Bankwana
Masu bibbiyarmu a wannan shafin da haka muke sallama da ku, sai kuma gobe da yardar Allah. Sunana Umaymah Sani Abdulmumin.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/07/2027
Haruna Kakangi da Ahmad Bawage da Umaymah Sani Abdulmumin
Masu bibbiyarmu a wannan shafin da haka muke sallama da ku, sai kuma gobe da yardar Allah. Sunana Umaymah Sani Abdulmumin.
Gwamnatin Togo ta kare amfanin da ta yi da karfi don tarwatsa masu zanga-zangar sauyin tsarin mulki da ya bai wa iyalan Gnassingbe damar ci gaba da mulkin da suka shafe tsawon shekaru hamsin sun yi.
Jama'a sun fusata bayan an kame masu sukar gwamnati.
Gilbert Bawara ministan harkokin al'umma ya shaidawa BBC cewa 'yan fafutuka daga ƙasashen ƙetare ne ke tayar da tarzoma a Togo don rusa gwamnati.
'Kungiyoyin kare hakkin 'yan Adam sun ce 'yansanda sun yi amfani da karfi, sun kuma zargi gwamnati da aiki da ƙungiyoyin masu dauke da makamai don kwantar da zanga-zangar.
Mista Netanyahu ya nemi mabiya addinin Druze da ke Isra'ila su guji tsallakawa cikin Siriya don kai taimako.
Ya ce yin hakan zai haifar da tarnaƙi ga harin da dakarun Isra'ila suke kai wa kungiyoyin da ke goyon-bayan gwamnatin Siriya.
Wakilin BBC ya ce a kwanaki biyu da suka gabata sojojin isra'ila sun kaddamar da hari ta sama kan dakarun tsaron Siriya da aka aika su kwantar da tarzoma a yankin da mabiya addinin Druze ke zaune.
A Sweida Mabiya addinin Druze akalla dari da hamsin ne ke zaune a Isra'ila, wadda ke kallon sabuwar gwamnatin Islama ta Siriya a matsayin barazana.

