Da gaske APC ce ke haɗa rikice-rikice a jam'iyyun adawar Najeriya?

PDP da APC
Lokacin karatu: Minti 4

Duk da cewa akwai sauran lokaci kafin babban zaɓen Najeriya a shekarar 2027, ana ci gaba da musayar yawu kan shirye-shiryen jam'iyyu na fuskantar zaɓen mai zuwa.

Jam'iyyun hamayya na zargin APC mai mulki a ƙasar da yunƙurin haifar da rikice-rikice a cikinsu domin hana su sukunin da za su iya fuskantarta da ƙarfi har su ƙwace mulki, lamarin da jam'iyyar mai mulki ta sha musantawa.

A shekarar 2023 ne dai Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi nasarar doke Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa, inda aka samu wasu gwamnonin PDP da ake zargin sun yi wa APC aiki.

Naɗa tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike wanda ɗan PDP ne, ya ƙara fito da zargin da wasu ke yi cewa APC na amfani da shi domin haifar da rikicin cikin gida, kamar yadda PDP take zargi.

PDP na fama da rikice-rikice masu yawan gaske, inda rikici tsakanin ɓangaren Atiku da na Wike ke kawo tsaiko kan gudanar da harkokin jam'iyyar, ciki har da gaza shirya babban taron ƙolin jam'iyyar.

Haka ita ma jam'iyyar NNPP ta zargi jam'iyyar mai mulki da hannu a rikice-rikicen jam'iyyun hamayya domin hana su kataɓus.

Taƙaddama tsakanin APC da PDP

A daren Talata ne kakakin tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP, Paul Ibe, ya zargi jam'iyyar APC da haddasa rikici a jam'iyyarsu ta PDP mai adawa.

Da ma masana harkokin siyasa sun daɗe suna kallon Nyesom Wike a matsayin ɗan aiken APC, saboda yadda yake riƙe da minista a gwamnatin Tinubu amma kuma yake kiran kansa ɗan PDP.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai babban daraktan yaɗa labarai na APC ya faɗa wa BBC cewa "PDP a matsayinta na babbar jam'iyyar adawa ba za daina zarginta ba kan ruɗanin shugabancin da take ciki har sai an sake dawowa lokacin zaɓe a 2027".

Kafin haka, Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume ya nemi ƴan siyasar arewacin ƙasar su jira har zuwa 2031 kafin su nemi takarar shugabancin ƙasar, lamarin da ya janyo cecekuce.

Mista Akume, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake hira da wani gidan talabijin a ƙasar, inda ya ce kamata ya yi a bar yankin kudancin Najeriya ya ƙarasa shekara takwas, kamar yadda ita ma arewa ta yi lokacin mulkin Shugaba Buhari.

Kalaman ba su yi wa Atiku Abubakar daɗi ba a matsayin wanda ya daɗe yana neman takara a PDP.

"Babu wata yarjejeniya da aka yi ko kuma wani tsari. Idan su a APC sun yi wannan tsari mu ba haka yake a wajenmu ba. Ya kamata su tsaya su mayar da hankali kan zaɓen da suka ƙwace," in ji Abdulrashid Shehu Uba, ɗaya daga cikin masu magana da yawun Atiku.

'Siyasar Najeriya na da ban mamaki'

A game da waɗannan zarge-zarge, BBC ta tuntuɓi Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami'ar Bayero ta Kano, wanda ya ce akwai ƙamshin gaskiya a zargin.

A cewarsa: "Ganin yadda abubuwa ke faruwa ba za a yi mamaki ba idan an ce jam'iyya mai mulki na da hannu a rikicin. Ko dai ba ita ƙirƙira ba, zai iya zama tana da hannu wajen rura rigingimun domin ganin ba su ƙare ba. Haka ake yi a siyasar Najeriya, inda kowace jam'iyya take ƙoƙarin rushe abokiyar hamayyarta ita kuma ta gina kanta."

Farfes Fagge ya ce ko a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi tsakanin Bola Tinubu da Atiku Abubakar, "Wike ya yi ƙoƙari domin tabbatar da jam'iyyarsa ta kafa gwamntin jiha, amma ya ƙi bayar da goyon baya wajen kafa ta tarayya".

Ya ƙara da cewa rigingimun suna yawa ne saboda yawancin jam'iyyun ba su da aƙida. "Kawai mutane suna shiga ne saboda biyan buƙata, idan buƙatar ba ta biya ba, su fice su kom wata. Ko kuma su zauna a ciki su mata ƙafar unguwa."

Sai dai farfesan ya ce ba yanzu aka fara hakan ba, domin a cewarsa, an yi a jamhuriyya ta ɗaya da ta biyu.

"Amma lamarin ya fi ƙamari a jamhuriya ta huɗu. Misali, manyan jam'iyyu su ne PDP da APP. Da PDP ta samu mulki, sai ta janye wasu jiga-jigan APP ta ba su ministoci, daga baya kuma suka narke a PDP."

A game da ko hakan na da illa ga dimokuraɗiyya, masanin siyasar ya ce rigingimun siyasa ne suka bai wa sojoji damar ƙwace mulki a jamhuriyya ta farko.

"Don haka wannan wata al'ada ce a siyasar Najeriya, amma a ƙarshe shi yake haifar da rigingimu na siyasa wanda yakan iya haifar da kashe-kashe da ƙone-ƙona, kuma a su ne suka jawo juyin mulki."

Sai dai a nasa ɓangaren, Farfesa Abubakar Mu'azu na Jami'ar Maiduguri kuma darakta a cibiyar diflomasiyya da cigaban ƙasa, cewa ya yi akwai mamaki jam'iyyun hamayya su riƙa cewa jam'iyya mai mulki ce ke haifar musu da rigima.

"Ai shi ma Wike an janye shi ne saboda ana ganin akwai abin da zai iya yi. Amma kuma akwai waɗanda za su fita daga jam'iyya mai mulkin su koma wasu jam'iyyun," in ji shi yana mai cewa su ma jam'iyyun adawar suna da damar janye wasu daga cikin masu mulki.

"Abin da yake gabansu shi ne mulki. Kamata ya yi jam'iyyun hamayya su tsara gidansu ta yadda za su ja hankalin masu zaɓe. Ai da ba APC ba ce take mulki, daga baya ne suka yi gyara, suka haɗe da wasu jam'iyyun, sannan suka kayar da PDP.

"Ya kamata su yi la'akari da cewa duk wanda yake kan mulki yana so ya ci gaba, ya rage nasu su san dabarar da za su yi domin ƙwace mulki."