma ya ce ba ya son ya ɗora laifi a kan wani.

Wali ya ce yana ganin ya kamata a yi babban taron jam'iyyar a samu tartibin shugabanci, sannan kwamitin zartarwar ya shiga aikinsa gadan-gadan na hukunci da ladabtar da duk mai laifi, yana ganin daga nan ƙila jam'iyyar ta dawo hayyacinta.