Asalin hoton, NIGERIA POLICE
Rundunar 'yansandan Najeriya ta soma zaman shari'a domin ladabtar da wasu manyan jami’anta kan laifuka daban-daban da ake zarginsu da aikatawa kamar rashin ɗa'a da saba dokokin gudanar da aiki.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce jami'anta da za su fuskanci shari;a su 151 daga rassa daba- daban na faɗin ƙasar.
A cikin wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi ya fitar, ya ce an soma zaman ne tun a ranar Litinin 14 ga watan Yuli, kuma za a kammala a ranar Juma’a 25 ga watan Yuli a shelkwatar 'yan sandan da ke babban birnin ƙasar Abuja.
Sanarwar ta kuma ce jami'an 'yan sanda da ake zargi da wasu laifuka da suka shafi rashin da'a da karya dokokin aiki, za su bayyana ne gaban kwamitin ladabtarwa na rundunar domin fuskantar shari'a.
Mai Magana da yawun rundunar ya ce kwamitin ladabtarwan wani ɓangare ne na rundunar da ke gudanar da bincike kan manyan jami'ai daga mukamin ASP zuwa sama.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kididdiga ta ƙasa, NBS ta ce an samu raguwar hauhawan farashi da maki 22.22 cikin 100 idan aka kwatanta da maki 22.97 cikin 100 a watan Mayun 2025.
Rahoton da ta fitar ya ce idan aka haɗe alkaluman bana sun yi ƙasa da maki 11.97 cikin 100 idan aka kwatanta da irin wannan lokaci a shekara ta 2024.
Hukumar ta ce ana iya ganin tasirin hakan a ɓangaren abinci da sauran kayan masarufi.
Tun bayan cire tallafin man fetur aka shiga cikin matsi na rayuwa da hauhawan farashin wanda ya je 'yan ƙasar cikin tasku.
Sai dai da wannan alkaluma idan aka cigaba da tafiya a haka babu mamaki nan gaba a samu sauki, in ji masana.
Gwamnatin Amurka ta ce ta tasa keyar wasu mutane biyar da ta bayyana a matsayin bakin haure masu aikata laifuka zuwa masarautar Eswatini da ke kudancin Afirka.
Mutanen biyar ‘yan ƙasar Laos ne da Vietnam da Yemen da Cuba da kuma Jamaica.
A wata sanarwa da ma'aikatar tsaron cikin gida ta fitar ta kafar sada zumunta ta ce ana tura su yankin ne da ke kudancin Afirka, saboda ƙasashensu na asali sun ki karɓar su.
An same su da laifuka daban-daban da suka haɗa da kisan kai da kuma lalata da ƙananan yara.
Hadi Siriki ya ce yawan mutanen da ke kwarara zuwa gaisuwa Daura daga sassa daban-daban na Najeriya da Ketare na nuna irin mutum da rayuwar da Muhammadu Buhari ya yi.
Ya ce mutum ne mai son jama'a da barkwanci, sanna makusanta da wadanda suka taba mu'amala ba za su mantawa da shi ba.
Hadi Sirika na waɗannan bayanai ne a wajen addu'a cika kwanaki 3 da rasuwar tsohon shugaban na Najeriya, wanda ya rasu a birnin Landan bayan fama da rashin lafiya.
Sai a jiya Talata aka binne marigayin, bayan tsaikon tahowa da gawar daga Landan zuwa Najeriya da aka fuskanta.
Manyan ƴan siyasar kasar da 'yan kasuwa da al'umma daga sassa daban-daban na kasar sun halarci zaman addu'o'in da aka yi a yau Laraba a Daura.
Wasu manyan ƴan adawa a siyasar Najeriyar ma sun halarcin addu''ar da aka yi a garin Daura na jihar Katsina.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da hada-hadar hannayen jari a Najeriya SEC ta ce ta soma bincikar kamfanoni masu shirin damfarar mutane ta hanyar yi musu alkawarin nunka mu su jarin da suka zuba da ake kira ponzi schemes guda 79 da ke aiki a fadin Najeriya.
Hukumar ta kuma ce ta soma gudanar da gangamin wayar da kai a lunguna da sakon ƙasar domin kare dukiyar 'yan kasar.
Sai dai wasu masana a fannin tsaron naurar intanet na ganin akwai bukatar gwamnati ta nunka kokarin da takeyi domin har yanzu alumma na fadawa tarkon masu irin wadannan shirye shirye.
Hukumar ta ce cikin wadanda ake binciken har da wani kamfani mai suna FF Tiffany wanda hukumar ta ce ana zargin sa da zambatar masu zuba jari kuma ya yaudari dubban 'yan Najeriya, a cikin Najeriyar da kasashen waje.
Hukumar ta SEC ta kuma yi alkawarin bayyana sakamakon binciken ga jama’a.
Hakazalika ta kuma bayyana irin wadannan yaudara a matsayin barazana ga yadda da amincewar mutane a fannin hada-hadar kudi ta ƙasar wanda kuma zai rage kwarin-gwiwar masu zuba jari.
Dakta Nasir Baba Ahmed, masani a fannin tsaron naurar intanet a Najeriya da Turai, ya kuma ce akwai wasu alamomi da 'yan Najeriya za su iya la'akari da shi domin gane irin wadannan dandali na yaudarar mutane.
Hukumar ta kuma jaddada aniyarta na kawar da duk wani shirin yaudarar mutane da kwashe musu kuɗaɗensu a Najeriya.
Ta kuma ce 'yan Najeriya za su iya ziyartar shafinta na intanet domin tabbatar da sahihancin duk wani kamfanin zuba jari kafin su sanya kuɗadensu.
Sai dai baya ga haka kuma, hukumar ta ce ta soma shiga lungu da sako na ƙasar kamar manyan kasuwanni da wuraren ibada domin wayar da kan jama’a kan yadda za su kaucewa irin wadannan masu yaudarar.
Hukumar ta kuma ce a cikin shekarar nan shugaban Kasar Bola Tinubu ya sanya hannu kan wata doka wadda ta bayar da damar cin tarar duk wanda aka kama da hannu a irin waɗannan shiri, naira miliyan 20 ko kuma zaman gidan yari na shekara 10.
Dakta Nasir ya ce akwai bukatar aiwatar da wannan doka yadda ya kamata da kuma daukar wadansu matakan domin kawo karshen wannan dabi'a.
Ko a cikin watan Afrilun wannan shekara, 'Yan Najeriya sun tafka asarar kuɗi a wani tsarin zuba jari mai suna CryptoBank Exchange wanda aka fi sani da CBEX da ya kai aƙalla naira triliyan daya.
Duk da wasu hukumomin ƙasar sun ce suna binciken lamarin domin gano masu hannu a ciki, kuma zuwa yanzu sun gano wasu daga cikinsu, sun ce da wuya su iya dawowa kowa da kudinsa.
Kakakin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya shaida cewa daga yau mataimakin shugaban ƙasa, Kashin Shettima da ministoci 22 da ya ke jagonta za su kammala zaman Daura.
Ya ce za su koma Abuja, inda shugaban ƙasa da sauran manyan jami'an gwamnati za su gudanar da taron addu'a ga marigayin, sannan za su ci gaba da karban gaisuwa a birnin Tarayyar.
Sannan gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda zai ci gaba da karɓan gaisuwa a gidan gwamnati da ke birnin jihar.
Sannan uwargidan marigayin da yaranta za su koma Kaduna zuwa ranar Juma'a domin ci gaba da karɓan gaisuwan jama'a.

Asalin hoton, EPA
An miƙa wa jagoran adawa a Turkiyya Ekrem Imamoglu hukuncin zaman gidan yari na watanni 20 sakamakon aibata mai gabatar da ƙara.
Mista Imamoglu, wanda ke tsare bisa tuhumar cin hanci ya dage cewa duk zarge-zargen da ake masa ɓata suna ne kawai na siyasa.
An kama tsohon magajin garin a watan Maris, lamarin da ya haifar da zanga-zanga a faɗin Turkiyya.
Ya ɗaukaka ƙara game da cin zarafin jami'in hukumar zaɓe, laifin da zai iya hana shi tsayawa takara a nan gaba.

Asalin hoton, Presidency
Gwamnatin jihar Benue ta ce har yanzu mutum 107 da aka jikkata a hare-haren da aka kai garin Yelwata, na samun kulawa a asibitin koyarwa na jihar da ke Makurdi.
Babban sakataren ma'aikatar jin-ƙai da kare afkuwar bala'i, Mista James Iorpuu ne ya bayyana haka yayin tattaunawa da manema labarai a Makurdi, babban birnin jihar.
Wasu da ake zargin ƴanbindiga sun afka wa jihar ranar 13 ga watan Yuni, inda suka kashe mutum sama da 100 a garin Yelwata, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.
Iorpuu ya ce jihar ta fara fuskantar hare-hare daga ƴanbindiga tun 2011.
Ya yi fatan kada a sake samun irin abin da ya faru a Yelwata, wanda ya ce ba a taɓa ganin irinsa ba a duniya.
An ga hayaki na tashi daga tsakiyar birnin Damascus, babban birnin Siriya bayan harin da Isra'ila ta kai.
An kuma bayyana cewa harin ya shafi ginin ma'aikatar tsaron ƙasar da ke dandalin Umayyad.

Asalin hoton, Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya sanar da ficewa daga babbar jam'iyyar adawa ta PDP.
Wata sanarwa da Atiku ya fitar, ya ce ya fice daga PDP ne saboda jam'iyyar ta sauka daga turbar da aka kafata a kai wanda kuma ya sha bamban da manufofinsa.
"Zan yi amfani da wannan dama wajen gode wa PDP saboda irin damar da ta ba ni. Abin taƙaici ne a gare ni wajen ɗaukar wannan mataki," in ji Atiku.
Atiku dai shi ya yi wa jam'iyyar PDP takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, inda ya sha kaye a hannun shugaba Bola Tinubu.

Asalin hoton, Esref Musa /Anadolu via Getty Images
Isra'ila ta kai hare-hare ta sama a Damascus, babban birnin Syria da kuma sauran yankuna - yayin da take nuna goyon baya ga mabiya addinin Druze.
Firaiministan Isra'ila Benjamen Netanyahu ya ce sojoji na aiki don tseratar da mabiya addinin addinin Druze da kuma kawo karshen ƙungiyoyin da ke goyon bayan gwamnati waɗanda ke kai musu hari a arewa maso kudancin Siriya.
Ministan tsaron Isra'ila, Isreal Katz ya yaɗa wani bidiyo na yadda aka kai wa wani gini a Damascus hari, wanda ya yi kama da harabar ma'aikatar tsaro.
Rahotanni sun ce an jikkata mutum tara a harin zuwa yanzu.

Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta ce za ta fara gudanar da bincike kan yiwuwar rashin daidaito da ke samu a hada-hadar kasuwanci tsakaninta da Brazil.
Wakilin kasuwancin Amurka Jamieson Greer ya ce binciken zai mayar da hankali ne kan hare-haren da gwamnatin Brazil ke kai wa kan kamfanonin sada zumunta na Amurka da kuma matakan kariya da ke cutar da wasu kamfanoni na Amurka da ma'aikata da manoma da masu kirkire-kirkiren fasaha.
Dangantaka tsakanin Washington da gwamnatin Barazil ta yi tsami tun bayan hawan shugaba Trump.
A makon da ya gabata, Mista Trump ya sanar da cewa daga wata mai zuwa Amurka za ta sanya harajin kashi 50 cikin 100 kan dukkan kayayyakin da ake shigowa da su daga Brazil.
Wasu manyan ƴan adawa a siyasar Najeriya sun halarci taron addu'o'i na kwana uku na marigayi tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a garin Daura, da ke jihar Katsina.
Buhari ya rasu a ranar Lahadi 13 ga watan Yulin 2025 a wani asibiti da ke birnin Landan.





Asalin hoton, Reuters
Aƙalla mutum 20 ne suka mutu a wani turmutsitsi a wata cibiyar rabon agaji da ke kudancin Gaza, wadda Amurka da Isra'ila ke goyon baya, a cewar ƙungiyar ta agaji GHF da kuma wani asibiti.
GHF ta ce mutum 19 ne suka mutu a turmutsitsin yayin da aka ɗaba wa ɗaya wuƙa a daidai lokacin da aka "shiga ruɗani" a cibiyar hukumar a yankin Khan Younis.
Ta ƙara da cewa ta yi imani mayaƙan Hamas ne suka janyo ruɗani a wajen.
Sai dai ofishin yaɗa labarai a Gaza karkashin ikon Hamas ya musanta iƙirarin, inda ya zargi GHF da ƙoƙarin "ɓoye" laifin da suka aikata.
Asibitin Nasser da ke Khan Younis ya ce ya karɓi gawawwakin mutum 21 waɗanda suka mutu sakamakon shaƙar hayaki mai sa hawaye da kuma turmutsitsi a wajen rabon agajin.
Wannan ne karon farko da ƙungiyar agajin ta GHF ke tabbatar da mutuwa a ɗaya daga cibiyoyinta.

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni sun ce aƙalla mutum 27 ne ake zargin ƴanbindiga sun kashe a jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya.
An kuma jikkata wasu da dama.
Wannan hari na zuwa ne kimamin wata ɗaya da kai wani hari da ya hallaka kusan mutum 200 a wani ɓangare na jihar.
Mazauna jihar sun bayyana kaɗuwa da harin, wanda suka ce ƴanbindigar da suka kai shi sun je ne ɗauke da manyan bindigogi a safiyar Talata.
Maharan sun bi gida zuwa gida, inda suka yi ta hallaka mutane da kuma cinna wa gidajensu wuta.
Wani jami'i a jihar ya shaida wa BBC cewa an ƙona wata jaririya mai kimamin wata uku tare da iyayenta.
Shi ma wani shugaban matasa ya bayyana cewa yawanci waɗanda lamarin ya rutsa da su, sun ƙone har ta kai ba a iya gane su.
Sun yi zargin cewa sojoji da ke kusa da wajen da aka kai harin sun ƙasa kai musu ɗauki yayin harin.
Ana sa ran gwamnan jihar ta Filato zai kai ziyara zuwa waɗannan al'ummomi da harin ya shafa - mai nisan kilomita 50 da Jos, babban birnin jihar.

Ana ci gaba da zaman makoki da kuma addu'o'i, bayan binne tsohon shugabann Najeriya Muhammadu Buhari a garin mahaifarsa da ke Daura, a jihar Katsina.
Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa za a yi sadakar uku yau Laraba.
Tawagar gwamnatin tarayya da ta jihar Katsina suna kan hanyar shiga Daura, kuma da zarar sun isa ne za a san abubuwan da za a yi yau.
A gefe guda kuma masu gaisuwa da juyayi suna ci gaba da zuwa gidan marigayin.



